ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, July 7, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shirye-shiryen Fara Kofin Afirka: Abin Da Ya Kamata Ku Sani

by Abba Ibrahim Wada
7 months ago
Kofin

Kamar yadda hukumar ƙwallon ƙafa ta nahiyar Afirka ta tsara, a ranar Lahadi 21 ga watan Disamba ne za a fara fafatawa a gasar cin kofin ƙwallon ƙafa ta nahiyar Afirka ta 2025, wadda ita ce karo na 35 da aka buga a tarihin gasar, kuma ita ce babbar gasa a Afirka.

Gasar Cin Kofin Afirka ta 2025 na tattare da ƙalubale, fiye da waɗanda aka yi daga shekara 10 zuwa 15 baya, inda tawaga 24 za su kece-raini a filayen wasa tara cikin biranen ƙasar Moroko shida.

  • Kasashe Nawa Ne Suka Samu Tikitin Zuwa Gasar Cin Kofin Duniya?
  • Yadda Aka Haɗa Jadawalin Rukuni Na Gasar Kofin Duniya 2026

A baya ana buga gasar tsakanin Yuni zuwa Yuli, amma a gasar bana za a yi ne cikin watan Disamba, saboda wasannin gasar kofin duniya da za a yi a 2026 daga 15 ga watan Yuni zuwa 13 ga watan Yuli da za a gudanar a Amurka da Canada da kuma Meɗico.

ADVERTISEMENT

CAF ta tsara cewa za a yi gasar ne daga Disamban 2025 zuwa Janairun 2026. Kuma wannan shi ne a karon farko da za a yi gasar cin kofin Afirka a lokacin da ake bikin Kirsimeti da na sabuwar shekara.

Sai dai akwai wasu muhimman bayanai da suka kamata a sani game da gasar, wanda ya kamata masoya ƙwallon ƙafa musamman a nahiyar Afirka su sani da kuma tarihin abubuwa da dama a gasar.

LABARAI MASU NASABA

FIFA Ta Tsallake Iyakarta Dangane Da Batun Dakatarwar Balogun – UEFA

FIFA Ta Dakatar Da Aiwatar Da Hukuncin Hana Folarin Balogun Buga Wasa

Ƙasar Masar ta lashe gasar ne a shekarun 1957 da 1959 da 1986 da 1998 da 2006 da 2008 da 2010. Haka kuma ta zo a ta biyu sau uku a shekarun 19621 da 2017 da kuma 2021, sai ta zo ta uku a shekarun 1963 da 1971 da 1974, sannan ta zo ta huɗu sau uku shi ma a shekarun 1976 da 1980 da 1984.

Ƙasar da ta fi tarin nasarori, wato yawan zinare da azurfa da tagulla idan aka haɗa baki ɗaya, wato ƙasar da ta fi zuwa wasannin na ƙarshe ko kusa da ƙarshe ita ce ƙasar Nijeriya, inda jimilla ta samu nasarar lashe ko dai kofin ko ta zo ta biyu ko ta uku sau 16.

Ta lashe gasar sau uku a shekarun 1980 da 1994 da 2013, sannan ta zo ta biyu sau biyar a shekarun 1984 da 1988 da 1990 da 2000 da 2023, sai kuma ta zo ta uku sau takwas a shekarun 1976 da 1978 da 1992 da 2002 da 2004 da 2006 da 2010 da kuma shekarar 2019.

Sannan a ɓangaren wasanni da tara maki, ƙasar Masar ce kan gaba, inda ta halarci gasar sau 26, sannan a ciki ta buga wasa 111. A cikin wasannin, ta samu nasara a guda 60, ta yi canjaras sau 24, sannan aka doke ta a wasa guda 27. Idan aka yi amfani da tsarin maki, wato maki uku a nasara, da maki ɗaya a canjaras sai rashin maki a rashin nasara, ƙasar Masar tana da jimillar maki 204. Sannan ƙasar da ke biye mata ita ce Nijeriya, wacce ta je gasar sau 20,

inda ta buga wasa 104, ta samu nasara a wasa 57, ta yi canjaras a wasa guda 24, sannan aka doke ta a wasa 23, inda jimilla ta tara maki 195.

Haka kuma a ɓangaren tarihin lashe gasar a jere, ƙasar Masar ɗin ce dai ta fi samun nasara domin ƙasar ta lashe gasar sau uku a jere a shekarar 2006 da 2008 da 2010.

Ƙasashe guda uku ne suka samu nasarar lashe gasar a karon farko da suka fara zuwa gasar: Masar ta lashe gasar a shekarar 1957 da ta fara buga gasar, sai Ghana da ta lashe gasar a shekarar 1963 da ta fara buga gasar, sai kuma ƙasar Afirka ta Kudu da ta lashe gasar a shekarar 1996 da ta fara buga gasar.

A ɓangaren zura ƙwallaye a raga kuma ɗan wasan ƙasar Kamaru Samuel Eto’o ne ya fi zura ƙwallaye a tarihin gasar, inda ya zura ƙwallo 18 a wasa 29 da ya buga a gasar guda shida da ya buga.

Tsohon ɗan wasan na Barcelona da Inter Milan ya halarci gasar a shekarun 2000 da 2002 da 2004 da 2006 da 2008 da 2010. Wanda yake biye masa shi ne Laurent Pokou na ƙasar Iɓory Coast, wanda ya ci ƙwallo 14 a wasa 12 da ya buga a gasar. Sai kuma ɗan ƙwallon Nijeriya Rashidi Yekini wanda ya zura ƙwallo 13 a wasa 20.

