ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, June 5, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Mulkin Tinubu A Shekara 3:Ina Aka Fito? Ina Aka Dosa?

by Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
2 hours ago
Tinubu

A yayin da Gwamnatin Shugaba Bola Ahmad Tinubu ta cika shekaru uku saman gadon mulki; al’ummar kasa na bayyana mabambantan ra’ayoyinsu kan salon mulkin da jam’iyyar APC ke jagoranta tun daga 29 ga watan Mayu 2023 zuwa yau.

A bayyane yake cewar gwamnatin Tinubu ta karbi mulki ne a lokacin da tattalin arzikin kasar ke cikin mawuyacin halin rai-kwakwai- mutu- kwakwai wanda ya hada da karyewar  darajar naira, raguwar ajiyar kudaden waje, hauhawar bashin gwamnati, matsin lamba kan tallafin man fetur, tabarbarewar sha’anin ilimi da kiyon lafiya, rashin wutar lantarki, da kuma uwa uba gagarumar matsalar tsaro da ta addabi sassan kasar.

Jim kadan da hawansa mulki, Tinubu ya fara da aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki masu girma wadanda masana da dama ke ganin su ne mafi girma da kowace gwamnati ta taba dauka a Nijeriya a cikin shekaru masu yawa.

ADVERTISEMENT

Wakilinmu ya yi waiwayen baya da cewar babban matakin farko da gwamnatin Tinubu ta dauka da ya girgiza ‘yan Nijeriya shine cire tallafin man fetur tun a cikin jawabinsa na farko bayan rantsar da shi, sai mataki na biyu na sassauta tsarin kasuwar canjin kudaden waje.

Gwamnatin ta bayyana cewa daukar tsauraran matakan sun zama wajibi ne domin ceto tattalin arzikin kasa daga durkushewa, jawo hankalin masu zuba jari da kuma dawo da daidaiton harkokin kudi, sai dai, bayan shafe shekaru uku saman mulki, ra’ayoyin jama’a na ci- gaba da rarrabuwa musamman a tsakanin masu goyon bayan tsarin da masu suka da cewar ba su ga wani canji a kasa ba.

LABARAI MASU NASABA

Har Yanzu Akwai Sauran Rina A Kaba Game Da Makomar Yara A Nijeriya

Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Yi Sanadin Mutuwar Mutane 7 A Bauchi

Masu goyon bayan matakin na nuni da alamun farfadowar manyan muhimman sassan tattalin arziki a alkaluman kudaden gwamnati tare da dawowar amincewar masu zuba jari, yayin da masu suka ke cewa talakawan Nijeriya ne suka fi daukar alhakin wadannan sauye-sauye ba tare da ganin wani gagarumin sauyi a yanayin rayuwarsu ba a mulkin da suka kira  “jiki magayi.”

Hujja mafi karfi da mukarraban gwamnatin Tiinubu ke gabatarwa ita ce gwamnatin na sake fasalin tattalin arziki, a cewar su cire tallafin man fetur ya rage matukar nauyin da ke kan kudaden gwamnati.

A tsawon shekaru, masana tattalin arziki da cibiyoyin kudi na kasa da kasa sun jima suna sukar tsarin tallafin a matsayin marar inganci, mafi tsada kuma hanya mafi sauki ta karfafa cin hanci da rashawa.

Ta hanyar kawo karshen shirin tallafin mai, gwamnati ta samu damar ‘yantar da dimbin kudaden jama’a wadanda za a iya karkata su zuwa ayyukan more rayuwa da ci-gaban jama’a, haka kuma gwamnatin ta aiwatar da gyare-gyare a kasuwar canjin kudaden waje.

Hada kasuwar canjin kudaden waje wuri guda, duk da wahalar da ya haifar ya samu karbuwa daga masu zuba jari da abokan hulda. A kan wannan jami’an gwamnati sun jaddada cewar sauye- sauyen sun kafa tubalin samun bunkasar tattalin arziki mai dorewa a nan gaba.

