ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 4, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tarihin Kwalejin Barewa (2)

by Idris Aliyu Daudawa
1 month ago
Barewa

Shirin Sauyawa Kwalejin Barewa Wuri Zuwa Zariya

Daga cikin shirye- shiryen da Hussey ya ke yi,na samarwa Kwalejin wani wuri an fara tunanin yin hakan ne. Shi ya fi son a samarwa Kwaleji wani sabon wuri a Zariya domin a fadada Kwalejin horarwa ta.Katsina, kamar yadda ya ke tunani, ba ta dace ba. Ita sabuwar babbar Kwalejin da ake son kafawa, tun da Zariya  tana da sassan da suka shafi asibiti, aikin gona, ayyukan al’umma da kuma jirgin kasa a can suke, ana iya samun sauki na tafiyar da ayyukan  idan akwai hadin kai.Shirin da Hussey ya ke yi ma  Zariya na samun babbar Kwaleji yana bukatar a samar da kudade da suka kai zuwa fam dubu sittin da uku (£53,000) a shekaru uku da suka fara daga 1931 -32.Sai dai saboda irin halin rashin kudin da ake fama da shi a lokacin, kudin shigar da Nijeriya ke samu ya yi kasa sosai abin bai kai fam miliyan biyar ( £5,000,000).Duk da kokarn Hussey, sai da gwamnati ta tsaida maganar gina sabuwar babbar kwalejin zuwa wani lokaci.

Kwalejin Kaduna: A watan Oktoba 1935, an samu amincewar kafa sabbin kwalejojin a Lardunan Arewa daga ofishin mulkin mallakar Turawan Ingila. A farkon shekarar 1934 ne,Hussey ya samu damar samun amincewar Laftanan Gwamna cewa duk wata maganar da ake ta kafa makarantar  Sakandare ko ta gaba da a Lardunan Arewacin Nijeriya abin ba za a samu nasarar shi ba, ba tare da wata sabuwar kwaleji  ba, duk da yake kuwa gwamnatin Arewa ta yi alkawarin za su bada fam dubu ashirin da uku (£23,000 ) daga hukumar mulkin Sarakuna saboda ayi aikin, an ci gaba da koma bayan tattalin arziki Gwamna   Cameron ya amince da  kashe kudin.Sai da kuma duk da hakan Hussey, ya yi kokari inda ya samu amincewar a kashe  fam dubu goma sha tara (£19,000,) za a samu  fam dubu goma sha uku (£13,000) daga hukumar Sarakuna  saboda a lokacin sune kamar yadda karamar hukuma take yanzu a Nijeriya,ya yin da fam dubu shida  (£6,000) daga  alfarmar Alfred Jones. Sashen ilimi ya yi shirin kwalejin da ake shirin yi za ta kasance dukkan manhajar koyarwa daya take da ta Katsina.Sai dai kuma, tunanin da Hussey ya yi na karuwar wadanda suka kammala Kwalejin Yaba ya hadu da fushin Sarakuna, Jami’an Turawan mulkin mallaka da kuma sashen ilimi.Cameron ya maida martini inda ya ce sabuwar kwaleji  za ta iya kasancewa daya da Kwalejin Yaba zuwa wani lokaci nan gaba kadan idan har aka hada da hakuri za ta goge irin kallon da ake yi ma makarantun Kudu.Amma wakilin Turawan mulkin mallaka da ke lura da Kano  cewa ya yi Kaduna ta fi kasancewa wurin da ya dace a kafa Kwalejin wato ita ce za ta maye makwafin ko gurbin ta Zariya wadda Hussey ya zaba. Kaduna, kamar yadda ake tsammanin za ta rage kishin da ake yi. Kaduna tana gaban cibiyar koyon aikin gona ta Samaru, kamar dai yadda sassan Asibiti da na ayyukan suke. Hussey bai da wata ta cewa. In banda ya samu amincewar, Cameron, an dai bada shawarar cewar Kaduna ba za ta kasance da tsada ba, saboda kuwa tuni take da wutar lantarki, ruwan famfo da kuma isassun gidaje da ma’aiktan Turawan Ingila.

ADVERTISEMENT

An amince da sunan Barewa

Bayan da aka amince da suna Kwalejin Kaduna, sai makarantar ta koma Arewacin hedikwatar Lardunan Arewa a shekarar 1938.A shekarar 1942, sai aka canza matakan da ake daukar daliban Kwalejin,aka fara daukar kananan yara wadanda basu taba samun wani ilimi ba.Nagartar ilimin Malaman makarantar da suke koyarwa lamarin ya kasance ya yi dai dai da irin sha’awar da sashen  ilimi ya ke da shin a ci gaba da nema ko kuma binciken samun masu nagarta, wato abinda ya yi kama da na Turawa ko bai kai irin na su ba.Wannan ya nuna sashen ilimi ya na samar da kwararrun Malamai, saboda yadda  ake koyin da tsarin ilimi na Turawan mulkin mallaka. A watan Satumba 1940, sai Sojojin Ingila suka bukaci filin da aka gina Kwalejin.Sai kuma aka maida kwalejin zuwa gine- ginen gidajen Railway karshen kudancin Kaduna, a wani wuri da ake kira da suna Kaduna Junction.

