ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, July 15, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sirrin Kasancewar Mu Shekara Fiye Da 40 A Matsayin Mata Da Miji”

by Yusuf Shuaibu
3 months ago
Miji

Ya kamata aure ya kasance rayuwa na farin ciki, amma wani lokacin rashin jituwa da rigingimu na faruwa a tsakanin ma’aurata. IBRAHIM OBANSA, Lokoja da ATTAH ANTHONY, Jalingo da ACHOR ABIMAJE, Jos, sun rubuta labarin yadda wasu ma’aurata da suka kasance tare tsawon fiye da shekaru 40.

A cikin wannan zamani da aure ke faɗawa cikin ruɗani, ma’aurata dama sun samu nasarar gudanar da rayuwar aure cikin lumana fiye da shekaru 40. Ta cikin mawuyacin lokaci da saukin rayuwa da lokuta masu kyau da mara kyau, sun tsaya tare. Wasu sun samu lokutan baƙin ciki da rashin jituwa, duk da haka suna son juna tare da yin haƙuri da juriya wanda ya sa suka kasance a tare.

  • Gwamna Dauda Lawal: Tsayayyen Namiji A Siyasar Yankin Arewa Maso Yamma
  • Ƙarin Farashin Man Fetur: TUC Ta Shawarci Gwamnati Ta Tallafawa Matatun Mai Na Cikin Gida

A yayin da yake zantawa da Jaridar LEADERSHIP, wani dattijo a Jihar Kogi, Mista Emmanuel Bolagi Boro, ya danganta nasarar aurensa na shekaru 40 da haƙuri da kuma juriya. Ya jaddada cewa waɗannan halaye suna da muhimmanci ga kowace alaƙa don ta bunƙasa.

ADVERTISEMENT

Boro, wanda ya fito daga ƙauyen Ogori da ke ƙaramar hukumar Ogori-Magongo ta Jihar Kogi, ya bayyana cewa yana da dogon sanayya da matarsa, Miss Mary Yomi Aturu, wanda a yanzu ta koma Miss Mary Yomi Boro, kasancewar ya san danginta tun kafin su yi aure.

“Mun kasance mun fito daga ƙauye ɗaya. Na san ta tun da daɗewa kuma na san danginta. Duk da haka, na tattauna da ita a yayin bikin girbin shekara-shekara na cocinsu a shekarar 1975, wanda na halarta a matsayin ɗalibi na makarantar sakandare,” ya tuna.

LABARAI MASU NASABA

Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

Kotu Ta Tsare Shugaban Makaranta Da Malami Kan Zargin Lalata Da Ɗaliba Mai Shekara 6 A Gombe

A cewarsa, dangantakarsu ta kasance shekaru 13 kafin aure, ta hanyar ɗabi’u masu ƙarfi da kuma komawa ga Allah. “A zamaninmu, abin ƙyama ne a yi jima’i kafin aure. Akwai tsananin tsoron Allah a zuciyarmu a cikin waɗannan shekaru,” in ji shi.

Ya jaddada cewa babu wata hanyar sihiri da za a samu aure mai nasara, yana mai lura cewa fahimtar juna da jure ƙalubale suna da matukar muhimmanci.

“Abin da ya fi muhimmanci shi ne, ma’aurata su fahimci juna. Idan suka yi hakan kuma a shirye suke su jure, auren zai yi nasara. Dole ne su kuma koyi yafiya. Zai kasance akwai laifuka daga ɓangarorin biyu, amma haƙuri da yafiya zai taimaka wajen ɗorewar aure,” ya ƙara da cewa.

Mista da Misis Boro sun yi aure suna da shekaru 32 da 28, kuma Allah albarkace su da yara uku, mata biyu da namiji ɗaya, waɗanda duk sun yi aure kuma suna zaune tare da iyalansu.

“Allah ya albarkace mu da yara uku, kuma a yau dukkansu sun yi aure sun cikin farin ciki. Mu ma yanzu mun tsofa, kuma har yanzu muna godiya ga Allah,” in ji shi.

Mista Boro ya kasance tsohon darektan yaɗa labarai ne a ma’aikatar gwamnatin Jihar Kogi, yayin da matarsa ta kasance tsohuwar shugabar makarantar St Mary da ke Lakwaja.

Kazalika, wata uwargida mai shekaru 82 a Jihar Taraba, Mama Ruth Sule Pantuɓo, ta danganta tsawon rai da kwanciyar hankali na aurenta mai shekaru sama da 60 tare da Sir George Sule Pantuɓo mai shekaru 87, ikon Allah da haƙuri da fahimtar juna.

Da yake magana kan aurenta, wadda aka ɗaura tun a shekarar 1966, Mama Pantuɓo ta ce babu wani tsari na musamman na samun zaman lafiya a aure face tsoron Allah.