LEADERSHIP Hausa ta labaro cewar gwamnatin Tinubu a yayin bayyana nasarorin da ta samu ta bayyana cewa a na ci-gaba da aikin shimfida dubban kilomitocin hanyoyin mota da gyaran gyare-gyare wasu hanyoyin a sassa daban-daban na kasar. Manyan ayyuka kamar babbar hanyar Lagos zuwa Calabar da tagwayen hanyar Sakkwato zuwa Badagry gwamnatin ta bayyana cewar muhimmai ne da za su sauya fasalin kasar ta hanyar bunkasa sufuri, inganta hadin kai, kasuwanci da ci- gaban yankuna. Haka kuma, ayyukan sabunta layukan dogo sun ci- gaba da gudana a karkashin gwamnatin da ke mulki.

Haka ma akwai karuwar samun kudaden shigar gwamnati, karin rabon kason kudin wata-wata ga jihohi da kananan hukumomi bayan cire tallafin man fetur sai dai jama’a da dama na kukan gwamnatin tarayya ta karfafawa jihohi ne kawai amma babu kwararan ayyukan nunawa da kyautatawa jama’a da gwamnonin suka aiwatar.

Muhimmin abin da gwamnatin Tinubu ta cimma a cikin shekaru ukun da suka gabata shi ne nasarar aiwatar da daya daga cikin manyan sauye-sauyen tsarin haraji cikin shekaru da dama, inda aka hada dokokin haraji daban-daban tare da sake fasalin yadda ake gudanar da su. A na sa ran wannan gyaran zai taimaka wajen tallafawa ci-gaban kasa a tsayin lokaci tare da karfafa tattalin arzikin kasar.

A ra’ayin ‘yan Nijeriya babban kalubalen da ke gaban gwamnati ba wai kawai cimma sauye-sauyen tattalin arziki ba ne, har ma da tabbatar da amfanin su ya bayyana a zahiri a rayuwar talakawan ‘yan kasa.

Idan a ka ketara kasashen waje kuwa, Nijeriya ta yi kokarin sake fasalin kan ta a matsayin kasa mai daukar hankalin masu zuba jari tare da kara tasiri a matsayin kasa mai muhimmanci a yankin Afurka.

A wannan fannin, gwamnatin Tinubu ta biya basussukan canjin kudaden waje da suka taru wadanda aka kiyasta sun haura dala biliyan 7, lamarin da tuni masu zuba jari suka yaba wanda ya kara daga kimar tattalin arzikin kasar

Sai dai LEADERSHIP Hausa ta ruwaito cewar al’ummar kasa sun bayyana cewar nasarorin da gwamnati ke ikirarin samu ba su yi tasiri a rayuwar al’umma ba ballantana har su saukaka halin kunchi da matsin da talakawa ke ciki ba kamar yadda ‘yan Nijeriya da dama suka bayyana.

A bayyane yake cewar cire tallafin man fetur ya haifar da tashin gwauron zabin farashin sufuri wanda cikin kankanin lokaci ya janyo hauhawar farashin abinci da sauran muhimman kayayyaki a fadin kasa bakidaya ta yadda daga Arewa har Kudu, ba abin da jama’a ke yi face kukan tsadar rayuwa.

Haka ma an samu sauye-sauyen farashin canjin kudaden waje a yayin da halin sayen kayayyakin amfanin iyalai ya ragu kwarai. Magidanta da dama sun tsinci kan su a yanayin kashe kaso mai yawa na kudaden su wajen sayen abinci, biyan kudin makaranta, hidimar magani da sauran bukatun yau da kullum.

A tsayin shekaru uku zuwa yau matsin rayuwa ta zama daya daga cikin manyan siffofin da za a fassara mulkin Tinubu. Duk da cewa wasu alamu na tattalin arziki na nuna fara samun daidaito, ‘yan Nojeriya da dama na ganin har yanzu amfanin wadannan sauye-sauye bai kai ga talakawa ba.

A yau kananan ‘yan kasuwa na fuskantar kalubale sakamakon tsadar gudanar da harkokin kasuwanci a yayin da ma’aikata ke ci-gaba da fuskantar matsin lamba kasancewar albashinsu ba zai wadace su ba a bisa ga hauhawar farashi wanda a kan hakan ne a kwanan nan kungiyar gwamnoni ta bukaci Shugaba Tinubu da ya kara mafi karancin albashin ma’aikata daga naira dubu 72 zuwa naira dubu 100.

