ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Matasa 1,200 Sun Amfana Da Horon Sana’o’i Ƙarƙashin Shirin ‘Renewed Hope’ A Kaduna

by Sulaiman and Shehu Yahaya
3 months ago
Matasa

Matasa maza da Mata 1,200 ne suka amfana da horon sana’o’i da tallafin jari a ƙaramar hukumar Igabi ta Jihar Kaduna karkashin shirin “Renewed Hope Empowerment Initiative” Na Shugaba Bola Tinubu da Gwamna Uba Sani.

Shirin, wanda aka gudanar domin inganta tattalin arzikin al’umma da samar da hanyoyin dogaro da kai, ya zo ne a daidai lokacin da gwamnatin tarayya ke aiwatar da manyan ayyukan raya ƙasa a Jihar Kaduna, ciki har da aikin gyaran hanyar Abuja–Kaduna–Zaria–Kano, hanyar Mando–Kaduna–Birnin Gwari, aikin bututun iskar gas na Kano zuwa Kaduna, da kuma ayyukan jirgin ƙasa da layin dogo na zamani.

Masu ruwa da tsaki da waɗanda suka ci gajiyar shirin sun yaba wa Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, bisa ayyukan raya ƙasa da suke aiwatarwa, inda suka bayyana cewa wadannan ayyuka za su taimaka wajen bunkasa tattalin arziki, samar da ayyukan yi da inganta rayuwar al’umma.

ADVERTISEMENT

Da yake jawabi a wajen bikin yaye wadanda suka kammala horon da aka gudanar a makarantar Firamare da ke Rigachikun, jagoran Shirin Abdulmuminu Aminu Zaria, ya ce shirin wata alama ce ta jajircewar gwamnatin tarayya da ta jihar wajen samar wa jama’a damar dogaro da kai ta hanyar horar da su sana’o’i.

Ya bayyana cewa an horas da mahalarta shirin a fannoni daban-daban guda takwas tare da ba su tallafin kuɗi domin su fara ko kuma su faɗaɗa sana’o’insu.“Mun horas da su sana’o’i daban-daban tare da ba su tallafin kuɗi domin su zama masu dogaro da kansu kuma masu amfani ga al’umma,” in ji shi.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

A nasa jawabin, Mai Kula da Shirin Renewed Hope Agenda a Jihar Kaduna, Abubakar Mohammed Mamadi, ya ce an kirkiri shirin ne domin bai wa mata da matasa ƙwarewa da kayan aikin da za su taimaka musu wajen samun ‘yancin tattalin arziki da kuma bayar da gudunmawa ga ci gaban al’umma.

Mamadi, wanda kuma shi ne mai ba Gwamnan Jihar Kaduna Shawara Kan Harkokin Siyasa, ya ce shirin ya yi daidai da manufofin “Renewed Hope Agenda” na Shugaba Tinubu da kuma hangen nesan gwamnatin Sanata Uba Sani na inganta rayuwar al’umma ta hanyar samar da ayyukan yi da shirye-shiryen tallafawa jama’a.

Ya buƙaci wadanda suka amfana da shirin da su yi amfani da damar da aka ba su yadda ya kamata, tare da ƙoƙarin zama masu ɗaukar ma’aikata maimakon jiran tallafin gwamnati kaɗai.

Ya yaba wa Gwamna Uba Sani bisa ayyukan ci gaba da yake gudanarwa a jihar, tare da gode wa dukkan mutanen da ƙungiyoyin da suka ba da gudunmawa wajen nasarar shirin.

Matasa
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
Matasa
Shehu Yahaya
+ posts Bio
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Gwamna Uba Sani Ya Yi Jimamin Rasuwar Dan Jarida Jafaru Yakubu Maitama
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Gwamnatin Kaduna Ta Fara Rabon Takin Zamani Kyauta Ga Manoma 150,000
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Zaka Iya Sayar da Takin Gwamnati Ka Sayawa Iyalinka Kaji — Imam Nuradden
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Rashin Tsaro: ACI Zata Kira Taron Gaggawa Na Masu Ruwa Da Tsaki A Kaduna

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
Next Post
Ɗan Majalisar Dokokin Bauchi, Hon. Wanzam, Ya Rasu

Ɗan Majalisar Dokokin Bauchi, Hon. Wanzam, Ya Rasu

LABARAI MASU NASABA

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.