ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, June 5, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Masana Sun Gano Dalilan Da Ke Sa Mata Da Jarirai Mutuwa Yayin Haihuwa

Kididdiga

by Rabi'u Ali Indabawa
11 months ago
Haihuwa

A cewar Majalisar Dinkin Duniya, Nijeriya na da yawan mace-macen mata masu juna biyu, inda ta zo a matsayi ta daya a duniya. Adadin mace-macen mata masu juna biyu an kiyasta kusan mutuwar 1,047 a cikin 100,000 masu rai. Wannan yana nufin cewa mace daya c eke rayuwa a cikin mata 19 a Nijeriya sakamakon ciki ko haihuwa, idan aka kwatanta da mace daya c eke mutuwa a daga cikin mata 4,900 na kasashen da suka ci gaba.

Nijeriya na bayar da gudunmowa ga wani kaso mai tsoka na mace-macen mata masu juna biyu a duniya, inda kusan kashi 28.5 cikin 100 na adadin mace-macen mata a duniya ke faruwa a can. Ciwon zub da jini a cikin mahaifa, da ciwon ciki, sepsis, toshewar nakuda da matsalolin zubar da ciki na cikin abubuwan da ke haifar da mutuwar mata masu juna biyu a Nijeriya.

  • Sin Ta Bai Wa Habasha Kayayyakin Tallafin Jinya
  • Gwamnatin Yobe Ta Rufe Kasuwanni Uku Saboda Fargabar Hare-haren Boko Haram

Majalisar Dinkin Duniya, ta yi nuni da cewa, yayin da aka samu wasu sauye-sauye, yawan mace-macen mata masu juna biyu a Nijeriya ya ragu matuka, kuma har yanzu ba a kai ga cimma burin ci gaba mai dorewa na kasa da 70 a cikin yara 100,000 da za su haihu nan da shekarar 2030. Yawan mace-macen jarirai shi ma abin damuwa ne, inda kashi 69 cikin 1,000 ke mutuwa a kowace haihuwa 1,000 mai rai ga yara ‘yan kasa da shekaru biyar.

ADVERTISEMENT

Munanan Abubuwa

LABARAI MASU NASABA

Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Yi Sanadin Mutuwar Mutane 7 A Bauchi

Arsenal Na Dab Da Ɗaukar Jeremy Monga Daga Leicester City

Da take magana kan abin da ya faru, wata ‘yar kasuwa a Abuja, Cynthia George, ta ce ta kusa zama daga cikin matan da suka mutu mata masu juna biyu da jarirai ba don gaggawar mijinta ba. Ta shawarci maza da su tashi tsaye wajen ceto matansu masu juna biyu da ‘ya’yansu.

Ta ce, “Na tuna cewa an yi mini rajista don haihuwa a wani asibiti kuma na sami kulawar haihuwa a can, na fuskanci fashewar membrane a gida, don haka muka garzaya zuwa asibiti, amma ba mu samu wani likitan karbar haihuwa ba, mutanen da ke wurin kawai ma’aikatan jinya ne da likitoci.

“Na kasance mai rauni kuma na kasa magana, amma mijina yana tsaye, ya kira wani likitan a dangi daga Burtaniya ya bayyana masa halin da ake ciki, daga baya, ya kai ni wani asibiti daban inda na haihu. Irin wadannan abubuwa ne da ake tsammanin duk wanda ya bi mai ciki ko mara lafiya zuwa asibiti. Wannan ya nuna ba kawai ku jira likitoci ko ma’aikatan jinya su shigar da matar ku ba ne kadai, sai kun yi da gaske.

“Yawancin mace-macen mata masu juna biyu a Nijeriya yana da yawa kuma yawanci ya kan faru ne sakamakon rashin iya aiki da sakaci na ma’aikatan asibiti. Akwai abubuwa da yawa da za a iya gujewa; za mu iya yin abubuwa masu kyau. Kai ne rayuwar matarka yayin da take dakin haihuwa a lokacin CS. Kai ne idanun matarka yayin da take cikin dakin aiki. Muna bukatar bin diddigi

Har ila yau, da take magana da wannan dan jarida, wata ma’aikaciyar jinya, Florence Alu, ta ce haihuwa na kara zama kasada yayin da mata ke kara girma, tana mai cewa mace-macen mata masu juna biyu da jarirai na ci gaba da karuwa saboda yawancin mata masu juna biyu suna gudu zuwa gidajen addu’o’i domin haihuwa, maimakon asibitoci masu inganci.

