ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, July 14, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Nazarin Yadda Jiragen Saman Yaƙin Sojoji Ke Ci Gaba Kashe Fararen Hula A Nijeriya

by Rabi'u Ali Indabawa
3 months ago

Ƙungiyoyin farar hula da masana harkokin tsaro sun nuna matuƙar damuwa da rashin jin daɗi kan harin sama da rundunar sojin saman Nijeriya, ta kai a wata kasuwa ta mako-mako da ke kan iyakar jihohin Borno da Yobe. Rahotanni sun nuna cewa harin ya yi sanadin mutuwar mutum sama da 200, waɗanda galibinsu ƴan kasuwa, tare da jikkata wasu da dama.

Lamarin ya faru ne a yammacin ranar Asabar a kasuwar Jilli, wadda ke tsakanin ƙananan hukumomin Gubio da Geidam a jihohin Borno da Yobe. An rawaito cewa an kai harin saman ne yayin wani farmakin soja da aka nufa kan ƴan ta’addan Boko Haram da ake zargin suna aiki a yankin.

  • CMG Ya Gudanar Da Babban Taron Masu Kirkirar Manyan Shirye-Shirye Da Fina-Finai
  • Tsohon Sanatan Gombe, Bayero Nafada, Ya Fice Daga PDP Bayan Ganawa da Shugabannin APC
  • ADC Ta Nemi A Binciki Nafiu Bala Bayan INEC Ta Ƙaryata Iƙirarinsa
  • Sojoji Sun Daƙile Harin ISWAP A Borno
  • Na Yi Tsayin-daka Domin Cika Alƙawarin Ƙasata Nijeriya

A wata sanarwa da aka fitar a ranar Lahadi, sashen sojin sama na rundunar haɗin gwiwa ta Joint Task Force (North East), Operation HADIN KAI (OPHK), ta bakin kakakinta, Sani Uba, ya ce an kashe ƴan ta’adda da dama a harin.

ADVERTISEMENT

Ya ƙara da cewa an lalata motocinsu, yayin da sauran waɗanda suka tsira suka tsere ta hanyoyi daban-daban.

Sai dai bayan rahotannin da ke fitowa kan cewa fararen hula sun mutu, rundunar sojin saman Nijeriya, Nigerian Air Force, ta sanar a wata sabuwar sanarwa cewa ta fara bincike kan lamarin.

LABARAI MASU NASABA

NDLEA Ta Cafke Ƴar Shekara 67 Da Hodar Iblis Da Aka Ɓoye A Cikin Ayaba

Gwamnatin Kaduna Ta Yaba Wa ONSA Kan Shirin Horon Masu Tsaron Daji ‘Forest Guards’

NAF ta ce tana ɗaukar zarge-zargen da muhimmanci, inda ta ƙaddamar da sashen binciken illar fararen hula (CHAI-Cell) domin gudanar da bincike a wurin da abin ya faru.

Kasuwar mako-makon na jawo ƴan kasuwa da masu saye daga al’ummomin da ke kewaye kamar Gubio, Futchimiram da Benisheikh a Jihar Borno, da kuma Gurokayeya da Geidam a Jihar Yobe.

Majiyoyi da dama sun ce jirgin yaƙin da ya kai harin yana bibiyar wasu da ake zargin ƴan ta’adda ne da suka je kasuwar domin karɓar haraji daga ƴan kasuwa da kuma neman kayayyaki.

Wani ganau mai suna Umar Bomai ya shaida cewa kusan ƴan kasuwa 200 ne suka mutu a ƙauyen Jilli da ke yankin Futchimiram a Ƙaramar Hukumar Geidam, yana mai cewa harin ya auku ne a lokacin da kasuwar ke cike da hada-hadar kasuwanci.

“Lamarin ya faru ne yayin da ake gudanar da kasuwanci. Da farko mun ga jirgi guda yana zagayawa sama da kasuwar, muna zaton yana bayar da tsaro. Amma daga baya al’amura suka sauya lokacin da ƙarin jirage suka iso har suka kai huɗu gaba ɗaya.”

“Ba zato ba tsammani muka ji wata ƙara mai ƙarfi, ba tare da sanin cewa harin sama ba ne. Kafin mu fahimci abin da ke faruwa, jiragen yaƙi suka fara kai hare-hare, mutane kuma suka fara gudu domin tsira da rayukansu.

