ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 4, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tarihin Kwalejin Barewa (1)

by Idris Aliyu Daudawa
1 month ago
Tarihin

Tarihin kwalejin Barewa wani babban lamari ne wanda ya sha yawan sauye-sauye ko canje- canje, labarin dai ya fara ne daga Katsina lokacin da aka kafa kwalejin horarwa ta Katsina.

Shawarar lamarin kafa ita kwalejin abin ya faru ne daga bangaren mai rikon mukamin Darekatn ilimi na Lardunan Arewa, Mista. F.M.Urling Smith da aka fi sani da (Malam Smith) wanda shi an san shi yana da bukatar samun karuwar ingantaccen ilimi ta hanyar samar da Malaman makaranta da suka samu horarwar.Tunda akwai bukatar ilimi a Lardunan Arewacin Nijeriya dole abin ya tafi tare da“yan asalin wurin”,don haka ne shi Urling Smith ya fahimci cewar akwai bukatar ingancin Malaman Afirka ko ma’aikata.Kamar yadda Urling Smith ya ke hasashe na ya dace a samu aji domin koyar da Malaman makaranta kamar yadda ya  dace.Saboda kuwa ya nuna matukar damuwa akan yadda tsarin ilimin ya ke yi tafiyar Kura,zai kuma ci gaba da,ayi hakan, matukar ba a samu Malamai na nahiyar Afirka ba wadanda za a iya basu horon da ya dace fiye da wadanda ake da su.Manufar ita ce bukatar samar da abubuwan koyarwa na kafa ta musamman ta koyarwa, da za ta taimakawa sauran Jami’an mulkin mallaka kamar su, Hans Bischer (Dan Hausa) wanda yake shi Darektan ilimi ne  tun farko ne ya ki bada goyon baya na wata makaranta a tsakiya da za a ce ta fi samun ci gaba fiye da sauran.Duk da yake dai,Lord Frederick Lugard Gwamna mai kare ko kula da Arewacin Nijeriya ya sa al’amarin a cikin abubuwan da, ya ke son yi a shekarar 1917, sai dai kash! aka ki aminewa da shawarar ta shi saboda rashin  Kudi da kuma da kuma ma’aikata.

Lamarin bai samu wani tagomashi ba sai zuwan wani sabon Gwamna,da ake kira Sir Hugh Clifford a lokacin shi ne maganar ta samu amincewa. Babbar manufar abin ita ce ilimi a Lardunan Arewa ba wai ana bukatar a horar da ‘yan Arewar ba ne domin su yi gogaiya da sauran ‘yan Afirka ba ne wajen neman ayyukan gwamnati ba,maimakon hakan shi sashen ilimi zai kasance wani abu ne da za ayi amfani da shi wajen yin aiki wajen  tafiyar da ayyukan hukumomin na Larduna.Hakan ya sa, Kwalejin horarwa ya kasance abinda aka amince da shi wajen tsarin ilimi wanda ya fi muhimmanci.

ADVERTISEMENT

Abin dogaron mu

Bayan da aka samu‘yar turjiya dangane da wurin da yafi dacewa a kafa kwalejin, sai aka zabi Katsina a matsayin wurin da yafi dacewa fiye da garuruwan da suke kan hanyar jirgin kasa kamar Kaduna, wadda ta kasance hedikwatar mulki ce ta Lardunan Arewa.Akwai abubuwan da suka sa aka zabi Katsina.Da farko dai, Katsina  an  dade ana yi mata kallo wani muhimmin wuri ne na koyon karatu abinda yasa, akwai nisa da yawa daga hanyoyin Jirgin kasa ga kuma“ga kuma wasu abubuwa na Allah ya yi mata wata mu’ujiza da Turawan mulkin mallakar Ingila suke tsoro”.Sauran abubuwan da suka sa aka zabi Katsina sun hada da akwai maganar abinda ya shafi kudi. Domin shi baya bukatar abinda zai, sa a kashe kudade masu yawa wajen gina ginin dindindin.Sarin Katsina na wancan lokacin Muhammadu Dikko (1906-1944),ya bada wani wuri da aka gina shi da kasa wato wurin da daliban za su zauna domin yin karatu. Sai Clifford ya amince da wurin da ba za a biya kudade masu yawa ba ya amince aka bar Kwalejin a Katsina.Bugu da kari kuma Sarkin Katsina,Muhammadu Dikko ya nuna jajaircewar shi da kuma hakurin bada taimako ga lamarin ilimin da gwamnati take son yi.