Ta ce, “Na haifi ‘ya’yana biyu na farko a cikin shekaruna 20, sannan na karshe bayan dogon hutu na shekara 32. Na sha bakar wahala sanda na dawo haihuwa, hakika na zubar jini bayan kwana takwas na haihuwa. Saboda yawan ziyartar asibiti na gaggawa, na yanke shawarar ba zan sami karin yara ba.

“Haihuwar jariri na zama mafi hadari yayin da mutum ya girma. A lokacin haihuwa, ana rarraba mata masu juna biyu zuwa nau’i daban-daban ta amfani da shekarun mutum, yawan yara, yanayin haihuwa a baya (idan akwai), tarihin likita, da kuma tarihin iyali.

Wannan zai fayyace idan za su yi wa ciki alama mai hadari ne ko a’a. Yawancin mutanen da ke da yara ba tare da aure ba suna kanana sosai, tsakanin shekaru 18-25. A wannan shekarun, ciki da haihuwa ba su da hadari. Za su gaya maka a asibiti cewa hadarin yana farawa daga shekaru 35 zuwa sama.”

Sakacin ma’aikatan asibti

A nata bangaren, wata mai sana’ar dinki a Abuja, Ruth Emenyi, ta ce ta kusa rasa ranta da jaririnta sakamakon abin da wasu kwararrun ma’aikatan jinya suka yi a asibitin da ta je domin haihuwa.

“A ranar Talata, makon da ya gabata, ina cikin nakuda, don haka na garzaya zuwa asibiti, a kan hanyar ne ruwa ya fashe, na ji kan jaririna ya fito, sai na yi amfani da hannuna don tallafa wa kan jaririna daga kada ya fita.

Kun san cewa ko da wani ya ruga ya kira ma’aikatan jinya, sai suka nuna ba su damu ba? Da hakan na kutsa kaina da dan karfin da nake da shi na shiga dakin aiki.

“Ina ta kururuwa, ina gaya musu cewa kan jaririn ya fito, amma ma’aikatan jinya nan suka yi watsi da ni, wani ma yana yi mini dariya, lokacin da na kasa komai, sai kawai na zauna a kasa domin fama da ciwon, sai jaririn ya fito, a lokacin ne suka gane cewa da gaske nake.

Sai da daya daga cikin ma’aikatan jinya da ke dakin haihuwa ta fito ta ga jaririna a kasa, sai ta daka musu tsawa tana tambayarsu me ye a matsayinsu na ma’aikatan jinya. Ko da suka ga jaririna a kasa, ba su iya taimakawa ba. Ta bani hakuri ta dauki jaririyar tawa ta yi saurin goge ta. Sai ta kai ni dakin haihuwa ta taimaka wajen fitar da mahaifa sannan ta gyara ni.

“Yawancin wadannan mutanen ba su san aikinsu ba, idan ka lura cewa ba sa yin abin da ake son yi, don Allah a gaggauta komawa wani asibiti domin wannan rayuwa daya ce kawai. Na yi farin ciki da cewa babu abin da ya faru da ni da jaririna a ranar Talata. Zuwa asibiti ni kadai ko tare da wanda ba zai iya jure wulakancin ma’aikatan kiwon lafiya ba yana da matukar hadari. Ma’aikatan lafiyarmu dole ne su dauki aikinsu da muhimmanci, “in ji ta.

Hakazalika, wata ma’aikaciyar gwamnati mai suna Ijeoma Ethel, ta ce ta rasa danta ne sakamakon rashin kula da lafiyarta.

“Shekaru uku ke nan da rasa dana na biyu saboda sakaci da kwararrun likitocin asibitin suka yi, Likitan ya zargi ma’aikatan jinya da ke bakin aiki, yayin da ma’aikatan jinya suka dage cewa sun yi abin da likitan ya ce, a ranar za a yi wa jaririna tiyata a ranar, Likitan ya ce wa ma’aikaciyar jinya ta ba shi maganin sa barci domin ya shirya aikin tiyatar.

