ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Manyan Haduran Jirgin Sama A Nijeriya (2)

Ci Gaba Daga Makon Daya Gabata

by Idris Aliyu Daudawa
3 years ago
Sama

LABARAI MASU NASABA

Tarihin Shugaban Makaranta Na Farko A Arewa Hedimasta (2)

Cin Amana Uku Da Suka Sauya Tarihi A Duniya

6. Ranar 4 watan Mayu 2002 mutane 72 sun mutum bayan da jirgin saman BAC One-Eleben wanda ya tashim Kano ya yada zango Jos ya sauka Legas ya fadi jim kadan bayan tashi daga tashar jirgin sama ta Kano.

Sashen kula da lafiyar yanayin da tashar jirgi take ya bayyana cewa: “Jim kadan bayan tashin jirgin saman daga Kano sai aka ga ya daina tafiya ya fadi a wurin da yake da dandazon mutane wato Gwammaja wanda kilomita daya ne daga tashar jirgin sama ta Kano.

Ya fadi akan gida mai hawa biyu ya kuma raba Masallaci biyu bayan ya rarrabu yak ama da wuta,ya lalata gidaje 23 a Gwammaja tare da makaranta da Masallaci.”

Bayan da jirgin ya fadi an bar jirgin har kwana 52 saboda rashin ingancin injin shi.Ya fadi bayan an yi awa goma aka sa ma shi wani injin jirgin da ba a aiki da shi.

Bayan da faduwar jirgin saman sa ma’aikatar harkokiin jirgin sama ta ta hana yin amfani da jirgin da yayi shekaru fiye da 22.

  1. Ranar 22 ga watan Oktoba 2005, mutane 117 sun mutum bayan da jirgin sama kirar 737 mallakar kamfanin jirgin sama na Bellbiew ya fadi kusa da Legas.

Jirgin na Bellbiew 210 mai zurga- zurgar cikin gida ya tashi ne daga Legas da karfe 8 da minti 35 na dare zuwa Abuja.

Masu lura yanayin da jirgin saman yake sun rasa tuntubar juna ne bayan minti uku da tash da safe sai aka samu baraguzan jirgin kilomita 30 Arewacin Legas rashin yanayi mai kyau ne ya kawo fadin jirgin saman.

  1. Ranar 10 ga Disamba 2005, mutane 108 sun mutu yawancinsu ‘yan makaranta ne na kwalejin Loyola Jesuit da ke Abuja,bayan da jirgin McDonnell-Douglas mallakar kamfanin jirgi na Sossoliso ya fadi lokacin da yake kokarin sauka a tashar jiragen sama ta Fatakwal. An ceto mutane biyu da ransu.

Babbar matsalar da tayi sanadiyar faduwar jirgin ita ce rashi yanayi mai kyau.Binciken da ak yi ya nuna cewar “matakin da ma’aikatan suka dauka na ci gaba da kusantar sauka ba tare da sanin halin da nisanda jirgin yake daga sama ba tare da sanin yanayin titin da jirgi zai hau lokacin sauka shine musabbin da yasa aka yi hadarin jirgin”.

Sauran dalilan sun hada da rashin aiki sosai na fitilun hanyar da jirgin zai hau zuwa inda zai tsaya ga kuma rashin inganci na yadda filin jirgin saman yake.

  1. Ranar 29 ga Oktoba 2006 mutane 97 sun mutu bayan da jirgin sama kirar Boeing 737 mallakar kamfanin ADC ya fadi kusa da Abuja ‘yan mintoci kadan bayan ya tashi daga filin jirgin sama na Abuja.

Jirgin na kamfanin ADC ya taso daga Legas ne kan hanyarsa ta zuwa Sakkwato amma sai ya  tsaya a Abuja.

Bai dade da tashi ba daga filin jirgin saman a Abuja sai jirgin saman Boeing 737 ya bugi kasa ya rabu daganan ya kama wuta a gona,matar da take aiki ta mutu sanadiyar bayan da baraguzan jirgin sun fado mata.Babban dalilin aukuwar hadarin shine matukin yaki daukar rashin yanayi mai kyau da muhimmanci.

  1. Ranar 3 ga Yuni 2012 jirgin saman kamfanin Dana ya fadi inda mutane 153 da ya dauko suka mutu.

Jirgin saman fasinja na McDonnell Douglas MD-83, 5N-RAM, na kamafanin Dana ya lalace ne lokacin da ya fadi a wurin da mutane ke zama a Legas.

Dukkan fasinjoji 146 da ma’aikata 7 sun mutu yayin da aka gano mutum 7 a gidajen wadanda jirgin ya shafe su lokacin da ya fadi.

Sama
Idris Aliyu Daudawa
+ postsBio
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Tarihin Rayuwar Galadiman Kano Alhaji Tijjani Hashim (2)
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Kyamar Baƙi: An Sake Kwaso Ƴan Nijeriya 83 Daga Afirka Ta Kudu
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Kamfanin Simintin Dangote Ya Tallafa Wa Manoma 60 Da Kayan Aiki A Edo
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Tsohon Shugaban Ƙasa Jonathan Ya Ƙaddamar Da Ayyukan Raya Ƙasa 18 A Jihar Bauchi
ADVERTISEMENT

MASU ALAKA

Laifukan Intanet: Kotun Abuja Ta Karɓi Rahoton DSS, Ta Ba Da Belin Wani Ɗan Gwagwarmaya
Tarihi

Tarihin Shugaban Makaranta Na Farko A Arewa Hedimasta (2)

May 30, 2026
Cin Amana Uku Da Suka Sauya Tarihi A Duniya
Tarihi

Cin Amana Uku Da Suka Sauya Tarihi A Duniya

February 22, 2026
Tarihin Sarkin Zazzau Ja’afaru Dan Isiyaku 1936-1959
Tarihi

Tarihin Sarkin Zazzau Ja’afaru Dan Isiyaku 1936-1959. (2)

January 11, 2026
Next Post
Sin Ta Shafe Shekaru 60 Tana Aikewa Da Ma’aikatan Agajin Jinya Zuwa Kasashen Waje

Sin Ta Shafe Shekaru 60 Tana Aikewa Da Ma’aikatan Agajin Jinya Zuwa Kasashen Waje

LABARAI MASU NASABA

Rashin Mulki Ke Firgita Atiku – Kakakin APC Na Kaduna

Rashin Mulki Ke Firgita Atiku – Kakakin APC Na Kaduna

September 9, 2026
Yaya Toure Na Dab Da Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai

Yaya Toure Na Dab Da Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai

September 9, 2026
Xi Jinping Ya Taya Kim Jong-Un Murnar Cika Shekaru 78 Da Kafuwar Koriya Ta Arewa

Xi Jinping Ya Taya Kim Jong-Un Murnar Cika Shekaru 78 Da Kafuwar Koriya Ta Arewa

September 9, 2026
’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

September 9, 2026
Yadda Jami’an ‘Yansanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa

Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara

September 9, 2026
Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.