“Duk da cewa mutane suna ƙoƙarin tserewa, hare-haren sun ci gaba. Mun ƙirga gawarwaki kusan 200 a wurin, kuma adadin na iya zarce haka,” in ji shi.

Wani mazaunin yankin, Babagana Bukar, wanda mahaifinsa na cikin waɗanda suka mutu, ya ce adadin waɗanda suka rasu na iya haura 200, domin ana ci gaba da gano ƙarin gawarwaki.

“Yawan waɗanda suka mutu na iya wuce 200. Wasu sun mutu a kasuwa, wasu kuma an kashe su a dazuka yayin da suke ƙoƙarin tserewa.

“Har a asibiti ma, mutane 11 daga cikin waɗanda aka kwantar sun rasu yayin jinya. Har yanzu muna ci gaba da ƙirga da kuma gano ƙarin gawarwaki,” in ji shi.

Da aka tuntuɓi kansilan yankin Futchimiram, Malam Lawan Zanna, ya ce kusan mutane 200 ne suka mutu a lamarin.

“Har yanzu ba mu tattara ainihin adadin waɗanda suka mutu ba, amma wani ganau ya tabbatar min da cewa sama da mutane 200 ne suka mutu a harin.

“Wataƙila za a samu cikakken bayani gobe, amma a halin yanzu, abin da zan iya cewa shi ne akwai mutane 24 da aka kwantar a Asibitin Ƙwararru na Geidam da kuma Asibitin Koyarwa na Damaturu,” in ji Zanna.

Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters, ya naƙalto mazauna yankin, su ma sun rawaito cewa fararen hula kusan 200 ne suka mutu a harin, wanda ya tabbatar da adadin da kansilan da sauran mazauna yankin suka bayar.

Jihar Yobe ta tabbatar da mutuwar fararen hula, yayin da al’umma ke roƙo domin bayar da gudunmawar jini.

Hukumar bada agajin gaggawa ta Jihar Yobe (SEMA) ta bayyana lamarin a matsayin wani harin sama na kuskure da ya shafi fararen hula a kasuwar Jilli ta ranar Asabar a Ƙaramar Hukumar Gubio ta Jihar Borno.

A cewar hukumar, wasu daga cikin waɗanda abin ya shafa ƴan kasuwa ne daga Ƙaramar Hukumar Geidam a Jihar Yobe.

SEMA ta ce bisa umarnin gwamna Mai Mala Buni, an riga an ƙulla tsarin agajin gaggawa tare da tura tawagogin tantancewa zuwa wurin da abin ya faru.

Hukumar ta buƙaci jama’a su kwantar da hankalinsu tare da gujewa yaɗa jita-jita, musamman kan adadin waɗanda suka mutu, tana mai tabbatar da cewa ana ci gaba da ƙoƙarin kai agajin jin ƙai.

Haka kuma, gwamnatin Jihar Yobe ta tabbatar da cewa fararen hula da dama, galibinsu ƴan kasuwa ne, sun mutu a harin.

Mai bai wa gwamnan shawara kan harkokin tsaro, Birgediya Janar Abdulsalam Dahiru (mai ritaya), ya ce: “Bangaren sojin sama na Operation HADIN KAI ya kai harin sama a Jilli, wuri da aka sani da mafakar Boko Haram a Ƙaramar Hukumar Gubio ta Jihar Borno, a ranar Asabar, 11 ga Afrilu, 2025.

“Wasu mazauna Geidam da suka je kasuwar Jilli sun shiga cikin waɗanda abin ya shafa. An kwashe su zuwa Asibitin Ƙwararru na Geidam inda ake kula da su.”

Gwamnatin ta sake jaddada cewa Jilli wuri ne da ake sanin ƴan ta’adda na amfani da shi, kuma yana cikin wuraren da ake gudanar da yaƙi da ta’addanci, tare da roƙon jama’a su kwantar da hankalinsu.

Wani mai aikin sa-kai a al’umma, Idriss Alhaji Baffa, ya shaida cewa Asibitin Ƙwararru na Geidam ya cika maƙil kuma yana buƙatar gadon asibiti da masu bayar da jini cikin gaggawa.

“Babu isassun gadon kwanciya a asibitin. Ana kula da wasu marasa lafiya a ƙasa, wasu kuma a cikin motoci saboda rashin wuri.

“Mutane da dama na buƙatar ƙarin jini cikin gaggawa. Duk da cewa wasu na son bayar da jini, samun jini mai dacewa ya zama ƙalubale. Lamarin na da matuƙar tsanani, kuma muna buƙatar taimako cikin gaggawa,” in ji shi.

Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Wasu Fusatattun Mutane Sun Lakaɗa Wa Mutum Biyu Duka Har Lahira A Kaduna
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Mun Ɗauki Nauyin Karatun Masu Digiri Ta Hanyar Sayar Da Ƙosai Da Ƙuli-ƙuli —Wasu Ƴan Kasuwa
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Adadin Mutanen Da Tsananin Zafi Ya Kashe A Turai Ya Haura Dubu 1,300 —WHO
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Pakistan Ta Kashe Mutum 36 A Hare-haren Da Ta Kai Kan Iyakarta Da Afghanistan

MASU ALAKA

Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Tsaro

NDLEA Ta Cafke Ƴar Shekara 67 Da Hodar Iblis Da Aka Ɓoye A Cikin Ayaba

July 11, 2026
Gwamnatin Kaduna Ta Yaba Wa ONSA Kan Shirin Horon Masu Tsaron Daji ‘Forest Guards’
Tsaro

Gwamnatin Kaduna Ta Yaba Wa ONSA Kan Shirin Horon Masu Tsaron Daji ‘Forest Guards’

July 9, 2026
Sojoji Sun Kama Mai Kai Wa Ƴan Ta’adda Kayan Aiki A Zamfara
Tsaro

Sojoji Sun Kama Mai Kai Wa Ƴan Ta’adda Kayan Aiki A Zamfara

June 25, 2026
Next Post
Sauya Sheƙa: An Gaza Cimma Matsaya Kan Komawar Gwamnan Bauchi APC

Sauya Sheƙa: An Gaza Cimma Matsaya Kan Komawar Gwamnan Bauchi APC

LABARAI MASU NASABA

CMG Ya Gudanar Da Babban Taron Masu Kirkirar Manyan Shirye-Shirye Da Fina-Finai

CMG Ya Gudanar Da Babban Taron Masu Kirkirar Manyan Shirye-Shirye Da Fina-Finai

July 14, 2026
Tsohon Sanatan Gombe, Bayero Nafada, Ya Fice Daga PDP Bayan Ganawa da Shugabannin APC

Tsohon Sanatan Gombe, Bayero Nafada, Ya Fice Daga PDP Bayan Ganawa da Shugabannin APC

July 14, 2026
ADC Ta Nemi A Binciki Nafiu Bala Bayan INEC Ta Ƙaryata Iƙirarinsa

ADC Ta Nemi A Binciki Nafiu Bala Bayan INEC Ta Ƙaryata Iƙirarinsa

July 14, 2026
Sojoji Sun Kashe ’Yan Ta’adda 3, Sun Ƙwato Makamai A Sakkwato

Sojoji Sun Daƙile Harin ISWAP A Borno

July 14, 2026
Na Yi Tsayin-daka Domin Cika Alƙawarin Ƙasata Nijeriya

Na Yi Tsayin-daka Domin Cika Alƙawarin Ƙasata Nijeriya

July 14, 2026
Tsaka mai wuyar Infantino da Koma bayan mulkin yamma

Tsaka mai wuyar Infantino da Koma bayan mulkin yamma

July 14, 2026
“Buhari Ya Taɓa tambaya Ta Mutane Nawa Na Kashe Saboda Yawan Azumin Dana Ke Yi”

“Buhari Ya Taɓa tambaya Ta Mutane Nawa Na Kashe Saboda Yawan Azumin Dana Ke Yi”

July 14, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Ce Za A Gurfanar Da Tubabbun ’Yan ta’addan Da Suka Sake Aikata Manyan Laifuka

Gwamnatin Tarayya Ta Ce Za A Gurfanar Da Tubabbun ’Yan ta’addan Da Suka Sake Aikata Manyan Laifuka

July 14, 2026
Tinubu Ya Gana da Gwamnan Kwara Bayan Harin Ta’addanci Da Ya Yi Ajalin Sama Da Mutane 160

Kyawawan Manufofin Buhari Za Su Ci Gaba Da Yi Wa ’Yan Nijeriya Tasiri – Tinubu

July 14, 2026
Abin Da Ake Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin” Da Aka Yanke Wa Sin Na Kashin Kanta Ba Shi Da Wani Amfani

Abin Da Ake Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin” Da Aka Yanke Wa Sin Na Kashin Kanta Ba Shi Da Wani Amfani

July 13, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.