“Bayan ‘yan mintoci kadan, karamin dana ya mutu a cikin dakin tiyata, abin da radadi. Wasu asibitoci a Nijeriya tarko ne na mutuwa, likitoci da ma’aikatan jinya ba su da tausayi. Ba za a iya kwatanta tashin hankali da rashin kunya ba. Ma’aikatan jinya sun zama marasa imani. Hatta yadda suke tafiya a hankali abin yana da ban tsoro,” in ji ta.

A nata bangaren, wata malama mai suna Rita Ezra, ta ce tsoma bakin maigidanta ne ya ceci rayuwarta da jaririn nasu, yayin da ta kusa zubar jini a lokacin da take haihuwa.

“Lokacin da aka zo haihuwa za ka ga babu wani mai mutunci! Lokacin da nake cikin dakin aiki, ma’aikatan jinya duk suna ta kururuwa don in haihu da kaina kuma a lokacin na yi rauni sosai, kusan a lokacin da na rasa rayuwata, mijina ya yi musu tsawa kan su yi amfani da wata hanya ta gaggawa wato CS!

“Likitoci da ma’aikatan jinya na Nijeriya ba su da wani amfani ga rayuwar dan’Adam, na gode wa Allah da mijina ya kasance tare da ni a lokacin haihuwa. Dole ce ta sa ya ja likitan ya zo ya kula da ni yayin da nake tsananin zubar da jini. Kada ku yi wasa da mutum a cikin al’amarin rayuwa ko mutuwa. Ya kamata mace mai ciki ta yi rajista da akalla asibitoci biyu.

Nasihar masanakulawar da ta dace don magance matsalolin.

Ya ce, “A matsayina na mai bincike mai cikakken ilimi da gogewa a cikin kula da yara, haihuwa, kafin haihuwa da kulawa, na sami gogewa da batutuwan da ya sa iyaye mata masu ciki suke kin zuwa asibiti kafin haihuwa da bayan haihuwa da kuma kasancewar haihuwa, ya faru ne a kan tushen addini, akida al’adu, jahilci, talauci, ra’ayi na al’umma da kuma rashin tausayi.

“Mace-macen mata da jarirai na da nasaba da yanayi daban-daban, a yankunan karkarar Nijeriya, suna da dabi’un al’adu da imani cewa matan da suka haihu ta hanyar gargajiya su ne mata na gaske kuma ana yin biki, yayin da wadanda suka haihu ta hanyar CS ake nuna musu wariya.

A yunkurin gano wannan kiyayya da imani na al’umma, mata da yawa suna mutuwa saboda kin yin tiyatar CS. Wasu kuma sun ki zuwa asibiti ne; har sai da suka makara kuma a karya suka rasa rayukansu da na jarirainsu.

“Saboda haka, a yankunan karkara, sun fi kusanci da jahilci, imani na al’adu da dabi’un da aka yada wanda hakan ya haifar da kashi mafi girma na yawan mace-macen mata da jarirai. Har ila yau, a cikin birane da yankunan karkara, sakaci, lokutan aiki, damuwa, rashin kulawa da karuwar fahimtar addini, musamman a tsakanin Kirista da Musulmai, wadanda suke so su tabbatar da wani batu na haihuwa kamar matan Ibraniyawa, suna da manyan dalilai na haihuwa.

“Sakamakon sakaci, rashin kulawa a tsakanin likitoci, ungozoma da masu kula da haihuwa a asibitoci suma suna tasiri da yawa kamar yadda ba’a kula da lafiyar kwakwalwa..”

Ya ci gaba da cewa, “Saboda haka, al’amura da dama na iya haifar da mace-macen mata masu juna biyu da jarirai, ya kamata a yi la’akari da CS tare da kula da lafiya da kuma yanayin da ya dace domin mahaifar mace na iya samun rauni a kan lokaci.