LABARAI MASU NASABA

Hukumar NCCE Ta Yi Tsare-tsaren Bunƙasa Horar Da Malamai

Abubuwan Da Ya Kamata Magidanci Ya Sani Bayan Matarsa Ta Haihu

Duk da yake dai ofishin mulkin mallakar basu nuna amincewarsu ba kan lamarin da ake bukatar su zuba jari na Fam dubu ashirin 20,000, (£20,000) da ake bukata na gina dakunan karatu na dindindin,ba tare da wani bata lokaci ba sai aka fara bada fam dubu hudu 4,000 (£4,000) saboda gine ginen da za a fara  da kuma fam dari 500 (£500 ) saboda sayen kaya. Zuwa karshen shekarar 1921, sai aka bude makarantar da dalibai wadanda matasa ne domin kuwa ta wani bangaren da iyalansu suna tafiya a kasa ko kuma suna zuwa kan Dawaki daga dukkan Lardunan Arewa.

A jawabin da ya gabatar Clifford lokacin da aka bude Kwalejin horarwa ta Katsina ranar 5 ga Maris 1922 inda ya ce:

Dole ne matasan da za su samu horo a wannan Kwaleji, wadanda daga baya kuma su ne za su koyar a Lardin Katsina da kuma sauran Masarautu, ya dace su maida hankalinsu lokacin da ake koya masu.Su maida hankalinsu wajen abinda ake koya masu saboda wani babban aiki ne wajen koyar da wasu.

Kada kuma su yi watsi da lura da lamurran addininsu, ko kuma su manta da al’adunsu, da na kasarsu, kada kuma su yi watsi da al’adar yi ma nag aba ladabi da biyayya musamman ma ga iyayensu, ga kuma dukkan masu mukamai na mulki ga kuma tsofaffi.

Hakanan ba kawai abubuwan darussan da aka koya maku daga littattafai, har ma da dabi’u nagari, halaye masu kyau, da kuma ganin girma, domin kuwa abubuwan da aka koya a littafi ‘yan kadan ne idan aka ce za a kwatanta su da sauran.

Kowane matashi wanda ya sami horo anan shi ma a gaba za a kira shidomin ya horar da mutane da yawa. Ya kamata kowa ya tuna da cewar “Babu wani mutumin da za a ga girman sa sosai sai wanda ya koya wato samu horo kwarai, shi ma za a yi ma shi ladabi”

Lokacin da aka fara yin karatun, makarantar ta maida hankalinta ne kawai kan ‘ya’yan masu hali, wato kamar Sarakuna da kuma wadanda suke kusa da su an fada masu su tura’ya’yansu makaranta. Wasu daga cikinsu sun yi yayin da wasu kuma suyka ki amincewa su tura ‘ya’yan nasu.

Fara zamanin ‘yan kasa

A wancan lokacin, dukkan malaman Turawan Ingila ne.Sai dai kuma duk da hakan, mutane biyu ‘yan Afirka suna da mukami a makarantar. Malam Nagwamatse yana koyar da Larabci shi ne kuma matsayin mai kula da wurin kwanan dalibai. Bugu da kari kuma yana kulawa da wuraren da dalibai suke kwana da kuma da’arsu. A lokacin ko tsakiyar shekarar ne, Malam Bello Kagara ya samu aiki a makarantar kamar yadda Nagwamatse yake yana koyar da Larabci da karatun Alkur’ani.

Tsakanin shekarar 1931-1937 babu wani daga cikin wadanda suka yi Shugabancin Kwalejin yake da farin jinni a Kwalejin kamar  Mista. G.A. J.Bieneman yake da shi. Bieneman shi ne Shugaban Kwalejin na farko  shi ne kuma ya dora ta kan tafarkin Eton a Kwalejin  horon Malamai ta Katsin. Sauran wadanda suka yi Shugabancin Kwalejin sun hada da, Trebor S.Phillips (1931-1934), William E. Nicholson (1934-1935)da kuma Eric Mort (1935-1946) suna daga cikin manyan jami’ai wadanda suka fara aiki a sashen kafin yakin duniya na daya.

Kwaleji mai zurfi ta Katsina: A shekarar 1929, an kara martabar makarantar daga Kwalejin horar da Malaman makaranta zuwa Kwalejin ilimi mai zurfi ta Katsina.An fara amfani ne da Kwalejin ilimi mai zurfi ta Katsina ranar 1 ga Afrilu 1931 hakan ne ya nuna irin tunanin da Gwamnatin Birtaniyya take yi dangane da Kwalejin. Masu kishin  kan irin yadda Arewa ta ke kokarin ci gaba kan tafarkin ilimi ya sa an fara tunanin a maida Kwalejin zuwa ko kamar irin yadda Kudancin Nijeriya suka ci gaba kan tafarkin na ilimin na su wato nagartar da yake da ita. Bayan da Urling Smith ya yi ritaya, Eric R.J. Hussey ya gaje shi a matsayin matsayin sabon Darektan ilimi.

