ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shettima Ya Ce Zuba Jari A Ɓangaren  Ilimi Ba Caca Ba Ce

by Idris Aliyu Daudawa and Sulaiman
8 months ago
Shettima

Mataimakin Shugaban kasa Kashim Shettima ya bayyana cewa babu wani zuba jari a bangaren ilimi da za’a daue shi tamkar wata Caca ce aka yi, domin kuwa shi ya tsaya kai da fata cewa bangaren na ilimi yake jagora kan samu gaba ta kasance gwanin ban sha’awa ga Nijeriya da ‘yan Nijeriya.

Bugu da kari ya yi wa ilimi kallon wani babban ginshiki ne na ci gaba, ci gaban tattali arziki da kuma ba kowa dama domin shi/ita a samu tsayawa da kafafu.

  • Sojojin Sama Sun Yi Lugudan Wuta, Sun Lalata Sansanonin Ƴan Ta’adda A Borno
  • DSS Ta Kama Jami’inta Kan Zargin Cin Zarafin Yarinya ‘Yar Shekara 16

Ya yi wannan jawabin ne lokacin da aka yi bukukuwan yaye dalibai na hadin gwiwa na Jami’ar Kashim Ibrahim a Jihar Borno , inda aka yaye jimillar dalibai 2,294 wadanda suka kammala karatunsu a shekarun karau  uku wato – 2022/2023, 2023/2024  da kuma 2024/2025, mataimakin Shugaban kasar ya yi kira da wadanda suka kammala karatunsu na Jami’a su dauki kansu a matsayin wani wuri ne daga wurinsu inda za’a koyi  tafiyar da gaskiya,rikon amana, son juna, da kuma inganci.

ADVERTISEMENT

Ya kara jaddada cewa halayen da za su rika nunawa lokacin mu’amalarsu da al’umma ta haka ne, za’a iya gane cewa ashe dukkan wadancan halaye daga can ne kuka kara koyonsu domin makarantu ba karatu kadai suke koyawa ba,da akwai  anu’oin tarbiyyar bayan tarniyyar da suka samu daga gida.

“Babu wata harkar zuba jari a ilimi da za ayi a dauke ta cewa matsayinta daya da harkar Caca. Wani tsari ne aka yi domin a gaba a sau dama ta kasancewa a yanayi wanda kowa zai ce gara da aka yi hakan.

LABARAI MASU NASABA

An Tantance Masu Neman Aikin Koyarwa 500 A Jigawa

JAMB Ta Ƙara Wa’adin Amincewar Guraben Karatu Zuwa 30 Satumba

Ya kara bayanin cewa ‘’Duk inda lamarin ilimi ya kai mutum ai yana tafiya da sunan ne, don haka za ku rika tafiya ce a sunan Jami’ar  Kashim Ibrahim saboda ai can ne aka kara wayar maku da kai kan yadda rayuwa take da kuma yadda ya dace a tafiyar da ita,  bayan irin tarbiyar da kuka samu a gida, ba wai ilimin zalla bane da akwai dabi’un da ake koyo daga makaranta. Hakanan ma kada ku bari a yaudare ku har a kai ga jan ra’ayinku har ku kai ga yin abinda zai zubar da mutuncunku, zuri’arku, da kuma makarantar da kuka yi kamar yadda ya bayyana,”.

Shettima ya bayyana cewa Jihar Borno da gwamnatin ta, ta san a bubuwan da za su iya faruwa a gaba sanadiyar yi wa harkar ilimi rikon sakainar kashi, tun da har, aka yi hakuri da shekarun da aka bata saboda lamarin rashin tsaro sanadiyar fadace- fadacen ta’addanci.

“Borno ta san irin yanayin da ta shiga a shekarun da aka bata da yadda suka kasance ba a maganar ilimi sai ta zaman lafiya ake nema.Amma suk da hakan al’ummar suka yi hakuri, al’ummar suka zabi ci gaba jajircewa duk da yake akwai abubuwan da aka rasa masu muhimmanci kamar yadda bayanin nasa ya nuna.

Ya ce wadanda suka kammala karatun jami’a sune wani babban ginshiki ne na ita Jami’armataimakin Shuban kasar ya tunatar da su cewa, Tarihi fa ya maida su suna da wata babbar gudunmawa da za su bada gaba tare da su.

“Ku ne kuka fara kammala karatu a wannan Jami’a.Tarihi zai yi bayani kan wannan Jami’ai ne ta yadda kuka tafiyar da rayuwarku.”

Ya jinjina wa wadanda nauyin koyarwa da Shugabancin Jami’ar ya rataya kansu, har da mutumin da ya fara jagorantar ta a matsayin mataimakin Shugban jami’ari, jagororinta na yanzu, Malamai, ma’aikata, saboda abinda ya kira da sunan “babban ginshikin da suka yi amfani da shi wajen fara lamarin koyarwa a tsakiyar Arewa maso gabas.”

Shettima
Idris Aliyu Daudawa
+ posts Bio
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Tarihin Rayuwar Galadiman Kano Alhaji Tijjani Hashim (2)
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Kyamar Baƙi: An Sake Kwaso Ƴan Nijeriya 83 Daga Afirka Ta Kudu
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Kamfanin Simintin Dangote Ya Tallafa Wa Manoma 60 Da Kayan Aiki A Edo
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Tsohon Shugaban Ƙasa Jonathan Ya Ƙaddamar Da Ayyukan Raya Ƙasa 18 A Jihar Bauchi
Shettima
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

MASU ALAKA

Shettima
Ilimi

An Tantance Masu Neman Aikin Koyarwa 500 A Jigawa

August 31, 2026
Shettima
Ilimi

JAMB Ta Ƙara Wa’adin Amincewar Guraben Karatu Zuwa 30 Satumba

August 29, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Ilimi

Kano Ta Yi Zarra Wajen Kashe Kuɗi Don Raya Ilimi A Yammacin Afirka

July 11, 2026
Next Post
AFCON 2025: Nijeriya Ta Kai Matakin Kusa Da Na Ƙarshe Bayan Doke Algeria

AFCON 2025: Nijeriya Ta Kai Matakin Kusa Da Na Ƙarshe Bayan Doke Algeria

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.