Haka ma Bankin duniya da sauran masu sa- ido sun ci- gaba da jaddada cewa talaucin da ‘yan Nijeriya ke fama na nan daram duk da an samu ci- gaba a wani bangare na tattalin arziki. Sai dai duk da cewa tattalin arzikin kasa ya bunkasa a bisa ga samun karin kudaden shiga, jama’a da dama na ganin matakan inganta rayuwar al’umma domin rage masu radadin manufofiin gwamnati masu tsauri ba su wadatar ba ko kadan.

A cikin shekaru uku fannin tsaro na ci-gaba da kasancewa wani babban abin damuwa da ke hanawa ‘yan Nijeriya bacci da ido biyu duk kuwa da cewa a wasu wuraren gwamnati ta samu nasara a yaki da ‘yan ta’adda da kungiyoyin masu aikata laifuka; rashin tsaro har yanzu na ci- gaba da shafar sassa da dama na kasar ta yadda jama’a ke kuka da kokawa kan yadda ‘yan bindiga suka mayar da yankunan su lahira kusa.

Al’ummomi a Arewa- maso- Gabas, Arewa- maso- Yamma da wasu yankuna a Tsakiyar Nijeriya na ci-gaba da fuskantar kalubale daban-daban a yayin da ‘yan bindiga ke cin karen su ba babbaka a ta’addanci da fashi da makami zuwa rikice-rikicen kabilanci da garkuwa da mutane.

Duk da yake gwamnati na jaddada cewar ta karfafa ayyukan tsaro, amma har yanzu ‘yan kasa da dama na jiran ganin ingantaccen sauyi a rayuwarsu ta yau da kullum domin ‘yan ta’addan ba su daina yi masu kisan gilla ba, ba su daina garkuwa da su ba, ba su daina kone garuruwan su ba kuma ba su daina tilasta masu biyan harajin noma ba.

Har ila yau, fannin da aka fi yawan magana a kai shi ne na wutar lantarki domin kuwa a cikin shekaru ashirin da suka gabata, gwamnati bayan gwamnati, sauyi a wannan fanni ya gagara kaiwa ga-gaci. Abin takaici shi ne fannin da aka zuba tiriliyoyin kudi ba tare da samun sakamako ba. A yau, ba abin da ya canza, ‘yan Nijeriya na ci- gaba da koke kan tsadar kudin wuta, lissafin kimantawa na mita da kuma yawaitar faduwar layin wutar lantarki.

Watanni kafin rantsar da shi a lokacin yekuwar neman zabe, Tinubu ya yi alkawarin samar da wutar lantarki ba tare da katsewa ba ga ‘yan Nijeriya idan aka zabe shi, har ma ya bayyana cewa ka da a sake zabensa idan har ya kasa cika wannan alkawari lamarin da har zuwa yau al’ummar Nijeriya na ci-gaba da zama a cikin zafi da tsananin duhu domin babu wuta babu alamarta, hasalima wasu da dama sun zabi fara amfani da wuta mai aiki da hasken rana wadda ita kan ta ta gagari talaka.

Haka kuma gwamnatin Tinubu ta yi alkawarin samar da guraben aikin yi ga matasan Nijeriya da kuma inganta yanayin kasuwanci ga kananan da matsakaitan ‘yan kasuwa, kamar kuma yadda ta yi alkawarin samar da ingantaccen yanayi ga manoma domin noma albarkatun gona a cikin kwanciyar hankali da kara wadata kasa da abinci, bayar da bashi ga manoma, wadanda alkawura ne da a yau da gwamnatin ta cika shekaru uku a kasa amma ba abin nunawa a kasa.

Jajantawa Nijeriya Ya Kamata A Yi – Atiku

Jagoran jam’iyyar adawa ta ADC kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana cewar jajantawa al’ummar Nijeriya ya kamata a yi a wadannan shekarun yana cewar a cike da hawaye aka rubuta sakamakon shekaru uku na mulkin Tinubu a Nijeriya.

