ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Abin Da Ya Sa Manoman Rani Na Alkama Suka Samu Matsala A Kano

by Abubakar Abba and Sulaiman
7 months ago
Alkama

Manoman rani na Alkama a Jihar Kano, na ci gaba da kokawa, kan gazawar gwamnatin tarayya, na cika alkawarinta na samar musu da dauki a karkashin shirinta na aikin noma na NAGS-AP.

A cewarsu, sun jira samun daukin daga wurin gwamnati, amma hakarsu ba ta cimma ruwa ba, duk da nanata alkawarin da gwamnatin ta yi.

  • Babu Hannun Ganduje A Sace Dadiyata – Shehu Sani
  • Gwamnatin Tarayya Ta Ankarar Da Masu Kiwon Kaji Kan Ɓullar Murar Tsintsaye

Har ila yau, sun koka da cewa; gwamnatin ta sha yi musu alkawarin samar musu dauki, musamman wajen samar musu da kayan aiki a cikin rahusa, amma har zuwa yanzu, ba su gani a kas ba.

ADVERTISEMENT

Daya daga cikinsu, Malam Habibu Garba da ke yin noma a Karamar Hukumar Garun Malam a jihar, ya sanar da cewa; jiran nasu ya ci gaba da kasancewa tamkar jiran gawon-shanu, na samu dauki daga wurin gwamnatin.

Gwamnatin, ta dai tsara shirin na NAGS-AP, da nufin kara bunkasa noman Alkama a cikin kasar, musamman domin a rage dogaro da shigo da ita daga ketare da kuma kara karfafa nomanta a fadin kasar baki-daya.

LABARAI MASU NASABA

Kha’amuna Khadi Ta Karɓi Jagorancin Gudanarwa Ta Bankin Noma

Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya

Sai dai, abin takaici, bayan shafe watanni manoman nata na jiran daukin, amma shiru kake ji, ganin cewa; ba su samu ba har aka fara gudanar da kakar noman rani na 2026.

Rahotannin sun bayyana cewa, daukin da aka tsara za a samarwa da manoman Alkamar, ya hada da rage musu farashin kayan nomanta da samar musu da ingantaccen takin zamani, da za a iya yin amfani da su, hekta guda 3,000 da aka kiyasata.

Kazalika, an tsara cewa; kowanne manominta daya zai samu buhu mai nauyin kilo 50, na ingantaccen irin noma da buhu uku na takin zamani, kan farashin gwamnati na kashi 50.

Sai dai, wani daga cikin manoman Alkamar a jihar, Shehu Bello Bahago ya ce; shigar da manoman suka yi a cikin shirin gwamnati wasu kakar noma na baya sun amfana.

Ya yi gargadin cewa, matukar gwamnatin ta gaza cika alkawarin, hakan zai iya janyo wa manoman jihar, su gaza ci gaba da nomanta.

“Manomanta da dama, sun zuba jarinsu a kakar nomanta ta bana, musamman ganin cewa; akasarinsu sun dogara ne da daukin da suka samu daga wurin gwamnati,“ in ji shi.

Kazalika, manoman sun kuma bayyana fargabarsu, kan rade-radin da ake yi na cewa; gwamnatin za ta shigo da Alkama daga ketare.

Shi kuwa, Shugaban Kungiyar Manoman Alkama na Kasa, reshen Jihar Kano (WFAN), Alhaji Musa Shehu, ya tabbatar da jiran da manaomanta na jihar ke ci gaba da yi na samun daukin gwamnatin.

Amma ya sanar da cewa, duk da wannan jinkirin na samun daukin na gwamnatin, hakan bai hana manoman yin amfani da ‘yan kudaden da suke da shi na yin noman ranin na bana ba.

Ya kara da cewa, abin takaici ne kan gazawar gwamnatin, na cika wannan alkawari nata da ta yi musu.

“A matakin kungiyar, mun yi kokarin tattaunawa da sauran ma’aikatun da ke kula da bangaren aikin noma, domin ganin an cimma nasarar wannan shiri, wanda kuma muna da yakinin cewa; za a wanzar da shi,” a cewarsa.

Sai ya ci gaba da cewa, abin takaici, babu daya daga cikin ‘ya’yan kungiyar da ya samu wani dauki daga wurin gwamnatin.

“Muna bukatar gwamnatin ta yi mana bayani, kan rashin cika wannan alkwari nata, domin kada manoman su kara yin wata asara a nan gaba,” in ji shugaban.

Kazalika, an ruwaito cewa; duk kokarin da aka yi, domin ji daga bangaren Ma’aikatar Aikin Gona da Samar da Wadataccen Abinci ta shiyyar Jihar Kano, kan wannan batu; hakan ya ci tura.

Alkama
Abubakar Abba
+ posts Bio
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Tun Ina Karama Marigayi Tumbuleke Ke Sa Ni Dariya —Hannatu Musawa
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Yadda Bikin Girke-girke Ya Karfafa Alaka Tsakanin Musulmai Da Kiristoci A Kaduna
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Nazari Kan Wasu Dalilan Da Ke Haddasa Sabanin Abotakar Jarumi Ko Jaruma A Kannywood
Alkama
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

Abin Da Ya Sa Gidauniyar NADF Da Bankin Manoma Suka Yi Haḍaka
Noma Da Kiwo

Kha’amuna Khadi Ta Karɓi Jagorancin Gudanarwa Ta Bankin Noma

August 1, 2026
Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya
Noma Da Kiwo

Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya

July 18, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Noma Da Kiwo

Sharhi A Kan Dabarun Zamani Na Yin Auren Ƴaƴan Itatuwa

July 11, 2026
Next Post
Laifi Tudu Ne, Lamarin Epstein Ya Tona Asirin Kasashen Yammaci Game Da Kare Hakkin Dan Adam

Laifi Tudu Ne, Lamarin Epstein Ya Tona Asirin Kasashen Yammaci Game Da Kare Hakkin Dan Adam

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.