Bayan da aka ba Hussey aiki  hakan ya sa aka fara yin wata sabuwar shawara ko kuma sabon tunani akan Kwalejin da kuma matsayin ilimi a Arewacin Nijeriya. Hussey ya bada shawarar yin gyara kan tafarkin ilimi a Lardunan Arewacin Nijeriya, wanda an tsara abin ne domin a gyara shi tsarin ilimi na Lardunan Arewacin Nijeriya ya zama daidai da na Lardunan Kudancin Nijeriya. Ita babbar Kwaleji ko Kwalejin ilimi mai zurfi ita ce za ta maye gurbin Kwalejin horarwa ta Katsina.

Babbar Kwaleji ko Kwalejin ilimi mai zurfi za ta samar da ilimin shekara biyu na gaba  daya, sai kuma horarwa ta musamman da za a bada fifiko ko maida hankali kan mukaman gwamnati. Babbar manufar ita ce a samu Malaman makaranta, mataimaka kan ayyukan da suka shafi Asibitoci,da kuma Akawu. “Makarantar Midil da ita ce ake yi kafin makarantun Firamare  za ta samar da karatu na shekara shida na karatu kan bangarorin ilimi, domin hakan ne ya sa Kwalejin ilimi mai zurfi ta Arewa ta kara bunkasa yadda ta ke, da zummar lamarin ya kasance tamkar yadda shi tafarkin ilimi ya ke a ko tsara yadda zai kasance a Yaba kusa da Legas.

Tarihin
Idris Aliyu Daudawa
+ postsBio
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Hukumar NCCE Ta Yi Tsare-tsaren Bunƙasa Horar Da Malamai
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Abubuwan Da Ya Kamata Magidanci Ya Sani Bayan Matarsa Ta Haihu
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Tarihin Shugaban Makaranta Na Farko A Arewa Hedimasta (2)
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Yadda Gidajen Abinci Ke Wasa Da Rayuwar Al’umma Ta Amfani Da Ruɓaɓɓen Tumatir

MASU ALAKA

Hukumar NCCE Ta Yi Tsare-tsaren Bunƙasa Horar Da Malamai
Ilimi

Hukumar NCCE Ta Yi Tsare-tsaren Bunƙasa Horar Da Malamai

May 31, 2026
Abubuwan Da Ya Kamata Magidanci Ya Sani Bayan Matarsa Ta Haihu
Ilimi

Abubuwan Da Ya Kamata Magidanci Ya Sani Bayan Matarsa Ta Haihu

May 30, 2026
Layya Babbar Ibada A Musulunci Na 1
Bakon Marubuci

Layya Babbar Ibada A Musulunci Na 1

May 27, 2026
Next Post
EFCC Ta Kama Ɗan Kamaru Kan Zargin Damfarar Naira Biliyan 1.5

EFCC Ta Kama Ɗan Kamaru Kan Zargin Damfarar Naira Biliyan 1.5

Discussion about this post

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

June 3, 2026
Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

June 3, 2026
Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

June 3, 2026
Majalisa Ta Nemi Tinubu Ya Canza Dabarun Yaƙi Da Ta’addanci Don Kawo Ƙarshen Kashe-kashe

’Yan Majalisar Tarayya 3 Sun Fice Daga APC Zuwa ADC da PRP

June 3, 2026
An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos

An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos

June 3, 2026
Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

June 3, 2026
Gwamnatin Beijing Ta Amince Da Kafa Cibiyar Kirkire-Kirkiren Fasahar Lissafi Mai Nasaba Da Sararin Samaniya

Gwamnatin Beijing Ta Amince Da Kafa Cibiyar Kirkire-Kirkiren Fasahar Lissafi Mai Nasaba Da Sararin Samaniya

June 3, 2026
Za A Fara Buga Gasar Kofin Sarkin Gombe Bayan Masu Ruwa Da Tsaki Sun Cimma Matsaya

Za A Fara Buga Gasar Kofin Sarkin Gombe Bayan Masu Ruwa Da Tsaki Sun Cimma Matsaya

June 3, 2026
Hada Kai Da ’Yan Awaren Yankin Taiwan Ba Zai Haifar Da Ɗa Mai Ido Ba

Hada Kai Da ’Yan Awaren Yankin Taiwan Ba Zai Haifar Da Ɗa Mai Ido Ba

June 3, 2026
An Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Na Magadan Gari Na 2026 A Beijing

An Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Na Magadan Gari Na 2026 A Beijing

June 3, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.