Wazirin Adamawa wanda shine dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar ADC ya bayyana hakan a wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan hulda da jama’a, Phrank Shaibu ya fitar a inda ya ce yayin da gwamnatin Tinubu ke bikin cika shekaru uku a kan mulki tare da tallace- tallace a kafafen yada labarai masu tsada da jawaban yabon kai amma jama’a na can cike da hawaye dauke da yunwa da matasa cike da bakin cikin rashin aikin yi, rushewar kasuwanci ga kuma ‘yan ta’adda can na cin karensu ba babbaka a yayin da gwamnati ke kallon abin ba tare da daukar kwakkwaran matakii ba.

A cewar Atiku kowace gwamnati na da ‘yancin bayyana ra’ayinta, amma babu wata gwamnati da ke da ‘yancin kirkirar ta ta gaskiyar. “Shekaru uku da suka gabata Shugaba Tinubu ya yi alkawarin kyautatawa ‘yan Nijeriya amma ba abin da ‘yan kasa suka samu face sabuwar wahala, sabon rashin tsaro da kuma sabon talauci.

“A yau, miliyoyin ‘yan Najeriya ba su iya biyan bukatun rayuwar yau da kullum, farashin abinci ya yi tashin gwauron zabi fiye da karfin iyalai, hauhawar farashi ya zama wata azaba mai kama da haraji ga talakawa, kananan da matsakaitan ‘yan kasuwa sun rufe harkokinsu, masu zuba jari na gujewa yanayin rashin tabbas, darajar naira ta zube kasa yayin da jama’a ba su da sauran halin sayen kayayyaki.”

Ya ce abin da ya kara tsananta wannan gazawa shi ne yadda gwamnatin Tinubu ke ci-gaba da ciwo bashi ba tare da taka-tsantsan ba, ya ce gwamnatin ta karbo tiriliyoyin naira da sunan bunkasa abubuwan more rayuwa da tattalin arziki, amma har yanzu ‘yan Nijeriya ba su ga sauyi mai ma’ana a rayuwarsu ta yau da kullum ba.

A cewar Atiku rahotanni sun nuna cewa yayin da Gwamnatin Tarayya ta karbo bashin kusan naira tiriliyan 11.9 cikin watanni tara kacal, a na zargin kusan tiriliyan N3.1 ne kawai aka kashe a ayyukan ci- gaba, saboda haka ‘yan Nijeriya na da hakkin yin tambaya mai sauki ta ina aka kai sauran kudaden su?

Ya ce “Abin da ya fi tayar da hankali shi ne yadda wani babban bangare na kudin da ake cewa an kashe a kan more rayuwa ya fi karkata ne ga wasu manyan ayyuka kamar tagwayen hanyar Lagos zuwa Calabar da hanyar Badagry zuwa Sokoto wadanda aka bai wa wani kamfani mallakar wani dan kasuwa da Tinubu ya taba bayyana a fili a matsayin abokin huldarsa.

Idan alkawuran da gwamnati ta yi wa jama’a na samun ribar sauye-sauyen tattalin arziki suka fara bayyana ta hanyar raguwar hauhawar farashi, daukar matasa aikin yi, inganta tsaro da kuma kyautata rayuwar jama’a, gwamnati za ta iya cewa an tabbatar da sahihancin matakan da ta dauka amma idan hakan bai faru ba, masu suka za su ci- gaba da cewa ‘yan Nijeriya kawai sun sha wahala mai tsanani ne  ba tare da samun ribar da aka yi musu alkawari ba.

Yayin da Nijeriya ke kusantar babban zaben 2027, tambaya guda da ke ci- gaba da zama ginshikin tattaunawar ‘yan kasa ita ce shin wahalhalu da sauye-sauyen suka haifar sun samar da isasshen sakamako da zai tabbatar da cewa an cancanci daukar wannan mataki ko akasin hakan?

A cikin shekaru uku da suka gabata, wadannan batutuwan sun ci-gaba da zama manyan manufofin gwamnatin Tinubu don haka nasara ko gazawar da aka samu a kai za su tabbatar da ko ‘yan Nijeriiya za su sake bashi wata dama a 2027 ko akasin hakan.

