ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sojoji Sun Nemi Ƴan Sokoto Su Miƙa Ragowar Ɓaraguzan Bam Ɗin Amurka

by Abubakar Sulaiman
8 months ago

Bayan harin saman da rundunar Sojin Amurka ta kai a ranar Kirsimeti a Arewacin Nijeriya, hukumomin soja a Jihar Sokoto sun yi kira ga mazauna jihar da su mika duk wani ragowar bam ko wani ɓaraguzan fashe wa da suka samu daga wuraren harin. Wannan mataki na nufin kare haɗɗari da tabbatar da tsaron jama’a.

Harin saman, wanda aka kai daga daren 25 ga Disamba zuwa safiyar 26 ga Disamba, 2025, ya mayar da hankali ne kan sansanonin ƴan ta’adda masu alaƙa da ƙungiyar ISWAP a dajin Bauni. Harin, wanda rundunar Amurka da Nijeriya suka haɗa kai wajen kai wa, ya yi amfani da makaman da ake jagoranta ta na’urar sarrafawa (GPS) da jiragen sama marasa matuƙi don lalata cibiyoyin ƴan ta’adda a yankin Sahel.

  • Amurka Ta Yi Iƙirarin Kama Shugaban Ƙasar Venezuela
  • Amurka Ta Bayyana Dalilin Janye Jakadanta Daga Nijeriya Da Wasu Kasashe 29

A wani bayani da shalƙwatar tsaron Nijeriya ta fitar, an bayyana cewa harin ya dogara ne kan bayanan sirri kuma an sami nasarar kashe barazanar da akai nufi, ba tare da jikkata fararen hula ba. Ana ci gaba da tantance sakamakon harin, kuma ana sa ran ƙarin bayani daga hukumomi bayan kammala bincike.

ADVERTISEMENT

Duk da tabbacin cewa babu farar hula da suka rasa rayuka, ragowar kayan fashe wa da abubuwan da ba a tantance ba da suka faɗo kusa da yankin sun haifar da damuwa kan tsaro. Sojojin sun yi kira ga mazauna yankin da su hanzarta miƙa duk wani ragowar bam ko kayan da suka ɗauka ga hukumomin tsaro don kauce wa fashewar haɗari da kuma taimakawa wajen cikakken bincike na ɓarnar da aka yi.

Haka kuma, an shawarci mazauna da su kai rahoton wuraren da ake zargin akwai kayan fashewa. Gwamnatin Jihar Sokoto ta tabbatar da harin kuma ta bayyana cewa aikin haɗin gwuiwa da rundunar Amurka wani ɓangare ne na ci gaba da ƙoƙarin kare rayuka da dukiyoyi daga barazanar ƴan ta’adda.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Iyalin El-Rufai Sun Bai Ministan Tsaro Wa’adin Kwana 7 Kan Zargin Rikicin Kudancin Kaduna
  • Abubakar Sulaiman
    Atiku Ya Zargi Gwamnatin Tarayya Da Cin Bashi Kamar Mashayin Da Kuɗi Ya Ƙarewa
  • Abubakar Sulaiman
    Boko Haram Ta Kai Hari Adamawa, Ana Fargabar Mutuwar Mutane 11
  • Abubakar Sulaiman
    Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Sokoto, Sun Kashe Mutane 7, Sun Yi Garkuwa Da 12

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
Next Post
Dalilin Ɗage Sauya Sheƙar Gwamna Abba Kabir Yusuf Zuwa 12 Ga Janairu

Dalilin Ɗage Sauya Sheƙar Gwamna Abba Kabir Yusuf Zuwa 12 Ga Janairu

LABARAI MASU NASABA

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.