ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, July 15, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Mazauna Bauchi Na Kokawa Kan Tsadar Farashin Acaba Duk Da Raguwar Farashin Mai

by Khalid Idris Doya
6 months ago
bauchi

Mazauna birnin Bauchi su na ci gaba da kokawa kan tsadar farashin kuɗin sufuri na Achaba da na Keke Napep, duk da raguwar farashin kuɗin man fetur da aka samu kwanan nan.

Da dama daga cikin fasinjoji sun ce tsadar kuɗin sufuri da ke ci gaba da yin tsada ya ƙara tsananta wahalar rayuwa, musamman ga masu ƙaramin ƙarfi da ke dogaro da Achava da Keke Napep wajen zirga-zirgar yau da kullum a cikin birnin.

  • Ƴansanda Sun Cafke Wani Mahaifi Bisa Zargin Yi Wa Ƴarsa Mai Shekara 8 Fyaɗe A Bauchi
  • Yadda Ɗalibai Ke Ɗaukar Darasi A Ƙasa, Cikin Rana Da Ƙarƙashin Bishiyoyi A Bauchi

A zagayen da Wakilinmu ya yi zuwa gidajen mai a ranar Talata ya tabbatar mafi yawan gidajen mai a Bauchi suna sayar da litar man fetur kan Naira N830, wanda ya ragu sosai idan aka kwatanta da tsohon farashin da ake sayar da litar mai da ya haura Naira N1,100.

ADVERTISEMENT

Duk da wannan ragin, mazauna sun koka cewa kuɗin sufuri bai sauƙa ba. A cewar wasu fasinjoji, tafiyoyi da a baya ke kai N200 yanzu suna kai N400 zuwa N500, lamarin da ke ƙara janyo wahalar ga mutane.

Sun bayyana halin a matsayin rashin adalci kuma ba tare da hujja ba, suna tambayar dalilin da ya sa masu sufuri suka ƙi rage kuɗin Achava daidai da raguwar farashin mai.

LABARAI MASU NASABA

‘Yansanda Sun Kama Shugaban PFIPC, Adeyemi

‘Yansanda Sun Kama Wani Kan Zargin Yi Wa ‘Yan Bindiga Safarar Makamai A Kano

Wani ma’aikacin gwamnati, Musa Abdullahi, ya ce ƙarin kuɗin sufuri ya tilasta masa rage zirga-zirgarsa tare da yin ɗan tafiya domin rage kashe kuɗin zirga-zirga.

Haka nan, wani ɗan kasuwa a Kasuwar Muda Lawal, Mustapha Mohammed, ya ce sufuri yanzu yana cin kaso mai yawa na ribar da yake samu a kullum, lamarin da ya rage masa tara riba mai tsoka.

Wani mazaunin jihar, Adamu Ashiru da ya zanta da Wakilinmu, ya ce a gaskiya wannan abun takaice ne, “Lokacin da ake sayar da litar man fetur a da baya kafin janye tallafin mai da ya sanya farashin ya tashi wurin da muke zuwa a Naira 200 ya dawo Naira 400 ko 500. To, abun takaici yanzu mai ya sauƙo daga sama da Naira 1,100 zuwa N830 amma masu abun hawa ba su sauƙo da farashin ba.”

Mazauna suna kira ga gwamnatin jihar Bauchi da ta shigo cikin lamarin ta hanyar samar da ƙarin motocin sufuri na jama’a domin sauƙaƙa matsalolin sufuri da kuma daidaita kuɗin tafiya a cikin birnin.

Wata ɗaliba a kwalejin kimiyya da fasaha mallakin gwamnatin tarayya da ke Bauchi, Khadija Ibrahim, ta ce shigar da motocin gwamnati masu arha zai rage dogaron fasinjoji ga ‘yan Achaba masu zaman kansu tare da kawo sauƙi mai matuƙar muhimmanci.

A halin da ake ciki, wani ma’aikacin gidan mai na Matriɗ Energy Limited da ke kan titin Dass Road, Bauchi, Saleem Usman, ya shaida ana cewa farashin fetur ya sauƙa a duk faɗin jihar.

Ya ce: “Hakika farashin fetur ya sauƙa a Bauchi. Yawancin gidajen mai suna sayarwa a kan N830 kowace lita. A baya, ya haura N1,000, inda wasu ke sayarwa sama da N1,100.”

Ya ƙara da cewa gidajen mai da ke da alaƙa da Dangote, kamar MRS filling stations, suna sayar da fetur a kan N739 kowace lita.

Ƙoƙarin samun martani daga ƙungiyar masu Achaba da Keke Napep bai samu ba har zuwa lokacin kammala wannan rahoton.

bauchi
Khalid Idris Doya
+ postsBio
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    ATBU Ta Janye Filin Ginin Masallaci Da Ta Bai wa TIMSAN, Ta Amince Kowa Ya Yi Addininsa Yadda Ya Fahimta
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    Ɗan Majalisar Dokokin Bauchi, Hon. Wanzam, Ya Rasu
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    Tsohon Mataimakin Gwamnan Bauchi, Audu Sule Katagum Ya Rasu
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    Kotu Ta Umarci DSS Ta Mutunta Umarninta Kan Shari’ar Filin Firo Na Bauchi

MASU ALAKA

‘Yansanda Sun Kama Shugaban PFIPC, Adeyemi
Labarai

‘Yansanda Sun Kama Shugaban PFIPC, Adeyemi

July 15, 2026
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta
Manyan Labarai

‘Yansanda Sun Kama Wani Kan Zargin Yi Wa ‘Yan Bindiga Safarar Makamai A Kano

July 15, 2026
Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu
Labarai

Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

July 14, 2026
Next Post
Cinikayyar Waje Ta Jihar Xinjiang Ta Kai Sabon Matsayin Ci Gaba A 2025

Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

July 14, 2026
Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

July 14, 2026
An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

July 14, 2026
Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

July 14, 2026
Sin Ta Tsara Bunkasa Darajar Cinikayyar Kayayyaki Zuwa Yuan Tiriliyan 60 Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

Sin Ta Tsara Bunkasa Darajar Cinikayyar Kayayyaki Zuwa Yuan Tiriliyan 60 Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

July 14, 2026
Katsina: Kotu Ta Yanke Wa Hauwa’u Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Taimaka Wa ’Yan Bindiga

Kotu Ta Tsare Shugaban Makaranta Da Malami Kan Zargin Lalata Da Ɗaliba Mai Shekara 6 A Gombe

July 14, 2026
An Bankado Muguwar Aniyar Japan Ta Haifar Da Tashin Hankali A Tekun Kudancin Sin

An Bankado Muguwar Aniyar Japan Ta Haifar Da Tashin Hankali A Tekun Kudancin Sin

July 14, 2026
Layin Dogo Tsakanin Tanzaniya Da Zambiya Ya Zama Shaidar Abota Tsakanin Sin Da Afirka

Layin Dogo Tsakanin Tanzaniya Da Zambiya Ya Zama Shaidar Abota Tsakanin Sin Da Afirka

July 14, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.