Tinubu
Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
+ postsBio
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    A Yayin Da Babban Bankin Ƙasa (CBN) Ke Yaƙi Da Laifukan Intanet
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    Halin Da Matsalar Tsaro Ta Jefa ‘Yan Gudun Hijira A Arerwacin Nijeriya
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    Sanata Tambuwal Ya Sadaukar Da Takararsa Ga Faruku Yabo
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    Dan-Iya Ya Zama Ɗan Takarar Gwamnan ADC A Sakkwato

MASU ALAKA

Har Yanzu Akwai Sauran Rina A Kaba Game Da Makomar Yara A Nijeriya
Manyan Labarai

Har Yanzu Akwai Sauran Rina A Kaba Game Da Makomar Yara A Nijeriya

June 5, 2026
Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Yi Sanadin Mutuwar Mutane 7 A Bauchi
Manyan Labarai

Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Yi Sanadin Mutuwar Mutane 7 A Bauchi

June 4, 2026
Arsenal Na Dab Da Ɗaukar Jeremy Monga Daga Leicester City
Wasanni

Arsenal Na Dab Da Ɗaukar Jeremy Monga Daga Leicester City

June 4, 2026
Next Post
Sabon Rikicin Manoma Da Makiyaya yayi Ajalin Mutuwar Mutane 7 A Bauchi

Sabon Rikicin Manoma Da Makiyaya yayi Ajalin Mutuwar Mutane 7 A Bauchi

Discussion about this post

LABARAI MASU NASABA

Dorewar Tattalin Arzikin Duniya Ya Dogara Ne Kan Ayyukan Tashoshin Jiragen Ruwa Na Afrika Ta Tsakiya, Cewar Dantsoho

Dorewar Tattalin Arzikin Duniya Ya Dogara Ne Kan Ayyukan Tashoshin Jiragen Ruwa Na Afrika Ta Tsakiya, Cewar Dantsoho

June 5, 2026
Sabon Rikicin Manoma Da Makiyaya yayi Ajalin Mutuwar Mutane 7 A Bauchi

Sabon Rikicin Manoma Da Makiyaya yayi Ajalin Mutuwar Mutane 7 A Bauchi

June 5, 2026
Babu Wani Shiri Na Kwaso ‘Yan Nijeriya Daga Falasdin Ko Isra’ila –Gwamnatin Tarayya

Mulkin Tinubu A Shekara 3:Ina Aka Fito? Ina Aka Dosa?

June 5, 2026
Hajji 2026: Mahajjata 1,905 Sun Dawo Nijeriya Daga Saudiyya

Hajji 2026: Mahajjata 1,905 Sun Dawo Nijeriya Daga Saudiyya

June 5, 2026
Har Yanzu Akwai Sauran Rina A Kaba Game Da Makomar Yara A Nijeriya

Har Yanzu Akwai Sauran Rina A Kaba Game Da Makomar Yara A Nijeriya

June 5, 2026
Matatar Dangote Ta Ƙara Yawan Man Da Take Tacewa Zuwa Ganga 700,000

Matatar Dangote Ta Ƙara Yawan Man Da Take Tacewa Zuwa Ganga 700,000

June 4, 2026
Ƴansanda Sun Daƙile Harin Ƴan Bindiga, Sun Kwato Shanu 25 A Sakkwato

Ƴansanda Sun Daƙile Harin Ƴan Bindiga, Sun Kwato Shanu 25 A Sakkwato

June 4, 2026
Takunkumin Amurka Ya Haifar Da Mummunan Tasiri Ga Tsarin Samar Da Kayan Latironi Na Duniya

Takunkumin Amurka Ya Haifar Da Mummunan Tasiri Ga Tsarin Samar Da Kayan Latironi Na Duniya

June 4, 2026
Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Kashe Mutane 7, Ya Jikkata 6 A Bauchi

Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Kashe Mutane 7, Ya Jikkata 6 A Bauchi

June 4, 2026
Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Yi Sanadin Mutuwar Mutane 7 A Bauchi

Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Yi Sanadin Mutuwar Mutane 7 A Bauchi

June 4, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.