ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ramadan: Gwamna Uba Sani Ya Yi Kira Ga Malamai Da Su Ƙarfafa Haɗin Kai

by Shehu Yahaya and Sulaiman
7 months ago
Ramadan

Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya bukaci malamai na addinin Musulunci da kafafen yaɗa labarai tare da kafafen sadarwar zamani da su yi amfani da watan Ramadan mai zuwa a matsayin wata babbar dama ta ƙarfafa zaman lafiya, haƙuri da haɗin kan ƙasa.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wajen taron Shekara-shekara na Kafin Ramadan na 2026 da Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta shirya a Babban Hedkwatarta da ke Kaduna.

ADVERTISEMENT
  • CBN Ta Amince Wa Bankin Masana’antu Buɗe Sashin Bankin Da Babu Riba
  • Dalilin Da Ya Sa Gwamnan Bauchi Ya Sauke Kwamishinan Tsaron Cikin Gida

Gwamna Uba Sani, wanda Sakataran Gwamnatin Jihar Kaduna, Dakta Mu’azu Meyare, ya wakilta, ya jaddada cewa matsalolin tattalin arziƙi, tsaro da zamantakewa da ƙasar ke fuskanta a halin yanzu sun ƙara ɗora nauyi a wuyan malamai da kafafen yaɗa labarai wajen jagorantar al’umma da hikima, ladabi da tausayi.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Akan hakan , Gwamnan ya yi kira ga malamai da su tabbatar da cewa darussan tafsiri da sauran shirye-shiryen wayar da kai na ramadan suna ƙarfafa haɗin kai, zaman lafiya, adalcin zamantakewa da kula da marasa galihu.

Ya bayyana cewa watan ramadan, wata ne mai tsarki da rahama, tarbiyya inda ya bukaci al’umma da suyu amfani da watan wajen ƙarfafa dabi’un sadaka, kishin ƙasa da addu’o’i ga ƙasa da shugabanninta.

Ya ƙara da cewa addu’o’i na gaskiya a wannan wata mai albarka suna da muhimmiyar rawa wajen warkar da ƙasa.

Gwamnan ya kuma yi kira ga gidajen rediyo, talabijin da kafafen sada zumunta na zamani da su kiyaye ƙa’idojin ƙwarewa da ladabi wajen watsa tafsiri da sauran shirye-shiryen addini, yana mai gargadin cewa a guji saƙonnin da ka iya tayar da fitina ko rarrabuwar kai.

Ya kumq tunatar da mahalarta cewa yi wa bil’adama hidima na daga cikin manyan ibadu a Musulunci.yana mai bayyana jajircewar Gwamnatin Jihar Kaduna ga shugabanci mai haɗa kowa da kowa, Gwamnan ya ce tsarin haɗin kai tsakanin addinai da gwamnati ta kafa ya taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin mabambantan addinai.

Hakazalika, ya tabbatar da goyon bayan gwamnati ga ilimin addini da tattaunawa, tare da yin alƙawarin ci gaba da haɗin gwiwa da JNI da sauran ƙungiyoyin addini.

Gwamnatin Jihar Kaduna ta sake jaddada shirinta na yin aiki kafada da kafada da malamai da kafafen yaɗa labarai domin zurfafa haƙuri, ƙarfafa haɗin kai da tabbatar da watan Ramadan mai cike da zaman lafiya da albarkar ruhi.

Taron ya gudana ne ƙarƙashin jagorancin Mai Martaba Shehun Borno, Alhaji Dakta Abubakar Ibn Umar Garba Abba Kiyari El-Kanemi, wanda ya jagoranci tattaunawar da ta mayar da hankali kan wa’azi mai alhaki, jituwa ta addini da kare zaman lafiya a lokacin Ramadan da bayan sa.

Taron Kafin Ramadan na JNI ya samu halartar manyan mutane daga sassa daban-daban na ƙasar, ciki har da sarakunan gargajiya, fitattun malamai da shugabannin al’umma, lamarin da ya nuna muhimmancin taron a matakin ƙasa wajen tsara tafarkin wa’azi da koyarwar addini gabanin watan Ramadan.

Ramadan
Shehu Yahaya
+ posts Bio
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Gwamna Uba Sani Ya Yi Jimamin Rasuwar Dan Jarida Jafaru Yakubu Maitama
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Gwamnatin Kaduna Ta Fara Rabon Takin Zamani Kyauta Ga Manoma 150,000
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Zaka Iya Sayar da Takin Gwamnati Ka Sayawa Iyalinka Kaji — Imam Nuradden
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Rashin Tsaro: ACI Zata Kira Taron Gaggawa Na Masu Ruwa Da Tsaki A Kaduna
Ramadan
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto
  • Sulaiman
    PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
Next Post
Xi Jinping Ya Yi Rangadin Ayyukan Kirkire-Kirkiren Kimiyya Da Fasaha A Beijing

Xi Jinping Ya Yi Rangadin Ayyukan Kirkire-Kirkiren Kimiyya Da Fasaha A Beijing

LABARAI MASU NASABA

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.