ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Saboda Iyalina Na Zabi Buga Wa Nijeriya Kwallo A Maimakon Ingila -Ola Aina

by Abba Ibrahim Wada
4 months ago
Ola

Dan wasan bayan kungiyar kwallon kafa ta Nottingham Forest Ola Aina ya bayyana cewa dangantaka ta iyali da kuma jin cewa shi dan Nijeriya ne sun taka muhimmiyar rawa a shawarar da ya yanke na wakiltar Nijeriya maimakon Ingila a matakin kasa da kasa.

Aina, yayin da yake magana da manema labarai a Nottingham Forest, ya bayyana cewa asalinsa na Nijeriya ya jagoranci zabin da ya yi na wakiltar kasar duk da cewar zai iya wakiltar kasar Ingila, an haife shi a Southwark dake birnin Landan, amma kuma iyayensa yan Nijeriya ne, Aina ya cancanci bugawa kasashen biyu wasa inda har ya wakilci Ingila a matakin matasa na ‘yan kasa da shekara 16 da 20.

Hakazalika ya kuma samu kira daga tawagar ‘yan kasa da shekara 21 a shekarar 2015, wani mataki da ya nuna yiwuwar samun gurbi tare da babbar tawagar kasar, duk da haka a shekarar 2017 Aina ya karbi gayyatar yin atisaye tare da babbar tawagar Nijeriya (Super Eagles) a Landan.

ADVERTISEMENT

“An haife ni kuma na girma a Landan, na yanke shawarar buga wa Nijeriya wasa, shawara ce da na yanke lokacin da nake kimanin shekaru 20, daga nan ne iyayena suka bani kwarin gwiwa, damar ta zo mini kuma na yi tunanin ita ce daidai a lokacin, don haka na dauki hakan da hannu biyu”, in ji shi.

Saboda ya riga ya wakilci Ingila a matakin matasa, Aina ya bukaci amincewar FIFA domin canza kasa, amincewar ta zo a lokacin da zai fara buga wa Nijeriya wasa a wasan share fage na gasar cin kofin Duniya da suka buga da kasar Zambia a watan Oktoban shekarar 2017.

LABARAI MASU NASABA

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana

“Iyalina suna alfahari da ni sosai, musamman lokacin da nake sanye da rigar Super Eagles, sun fi son rigar fiye da ni, saboda haka abin alfahari ne a wajena” in ji shi, tun bayan da ya sauya kasa, Aina ya fuskanci matsaloli daban-daban, inda ta kai ga an cire shi daga cikin tawagar Nijeriya a gasar cin kofin Duniya ta shekarar 2018, yayin da Super Eagles kuma ta kasa samun cancantar shiga gasar cin kofin duniya ta shekarar 2022 da 2026.

Duk da haka, ya samu nasara a gasar cin kofin kasashen Afirka, inda ya lashe tagulla a shekarar 2019 da azurfa a shekarar 2023, a matakin kungiya, tsohon dan wasan na Chelsea a halin yanzu yana cikin kungiyar da za ta fafata da Aston Billa a wasan kusa da na karshe na gasar UEFA Europa League.

Ola
Abba Ibrahim Wada
Website |  + postsBio
  • Abba Ibrahim Wada
    Yaushe Za A Fara Kofin Zakarun Turai
  • Abba Ibrahim Wada
    Messi Ya Yi Ritaya A Argentina: Da Me Za Mu Iya Tuna Gwarzon Duniyar?
  • Abba Ibrahim Wada
    Su Waye ‘Yan wasan Nijeriya Da Za Su Buga Gasar Firimiyar Ingila Ta Bana?
  • Abba Ibrahim Wada
    Chelsea A Ƙarƙashin Xavi Alonso

MASU ALAKA

Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana
Wasanni

Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana

September 8, 2026
Kofin Duniya: Yau Falconets Za Su Kece Raini Da Spain
Wasanni

Kofin Duniya: Yau Falconets Za Su Kece Raini Da Spain

September 7, 2026
Next Post
Kamfanin Mercedes Zai Shigar Da Osimhen Kara Kan Rashin Biyan Bashi

Kamfanin Mercedes Zai Shigar Da Osimhen Kara Kan Rashin Biyan Bashi

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.