ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Mace Ta Doke Namiji A Zaɓen Fidda Gwani Na Majalisar Tarayya A Katsina

by El-Zaharadeen Umar
4 months ago

Tsohuwar mai bai wa Gwamna Raɗɗa shawara kan ilimin ’ya’ya mata, Hajiya Jamila Abdu Mani, ta samu nasara kan abokin takararta Ahmad Saleh Junior da gagarumin rinjaye a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC mai mulki.

Da yake bayyana sakamakon zaɓen fidda gwanin da aka gudanar a mazaɓu 22 da ke ƙananan hukumomin Bindawa da Mani, shugaban kwamitin zaɓen, Hon. Shafi’u Abdu Duwan, ya ce Hajiya Jamila Abdu Mani ta samu ƙuri’u 2,498, yayin da Ahmad Saleh Junior ya samu ƙuri’u 1,256.

Tun farko dai an yi ta ce-ce-ku-ce bayan da aka bayyana cewa an gudanar da sasanci wanda ya bai wa Jamila Abdu Mani nasara, amma abokin takararta ya ƙi amincewa da hakan, lamarin da ya kai ga gudanar da zaɓen fidda gwani.

ADVERTISEMENT

Yanzu haka, Hajiya Jamila Abdu Mani ce mace kaɗai da ta samu tikitin takarar kujerar majalisar tarayya daga jihar Katsina a ƙarƙashin jam’iyyar APC domin wakiltar ƙananan hukumomin Bindawa da Mani a zaɓen 2027.

Haka kuma, idan za a iya tunawa, ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Bindawa da Mani a yanzu, Hon. Ahmad Yusuf Ibrahim na jam’iyyar APC, bai shiga wannan takara ba saboda shi ma daga ƙaramar hukumar Bindawa ya fito.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Batun tsayawarta takara ya kasance ɗaya daga cikin abubuwan da suka jawo muhawara a siyasar Jihar Katsina, musamman tsakanin malamai da masu sharhi kan al’amuran yau da kullum.

Yanzu dai abin jira a gani shi ne yadda za ta tunkari babban zaɓen, la’akari da irin ƙalubalen da ta ke fuskanta a matsayinta na mace ’yar takara daga jihar.

El-Zaharadeen Umar
+ postsBio
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Cutar Mashako:Yadda Yara Ke Mutuwar Bazata A Jihohin Katsina Da Kano
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Mauludin Annabi (SAW): Shugaba Tinubu Ya Nemi A Yi Addu’o’in Nasara Kan Matsalar Tsaro
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Shekaru 8 Cikin Raɗaɗi: Wani Bawan Allah Ya Samu Tiyata Kyauta Daga Gidauniyar Mangal
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Tinubu Ya Nemi Malamai Su Taimaka Wajen Yaƙi Da Ƴan Ta’adda

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
Next Post

An Tsaurara Matakan Tsaro Yayin Da APC Ta Fara Zaɓen Fidda Gwani A Kaduna

LABARAI MASU NASABA

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.