Tsohon hadimin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad, ya shiga tattaunawa a kafafen sada zumunta bayan yadda ya yi magana da harshen Turanci a wani taron tattaunawa da aka gudanar a dandalin X, lamarin da ya sa wasu masu amfani da kafafen suka fara zargin cewa yana amfani da fasahar basirar na’ura (AI) wajen rubuce-rubucensa.
Tattaunawar, mai taken “From Online to Grassroot: The Role of CBM in Youth Mobilization”, wadda Dandalin City Boy Movement ya shirya, ta tattauna rawar da ƙungiyar ke takawa wajen wayar da kan matasa da ƙarfafa shigarsu harkokin siyasa, wanda Bashir Ahmad, na daga cikin waɗanda suka yi tsokaci yayin tattaunawar.
Zargin ya samo asali ne daga bambancin da wasu masu amfani da kafafen sada zumunta suka lura da shi tsakanin yadda Bashir, ya yi magana da Turanci yayin tattaunawar da kuma yadda rubuce-rubucensa ke fitowa a shafukansa na sada zumunta, inda yake bayyana ra’ayoyinsa kan batutuwa daban-daban cikin ingantaccen Turanci.
Wasu daga cikin masu amfani da X, sun yi ta bayyana ra’ayoyinsu a sashen sharhi, inda suka yi tambayoyi kan yiwuwar amfani da AI wajen tsara rubuce-rubucensa. Sai dai, wannan zargi ya ta’allaka ne kan yadda ya yi magana a wannan tattaunawa, ba tare da wata hujja kai tsaye da ta tabbatar da amfani da fasahar ba.
Lamarin ya kuma sake tayar da muhawara kan yadda AI ke sauya yadda mutane ke rubutu da sadarwa a kafafen sada zumunta, musamman wajen tsara saƙonni cikin ingantaccen harshe. Duk da haka, iya rubutu da wani harshe ba lallai ya nuna cewa mutum zai iya yin magana da shi cikin ƙwarewa iri ɗaya ba.
Sai dai har ya zuwa fitowar wannan rahoton, babu wata hujja da aka gabatar da ta tabbatar da cewa Bashir Ahmad yana amfani da AI wajen rubuce-rubucensa, illa dai kawai ra’ayoyin jama’a a shafukan X, wanda ke ci gaba da yamutsa hazo.