“Ya kamata a inganta ilimin da ya dace ga iyaye mata saboda ba a ba da fifiko ga amfanin kula da mata masu juna biyu da kuma wayar da kan mazauna karkara ba, ya kamata a yi la’akari da tsarin iyali don taimakawa iyalai da mata su rayu yadda ya kamata, matan da ke dabi’ar zubar da jini bayan haihuwa ya kamata su yi la’akari da shawarwarin likita da kuma kulawa da kyau don rage yawan mace-mace.”

A nasa ra’ayin, wani likita kuma shugaban kungiyar masu ba da shawara ga jihohi da ci gaban kasa (STAND) Dr. Otubo Bictor O., ya shawarci mata masu juna biyu da su je inda ya dace da za a basu kulawa (asibiti), yana mai cewa asibitoci na ba da fifiko wajen ceton rayuka.

Ya ce lafiyar mai juna biyu uwa uba wani bangare ne na muradin ci gaba mai dorewa (SDG3), kuma gwamnatin tarayya na yin kokari sosai don tabbatar da daukar ciki lafiyayye da tallafi ga mata da iyalansu, ya kara da cewa kula da masu haihuwa da haihuwa a zahiri suna da araha a asibitocin gwamnati.

“Na sha ganin al’amuran da dama na mata masu juna biyu da ke guje wa ziyartar asibiti domin kula da masu juna biyu har sai lokacin ya kure, a gaskiya na sadaukar da wani babi gaba daya a cikin littafina mai suna “My Family Companion” kan batutuwan da suka shafi kula da mata masu juna biyu, daya daga cikin labaran da na bayar a cikin littafin akwai wata mara lafiya da aka kai sashenmu na gaggawa tare da korafin ciwon ciki mai tsanani da suma.”

“Ya kamata a inganta ilimin da ya dace ga iyaye mata saboda ba a ba da fifiko ga amfanin kula da mata masu juna biyu da kuma wayar da kan mazauna karkara ba, ya kamata a yi la’akari da tsarin iyali don taimakawa iyalai da mata su rayu yadda ya kamata, matan da ke da dabi’ar zubar da jini bayan haihuwa ya kamata su yi la’akari da shawarwarin likita.

“Wani al’amari ya faru ne a cikin bututun mahaifar wata mata na hagu, kuma lamarin ya yi tsanani sosai har sai da muka cire dukkan bututun, abin da ya fi tayar da hankali shi ne, yayin da muke yi mata tiyata, mun gano cewa an cire mata bututun fallopian na dama shekaru da suka wuce saboda fashewar da ta yi a baya. Wannan fashewar ta farko ta faru ne tun tana ‘yar shekara 17. An yi mata fyade, amma saboda tsoron wulakanci da tsoro da iyayenta suka ji suka yi shiru, “in ji ta.

Ya kara da cewa, “Ba ta ma san tana dauke da juna biyu ba, sai da ta fadi, aka garzaya da ita asibiti, tun da farko iyayenta sun dauka ciwon ciki ne, amma bayan da aka yi mata gwaje-gwaje da gaggawa, likitoci sun tabbatar da cewa ta samu ciki ne, kuma sai da aka yi tiyata, bayan shekaru da yawa, ta yi aure ta sake samun juna biyu, amma abin takaici, ta ki ba wa haihuwar kulawa da wuri.

“Babban abin da ke haddasa mace-macen mata masu juna biyu da jarirai a Nijeriya shi ne rashin zuwa duba lafiya, Wannan ya kan haifar da yanayin da mutane ke neman taimakon likita a mawuyacin hali bayan lokaci ya kure.

“Abubuwa da yawa na iya haifar da mace-macen mata masu juna biyu kuma yawan haihuwa a kansa ba dalili ba ne, na farko, dabi’a tana sarrafa cewa mace ba za ta iya haihuwa ba har abada ba, mun san game da bacewar al’ada, abin da ke damun yawan masu haihuwa, ko kuma abin da muke kira daidaito, shi ne tazara.

Matsakaicin lokacin ciki shi ne tsakanin watanni 18 zuwa 24. Yin ciki da sauri bayan haihuwar da ta gabata na iya sanya damuwa mai yawa a jikin mace, yana kara hadarin rikitarwa har ma da mutuwar uwa.