Sannan wanda ya fara cin ƙwallo a gasar shi ne ɗan wasan ƙasar Masar, Raafat Attia, wanda ya fara zura ƙwallo a gasar ta farko. A wasan farko na gasar ta farko, wanda aka buga a ranar 10 ga watan Fabrairun shekarar 1957 wanda aka fafata tsakanin Masar da Sudan, shi ne ya zura ƙwallo ta farko a wasan wanda Masar ta samu nasara da ci 2-1.

Har ila yau, yan wasan da suka fi taka wasanni a gasar su ne Rigobert Song na ƙasar Kamaru, wanda ya wakilci ƙasar tsakanin shekarar 1998 zuwa shekarar 2010, da kuma André Ayew na ƙasar Ghana wanda ya wakilci ƙasar Ghana tsakanin shekarar 2008 zuwa shekarar 2023. Kuma kowanne daga cikinsu ya buga wasanni 36 ne a gasar.

Kofin
Abba Ibrahim Wada
Website |  + postsBio
  • Abba Ibrahim Wada
    Lampard Zai Ci Gaba Da Zama A Coventry City
  • Abba Ibrahim Wada
    LeBron James Zai Bar Los Angeles Lakers 
  • Abba Ibrahim Wada
    An Raba Jadawalin Gasar Premier Ta Ingila Ta Kakar Wasan 2026/2027
  • Abba Ibrahim Wada
    Daga 1930 Zuwa 2026: Yadda Aka Buga Wasa Na Dubu Ɗaya A Gasar Kofin Duniya

MASU ALAKA

FIFA Ta Tsallake Iyakarta Dangane Da Batun Dakatarwar Balogun – UEFA
Wasanni

FIFA Ta Tsallake Iyakarta Dangane Da Batun Dakatarwar Balogun – UEFA

July 6, 2026
FIFA Ta Dakatar Da Aiwatar Da Hukuncin Hana Folarin Balogun Buga Wasa
Wasanni

FIFA Ta Dakatar Da Aiwatar Da Hukuncin Hana Folarin Balogun Buga Wasa

July 5, 2026
Lampard Zai Ci Gaba Da Zama A Coventry City
Wasanni

Lampard Zai Ci Gaba Da Zama A Coventry City

July 5, 2026
Next Post
Shugaban Ghana: Sin Ta Kasance Abokiyar Afirka Ta Gaske A Ko Da Yaushe

Shugaban Ghana: Sin Ta Kasance Abokiyar Afirka Ta Gaske A Ko Da Yaushe

LABARAI MASU NASABA

Kasuwa Ce Ke Saita Tsarin Cinikayyar Sin Da EU In Ji Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin

Kasuwa Ce Ke Saita Tsarin Cinikayyar Sin Da EU In Ji Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin

July 6, 2026
Dukkan Kabilun Kasar Sin Na Zaman Tsintsiya Madaurinki Daya

Dukkan Kabilun Kasar Sin Na Zaman Tsintsiya Madaurinki Daya

July 6, 2026
Mutane 15 Sun Mutu A Hatsarin Mota A Jihar Kwara

Mutane 15 Sun Mutu A Hatsarin Mota A Jihar Kwara

July 6, 2026
Gwamnatin Sin Ta Fara Aika Zagayen Farko Na Kayakin Agajin Gaggawa Ga Venezuela

Gwamnatin Sin Ta Fara Aika Zagayen Farko Na Kayakin Agajin Gaggawa Ga Venezuela

July 6, 2026
FIFA Ta Tsallake Iyakarta Dangane Da Batun Dakatarwar Balogun – UEFA

FIFA Ta Tsallake Iyakarta Dangane Da Batun Dakatarwar Balogun – UEFA

July 6, 2026
Shugabannin Sin Da Madagascar Sun Yi Musayar Sakon Taya Murnar Cika Shekaru 20 Da Kulla Alakar Diflomasiyya Tsakaninsu

Shugabannin Sin Da Madagascar Sun Yi Musayar Sakon Taya Murnar Cika Shekaru 20 Da Kulla Alakar Diflomasiyya Tsakaninsu

July 6, 2026
Rashin Tsaro: Kisa Ne Ya Fi Cancanta Ga ‘Yan Ta’adda Ba Gyaran Hali Ba – Ɗan Majalisa Gagdi

Rashin Tsaro: Kisa Ne Ya Fi Cancanta Ga ‘Yan Ta’adda Ba Gyaran Hali Ba – Ɗan Majalisa Gagdi

July 6, 2026
Mu Leka Yadda Kasar Sin Ke Raya Hakkin Dan Adam Daga Taron Gefe Na UNHRC

Mu Leka Yadda Kasar Sin Ke Raya Hakkin Dan Adam Daga Taron Gefe Na UNHRC

July 6, 2026
ADC Ta Rushe Shugabannin Jam’iyyar A Kano, Ta Naɗa Kwamitin Riƙo

ADC Ta Rushe Shugabannin Jam’iyyar A Kano, Ta Naɗa Kwamitin Riƙo

July 6, 2026
Rundunar Sojin Ruwan Sin Ta Yi Gwajin Makami Mai Linzami Ta Amfani Da Jirgin Ruwa Mai Nutso

Rundunar Sojin Ruwan Sin Ta Yi Gwajin Makami Mai Linzami Ta Amfani Da Jirgin Ruwa Mai Nutso

July 6, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.