ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Laifi Tudu Ne, Lamarin Epstein Ya Tona Asirin Kasashen Yammaci Game Da Kare Hakkin Dan Adam

by Sulaiman and CGTN Hausa
7 months ago
epstein

Gawurtaccen mai lalata kananan ‘yan matan nan, Jeffrey Epstein da aka bayyana cewa ya kashe kansa lokacin da yake tsare a kurkuku, sunansa ya karade kafafen yada labaru na duniya, sabo da kaurin sunan da ya yi wajen aikata laifin safarar kananan ‘yan mata tare da rarraba su ga manyan mutane ana yi musu fyade. 

Mutuwar Jeffrey Epstein dai ta bar baya da kura, sabo da tonon sililin da ya bankado na abin kunya kan wasu fitattun mutane na duniya.

  • Ganduje Ya Musanta Zargin Nasir El-Rufai Kan Ɓacewar Dadiyata
  • Abin Da Ya Sa Manoman Rani Na Alkama Suka Samu Matsala A Kano

Asirin Epstein, ya fara tonuwa ne tun shekarar 2008, lokacin da wata kotu a birnin Florida na kasar Amurka ta samu Ba’Ameriken da laifin safarar ‘yan matan masu kananan shekaru tare da tursasa masu yin karuwanci, aka kuma yanke mashi hukuncin daurin watanni 18. Sai kuma a shekara ta 2019 gwamnati ta shigar da kararsa tare da tuhumarsa da laifin lalata da kananan ‘yan mata. To sai dai lokacin da yake tsare an wayi gari aka same shi ya kashe kansa.

ADVERTISEMENT

Mutuwar Jeffrey Epstein ta sanya allura ta tono garma sakamakon manyan mutanen da aka bankado suna da ma’amala ta kut da kut da Epstein a cikin wannan harka ta baɗala da kananan ‘yan mata. Irin wadannan mutane sun haɗa da jiga-jigan ‘yan siyasa da manyan attajirai da fitattun shugabanni na duniya.

Abin tashin hankalin a nan shi ne yadda kundin da aka fitar na baya bayan nan game da abin kunyar da aka fitar yake dauke da sunayen wasu fitattun mutane a fannin siyasa da harkar kudade daga Amerika da Turai. Irin wadannan mutane sun haɗa da shugabanni, ‘ya’yan gidan sarauta, jami’an diplomasiyya, ‘yan siyasa, masana, da masu kamfanonin jarida, an kuwa same su da alaka ta kut da kut da Mr. Epstein. Don haka yanzu kallo ya koma sama, shaho ya dauki giwa. Yanzu ba ma ta batun Epstein ake ba, yanzu hankali ya karkata kan irin wadannan manyan mutane, wadanda da bazarsu Epstein yake taka rawa.

LABARAI MASU NASABA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

Yanayin mutuwar Jeffrey Epstein dai ta sanya jama’a tababa kan hakikanin ikirarin cewa kashe kansa ya yi. Fallasa sunayen irin wadannan mutane dake da alaka da Epstein ya kara jefa shakku kan yanayin mutuwar Mr. Epstein da cewa akwai rufa rufa.

Abin da mummunan lamarin na Epstein ya fallasa bai tsaya ga abin kunya ba kadai, lamarin ya nuna irin yadda ake yi wa doka karan tsaye tare da wulakantar da mutuncin dan adam a Amerika da kasashen yammaci. Wannan ya nuna ikirarin cewa kowa daidai yake da kowa a gaban shari’a a matsayin almara. Akwai shafaffu da mai wadanda doka ba ta hawa kansu, wato za su karya doka su kwana lafiya. An wayi gari a yau irin tabargazar da ake tafkawa a gwamnatin Amerika da majalisar dokokin kasar ya zubar da mutunci da kimar gwamnati a idon ‘yan kasar, musamman kan irin yadda ‘yan siyasa suka gurbace.

Wannan abin kunya da lamarin Epstein ya fallasa ya sanya tilas kasashen yammaci sun sunkuyar da kansu cikin kunya, sabo da irin babatunsu kan batun kare hakkin dan adam. Tun da ga shi yanzu ta tabbata sun gaza ba da kariya ga mutuncin kananan ‘yan matan da ake ci ma zarafi. (Lawal Mamuda)

epstein
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
epstein
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

MASU ALAKA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta
Ra'ayi Riga

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

September 8, 2026
Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin
Ra'ayi Riga

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

September 4, 2026
Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa
Ra'ayi Riga

Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa

September 2, 2026
Next Post
Hakimin Da Aka Sace A Jihar Kogi Ya Shaki Iskar ‘Yanci

Kogi Ta Rufe Kasuwanni Da Filayen Motoci Don Fitar Da ‘Yan Ta’adda

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.