Ta bayyana yadda ta haɗu da mijinta, ta ce dangantakarsu ta fara ne da kasancewa abokai kafin ta koma soyayya, “kuma babu wani asiri sai dai Allah ya shiga cikin lamarin aurenmu. Allah ya kasancewa mai aminci. Muna ƙoƙarin biyayya gare shi, kuma ya taimaka mana ta hanyoyi da dama. Ya zo wurin aikina, muka zama abokai, sannan daga baya muka yi aure,” ta tuna.

Yayin da take tunani ƙalubalen aure a tsawon shekaru, tsohuwar ta ce duk da cewa kowanne aure yana da ƙalubale da farin ciki, amm fahimtar abokin zama da yadda za a warware matsala suna da muhimmanci, kamar yadda ta ce, auren na da ƙalubale, amma ya danganta da wanda ka aura da yadda kake magance matsaloli. A gare mu, mun kasance tare kuma muka ci gaba da zama tare. Ba mu taɓa rabuwa ko da na rana guda ba.”

Ta bayyana mijinta a matsayin mutum mai aiki tuƙuru kuma mai ladabi wanda ya kasance mai sadaukarwa ga aikinsa da iyalinsa, duk da cewa a wasu lokutan, yana son yi hira da abokansa. Ta ƙara da cewa sakamakon jure bambance-bambancen da ke tsakaninsu da warware matsaloli ta hanyar tattaunawa da addu’a ya taimaka musu wajen shawo kan matsalolin aurensu.

A cewarta, akwai abubuwa da yake yi da ba ta so, sannan ita ma akwai abubuwa da take yi da shi ma ba ya so, amma suna tattauna a tsakaninsu da yi addu’a, wanda shi ne silar samun nasarar aurensu.

Ta nanata cewa aure yana nufin mutane biyu masu yafiya suna zaune ƙarƙashin rufin gida guda ɗaya.

Mama Pantuɓo ta kuma jaddada muhimmancin kimar iyali, tana bayyana cewa kula da yara da kiyaye haƙƙoƙin gida ya ba da gudummawa sosai ga dangantakarsu mai ɗorewa. Ta shawarci matasan ma’aurata su yi haƙuri da juna da kuma kula da tarbiyyar ‘yaƴansu yadda ya kamata. Ta ƙara da cewa matasa ma’aurata a yau suna buƙatar haƙuri, da yawa suna samun rikici kan abubuwa marasa muhimmanci kuma ba su da haƙuri, wanda kuma da zarar kun yarda da juna dole ne ku kula da gidanku domin ku zauna tare.

Matar ta kuma yi kira ga ma’aurata su kiyaye kyakkyawar dangantaka da iyalansu, tana gargaɗin cewa rashin warware matsaloli da ƴan’uwa ta aure na iya kawo rashin daidaito a cikin aure, kuma da zarar akwai soyayya da girmamawa tsakanin miji da mata, da iyalansu, za a samu zaman lafiya.

Mama Pantuɓo ta ce bayan shekaru da yawa tare da mijinta, ta dubi baya tare da godiya ga Allah. Ta jaddada cewa duk da ƙalubalen da ba za a iya kaucewa su ba, jajircewarsu ga juna ta sa iyalinsu sun kasance cikin haɗin kai.

Wani mutum mai shekara 80 a Jihar Filato, Jacob Ajayi, ya shaida wa LEADERSHIP cewa haƙuri da jimrewa da amincewa da juna su ne abubuwan da suke taimaka masa wajen samun aure mai cike da nasara.

Yayin da yake magana kan sirrin ɗorewar haɗin gwiwa a cikin aure, ya yi iƙirarin cewa samun nasarar aure ta ta’allaƙa ne wajen ɗaukar juriya ga namiji ko mace, sai dai ya nuna damuwarsa kan yayin aure a yau, inda masoya masu shirin aure ba sa gudanar da bincike kan wanda za su aura kafin su shiga daga ciki.

“Suna karkatar da hankalinsu ga abubuwa na wucin gadi kamar kyau da ilimi da mahaifinta, ko mahaifinsa mai dukiya. Waɗannan ba za su tabbatar da samun aure mai nasara ba,” ya bayyana.

Ya ba da shawarar ga ma’aurata masu niyya yin aure a ko da yaushe su binciki abokin da za su aura, kamar danginsa kafin su shiga aure. Ya ƙara da cewa ya kasance ka san komi gami da shi ko game da ita.

Pa Ajayi ya kuma bayyana cewa akwai lokacin da shekaru ko kyawu za su shuɗe, amma hali zai ci gaba da kasancewa cikakke.

