Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya taya Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, murnar sake lashe zaɓen gwamnan jihar, yana mai cewa nasarar ta nuna zaɓin al’ummar jihar da suka bayyana ra’ayinsu ta hanyar ƙuri’a.
Atiku ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Lahadi, inda ya ce sakamakon zaɓen ya nuna abin da al’ummar Osun suka zaɓa. Ya kuma yaba wa al’ummar jihar bisa yadda suka gudanar da zaɓen cikin lumana, tare da yi wa Adeleke fatan samun nasara a wa’adinsa na biyu.
Ya ce: “Ina taya Gwamna Ademola Adeleke murnar sake zaɓensa a matsayin Gwamnan Jihar Osun. Nasararsa ta nuna zaɓin al’ummar Osun kamar yadda suka bayyana a akwatin zaɓe.” Atiku ya ƙara da cewa ya yaba wa al’ummar jihar bisa sha’awarsu da kuma yadda suka shiga zaɓen cikin lumana.
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ayyana Adeleke, ɗan takarar jam’iyyar Accord, a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan Jihar Osun da aka gudanar, bayan ya samu ƙuri’a 511,067.
Adeleke ya doke babban abokin hamayyarsa, Bola Oyebamiji na jam’iyyar APC, wanda ya samu ƙuri’a 444,815. Atiku ya ce yana fatan Adeleke zai ci gaba da samun nasara wajen yi wa al’ummar Osun hidima a wa’adinsa na biyu.














