ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Talauci Ba Hujjar Aikata Muggan Laifukka Ba Ne 

by Ibrahim Bala
5 months ago

Assalamu Alaikum Wa Rahmatullahi Ta’ala Wa Barakatuhu. Jama’a barkanmu da kasancewa tare da wannan fili mai albarka, wanda muke zaƙulo batutuwan da suke ci wa al’umma tuwo a ƙwarya.

A wannan gaɓar zan ja hankalin matasa da kuma iyaye musamman maza. An shiga wani yanayi da sai dai mu yi addu’a, mu riƙa ƙoƙari muna daina amfani da kalmar taluaci muna yin ɓarna, wannan ba daidai ba ne.

Babu yadda za a yi talauci ya saka saɓon Allah, wannan ba daidai ba ne ba. Dole ne mu ja hankali mu kiyaye, samari ne lungu da saƙo gasu nan an koya musu sana’ar sayar da kayan maye, wannan kuma sai dai mu ce innalillahi wa inna ilaihirraji’un.

ADVERTISEMENT
  • Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027
  • Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

A gefe guda ɓarna tana ta wanzuwa har da matan aure ake kai wa ajiyar ƙwayoyi, idan an je siya sai a riƙa shiga gidajen ana karɓa ana siya, kuma ana fakewa da cewa wai talauci ne yake janyo wa, wannan ba daidai ba ne ba.

Allah ya baka rai, ya baka lafiya, to, ya baka damar da za ka tsaya ka nemi abin da za ka dafa ka rufawa kanka asiri. Ka shayar da iyalinka halal ba haram ba. Sannan kai matashi ka tsaya ka nemi halaliyarka.

LABARAI MASU NASABA

Buni Ya Nuna Kwarewarsa Ta Diflomasiyya

Shin Tinubu Ya Tabbatar Da Sauke Ribadu Daga Mukaminsa?

Wannan shi ya sa kodayaushe a rayuwa muke shiga cikin wani yanayi, kamar ka haifi ‘ya’ya a rasa yadda za a yi da su, ba dan komai ba saboda neman da aka yi ba a tsaya an yi shi na tsakani ga Allah ba, an bi ta ɓarauniyar hanya wajen tara dukiyar da aka mallaki iyalan.

Ina ganin ya kamata mu tsaya mu yi wa kanmu faɗa halin da ƙasar take ciki, kullum cewa muke yi shugabanni kaza! Shugabanni kaza!! bayan mu, ba ma duba mu me muke yi? to, dole mu zauna idan kai magidanci ne kai ka tsaya ka san ma ‘yaƴanka wacce irin sana’a suke yi da suke samun kuɗi. Saurayin ‘yar ka me yake yi ma, da har yake zuwa gurinta ya siya mata abu kaza?.

Kar idonmu ya rufe mu riƙa ganin wane yana samun kuɗi, sana’a ce wacce take kawo kuɗi. Mu kalli halaliyar, kaɗan me albarka ya fi me yawa mara albarka. Mu tsaya mu mayar da hankali saboda hadisi ne ingantacce cewar, kai hani da aljihunka, ko da hannunka, ko da bakinka.

Indai waɗannan abubuwa da za su kawo tangarɗa ko cutuwa ga al’ummar musulmi to, ya kamata saboda sayar da kwayoyi ya kan iya sakawa samari su aikata abubuwan da ba acikin tunaninsu da hankalinsu suke ba. Lokaci ne da ya kamata mu yarda cewar, daga gidajenmu za mu fara ɗaukar matakin gyara, sannan mu fita waje.

Amma a gidanka ka bar baya da ƙura, baka tsaya ka tsananta ka yi faɗa ga ‘yaƴanka ba, kai dai kawai ana shigo maka da abinci, ‘yaƴanka sukan iya ɗaukar nauyinka na kuɗin makaranta ko suturar da za ka saka sai ka ja baki ka yi shuru.

Dole ne wannan abun mu hankalta da shi, wallahi wannan abun ya fara shiga lunguna da saƙo. Wasu ɓata gari suna zuwa suna rabawa yara kwayoyi suna siyarwa suna samun riba me yawa. Dole ne mu magance wannan matsalar, kafin a ci mu da yaƙi.

Wassalamu Alaikum.

Ibrahim Bala
+ postsBio
  • Ibrahim Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/ibrahim-bala/
    Hanyoyin Da Za A Bi A Rage Yawan Zawarawa
  • Ibrahim Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/ibrahim-bala/
    A Duba Halin Da Masu Buƙata Ta Musamman Ke Ciki
  • Ibrahim Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/ibrahim-bala/
    Matsalar Ƙwacen Waya: Ina Mafita?
  • Ibrahim Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/ibrahim-bala/
    Falalar Goman Farko Na Zul-hajji 

MASU ALAKA

Zanga-Zanga: Gwamnatin Yobe Ta Bayar Da Umarnin Rufe Makarantun Jihar
Bakon Marubuci

Buni Ya Nuna Kwarewarsa Ta Diflomasiyya

August 28, 2026
An Kusa Ceto Ɗaliban Neja Da Aka Sace – Ribadu
Bakon Marubuci

Shin Tinubu Ya Tabbatar Da Sauke Ribadu Daga Mukaminsa?

August 28, 2026
Kwairanga Ya Kafa Tarihi A Shugabancin Hukumar Kula Da Kasuwar Hannun Jari Ta Nijeriya
Bakon Marubuci

Kwairanga Ya Kafa Tarihi A Shugabancin Hukumar Kula Da Kasuwar Hannun Jari Ta Nijeriya

July 24, 2026
Next Post
Hukumar Shari’a Ta Kano Ta Hukunta Alƙalai Da Ma’aikata Kan Laifukan Rashin Ɗa’a

Hukumar Shari’a Ta Kano Ta Hukunta Alƙalai Da Ma’aikata Kan Laifukan Rashin Ɗa'a

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.