“Ba za ka iya sa ran samun aure mai nasara ba idan ka fito daga dangin da ake sakin aure da masu shan giya da mutane masu zinace-zinace, wanda matansu ba su zama wuri guda ba,” in ji shi.

Ya shawarci ma’aurata su kasance masu haƙuri da girmama juna da kuma jin tsoron Allah, domin wannan yana cikin littafi Mai Tsarki, kuma ka da su bari abubuwa marasa ɗorewa su ja hankalinsu, kamar motoci masu kyau da gidaje masu kyau da dukiyar ban mamaki. “Me zai faru idan kyau ya shuɗe, ba motoci, ba gidaje da kuma dukiya sun tafi? Za ku rabu ne?” ya tambaya.

Ajayi ya ce ya yi aure a shekarar 1970 kuma zuwa watan Yuni, aurensa zai cika shekaru 56.

“Na haɗu da matata ta hanyar wani abokina lokacin da take zaune tare da babban yayanta, wanda ya kasance ma’aikacin tsohuwar hukumar kasuwancin jihohin Arewa (NSMB),” ya tuna.

A cewarsa, kafin wannan lokaci, yana soyayya da mata da yawa, wasu daga cikinsu malamai ne, wasu kuma ma’aikatan jinya ne, amma ya ɗauki lokaci kafin ya je ya auri matarsa, Esther, saboda ba ta cikin irin mutanen da suka yi fice, wato tana daga cikin mutane masu kamun kai kuma ba ta rayuwar ƙarya da yawancin mata ke yi a wannan zamani.

 

Miji
Yusuf Shuaibu
+ postsBio
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Amurka Ta Yi Alƙawarin Sa Ido Sosai A Zaɓen Nijeriya Na 2027
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Sautin Muryar Da Aka Fallasa Kan El-Rufai Ya Haifar Da Zazzafar Muhawara
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Ci-ma-zaunen Ƴan Siyasa Ne Ke Tunanin Yin Maguɗi A Zaɓen 2027 – Makarfi
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    An Samu Ruɗani Kan Rashin Bayyana Jerin Ƴan Takarar Jam’iyyun Siyasa Na Zaɓen 2027

MASU ALAKA

Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu
Labarai

Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

July 14, 2026
Katsina: Kotu Ta Yanke Wa Hauwa’u Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Taimaka Wa ’Yan Bindiga
Manyan Labarai

Kotu Ta Tsare Shugaban Makaranta Da Malami Kan Zargin Lalata Da Ɗaliba Mai Shekara 6 A Gombe

July 14, 2026
Nijeriya da Masar Sun Ƙulla Haɗin Gwiwa Domin Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi
Labarai

Nijeriya da Masar Sun Ƙulla Haɗin Gwiwa Domin Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi

July 14, 2026
Next Post
Tsarin Siyasar Kano: Ya Kamata Gwamna Abba Ya Yunkura…

APC Ta Gabatar Da Mutane Uku Domin Cike Muƙamin Kujerar Mataimakin Gwamnan Kano

LABARAI MASU NASABA

Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

July 14, 2026
Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

July 14, 2026
An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

July 14, 2026
Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

July 14, 2026
Sin Ta Tsara Bunkasa Darajar Cinikayyar Kayayyaki Zuwa Yuan Tiriliyan 60 Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

Sin Ta Tsara Bunkasa Darajar Cinikayyar Kayayyaki Zuwa Yuan Tiriliyan 60 Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

July 14, 2026
Katsina: Kotu Ta Yanke Wa Hauwa’u Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Taimaka Wa ’Yan Bindiga

Kotu Ta Tsare Shugaban Makaranta Da Malami Kan Zargin Lalata Da Ɗaliba Mai Shekara 6 A Gombe

July 14, 2026
An Bankado Muguwar Aniyar Japan Ta Haifar Da Tashin Hankali A Tekun Kudancin Sin

An Bankado Muguwar Aniyar Japan Ta Haifar Da Tashin Hankali A Tekun Kudancin Sin

July 14, 2026
Layin Dogo Tsakanin Tanzaniya Da Zambiya Ya Zama Shaidar Abota Tsakanin Sin Da Afirka

Layin Dogo Tsakanin Tanzaniya Da Zambiya Ya Zama Shaidar Abota Tsakanin Sin Da Afirka

July 14, 2026
Nijeriya da Masar Sun Ƙulla Haɗin Gwiwa Domin Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi

Nijeriya da Masar Sun Ƙulla Haɗin Gwiwa Domin Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi

July 14, 2026
CMG Ya Gudanar Da Babban Taron Masu Kirkirar Manyan Shirye-Shirye Da Fina-Finai

CMG Ya Gudanar Da Babban Taron Masu Kirkirar Manyan Shirye-Shirye Da Fina-Finai

July 14, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.