A wata hira da Blueprint Weekend, wani mai ba da shawara kan harkokin ilimi da kudi na Burtaniya, Anthony Oko, ya ce hadewar addini, akida al’adu, jahilci, talauci, son zuciya da kuma tasirin abokan gaba na iya haifar da mace-macen mata da jarirai, yana mai ba da shawarar cewa Sashen Caesarean (CS) ya kamata a yi la’akari kulawar da ta dace don magance matsalolin.

Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    NSCDC Ta Cafke Mutum 10 Da Ake Zargi Da Satar Kayan Gwamnati Da Kuma Fashi A Kano
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƴansanda Su Ƙi Karɓar Cin Hancin Naira Miliyan 500 Daga Hannun Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙasashen DR Congo Uganda Da Sudan Sun Haɗa Kai Domin Yaƙar Ibola
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Zafin Rana Ya Yi Ajalin Mutum 16 A Indiya

MASU ALAKA

Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Yi Sanadin Mutuwar Mutane 7 A Bauchi
Manyan Labarai

Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Yi Sanadin Mutuwar Mutane 7 A Bauchi

June 4, 2026
Arsenal Na Dab Da Ɗaukar Jeremy Monga Daga Leicester City
Wasanni

Arsenal Na Dab Da Ɗaukar Jeremy Monga Daga Leicester City

June 4, 2026
Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili
Manyan Labarai

Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili

June 4, 2026
Next Post
Ayyukan ‘Yan Ta’adda Na Barazana Ga Shirin Gwamnati Na Wadata Kasa Da Abinci

Ayyukan 'Yan Ta'adda Na Barazana Ga Shirin Gwamnati Na Wadata Kasa Da Abinci

LABARAI MASU NASABA

Matatar Dangote Ta Ƙara Yawan Man Da Take Tacewa Zuwa Ganga 700,000

Matatar Dangote Ta Ƙara Yawan Man Da Take Tacewa Zuwa Ganga 700,000

June 4, 2026
Ƴansanda Sun Daƙile Harin Ƴan Bindiga, Sun Kwato Shanu 25 A Sakkwato

Ƴansanda Sun Daƙile Harin Ƴan Bindiga, Sun Kwato Shanu 25 A Sakkwato

June 4, 2026
Takunkumin Amurka Ya Haifar Da Mummunan Tasiri Ga Tsarin Samar Da Kayan Latironi Na Duniya

Takunkumin Amurka Ya Haifar Da Mummunan Tasiri Ga Tsarin Samar Da Kayan Latironi Na Duniya

June 4, 2026
Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Kashe Mutane 7, Ya Jikkata 6 A Bauchi

Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Kashe Mutane 7, Ya Jikkata 6 A Bauchi

June 4, 2026
Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Yi Sanadin Mutuwar Mutane 7 A Bauchi

Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Yi Sanadin Mutuwar Mutane 7 A Bauchi

June 4, 2026
Mun Kaɗu Matuƙa Kan Labarin Mutuwar ‘Yan Mauludi A Hanyar Saminaka – Gwamnan Kaduna

Gwamna Sani Ya Kashe Sama Da Naira Biliyan Ɗaya Kan Tallafin Ɗalibai A Kaduna – Kwamishina

June 4, 2026
Sin Ta Ware Kudi Har Yuan Biliyan 99.9 Domin Tallafawa Kula Da Lafiyar Yara A 2026

Sin Ta Ware Kudi Har Yuan Biliyan 99.9 Domin Tallafawa Kula Da Lafiyar Yara A 2026

June 4, 2026
Tasirin Nasarar Da Kasar Sin Ta Cimma A Fannin Kakkabe Matsanancin Talauci

Tasirin Nasarar Da Kasar Sin Ta Cimma A Fannin Kakkabe Matsanancin Talauci

June 4, 2026
Sabbin Ra’ayoyin Ci Gaba: Manufofin Zamani Na Zamanantarwa

Sabbin Ra’ayoyin Ci Gaba: Manufofin Zamani Na Zamanantarwa

June 4, 2026
Fargabar Satar Mutane Ya Sa An Rufe Makarantu A Abuja Da Mararaba

Fargabar Satar Mutane Ya Sa An Rufe Makarantu A Abuja Da Mararaba

June 4, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.