LABARAI MASU NASABA

Hukumar NCCE Ta Yi Tsare-tsaren Bunƙasa Horar Da Malamai

Abubuwan Da Ya Kamata Magidanci Ya Sani Bayan Matarsa Ta Haihu

Shi sabon wurin an raba shi da cikin gari fiye da tsohon wurin da aka samar na ainihi. Mort wanda a lokacin shi ne Shugaban makarantar bai gamsu da cewar shi sabon wurin ne zai kasance wurin makarantar na dindindin ba. Mort ya ce dalibai wadanda suka lamarin aikin gona ya fi dacewa da su, ba za su san  a maganar gaskiya yadda lamarin rayuwar birni ta ke ba.Ya yi tunanin cewa Arewacin Kaduna wurin bai dace da  makarantar Sakandare ba saboda yadda gine- ginen suke  bayan yakin duniya na biyu, Mort ya samu wata amincewa a maida Kwalejin zuwa  Zariya.

Makarantar Sakandaren Gwamnati/ Kwalejin Gwamnati/ Barewa Kwaleji Zariya:

A shekarar 1949, Kwalejin ta bar wurin da take a Kaduna Junction zuwa Zariya. Duk wadansu ayyuka na taimakawa Kwalejin Mort ya yi ana ma iya gane hakan.Ya ci gaba da tafiyar da Kwalejin cewa ta ‘’yan Arewa ce” a dukkan al’ada da kuma irin kayan gargajiya, koda kuwa dalibin ya kasance ko da halayen shi ba na Musulmi ba ne.Lokacin da Kwalejin ya koma Zariya ana kiran shi da suna, Makarantar Sakandaren gwamnati ta Zariya,daga baya kuma ta koma Kwalejin gwamnati ta Zariya.Sai shekarar 1972 lokacin da ake bikin cika shekara 50 da kafa Kwalejin ne aka canza sunan shi zuwa Barewa Kwaleji. Sunan Barewa an samo shi ne daga Bajen kwalejin wanda Barewa ce ta ke gudu.Barewa ana kiranta Gazelle a cikin harshen Hausa.

Irin yadda wadanda suka yi makarantar suka bayar da gudunmawarsu ta ga ci gaban kasa kwarai da gaske.

Barewa Kwaleji a matsayin makarantar da ta ke ta kowane dan asalin sashen Arewa ne ta yi matukar shahara ta bangarori daban- daban.Abu na farko shi ne ta tara matasa tun daga Sakkwato wadda ta ke daga kusan karshen Arewa maso yamma; sai kuma daga karshen sashen Arewa ta tsakiya kamar Adamawa da Borno; hakanan ma kamar Benuwe da Kabba  daga bangaren  na Midi Bel sun yi karatu tare. Da akwai kuma manyan Shugabannin Arewa a lokacin da Nijeriya ta samu ‘yancin kai,sun yi karatu tare da kuma yin wasa tare a makaranta lokacin shekarunsu na karatu a cikin Kwalejin ta Barewa. Wadannan manyan mutanen na Arewan da suka yi makarantar sun hada da Sir Kashim Ibrahim (B73) daga Borno (tsohon gwamna na Arewacin Nijeriya) Sir Ahmadu Bello (B87) daga Sakkwato (tsohon Firimiyan sashen Arewa.) Sir Abubakar Tafawa Balewa (B145) daga Bauchi (Firayim Ministan Nijeriya na farko);Alhaji Aliyu Makaman Bida (B8) daga Neja (tsohon  ministan kudi) Alhaji Isa Kaita (B111) daga Katsina (tsohon ministan ilimi) da Alhaji Yahaya Madawaki (B54)daga Ilorin. (tsohon ministan ayyuka).Akwai ma mai alfarma Sultan (B2612) Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad 111 da Sarakuna da dai sauransu.

Wani abin burgewa dangane da su daliban Barewa Kwaleji shi ne saboda sunan ita makarantar da suka yi, ba kuma tare da yin la’akari da wani abu ba sun dauki kowane daga cikinsu a matsayin ‘yan’uwa ko abokai, kome nisan daga wuraren da suka zo.

Wani abin sha’awa, shi ne abin burgewa na Barewa Kwalejin shi ne yadda wadanda suka kammala makaranta suna tunawa da kuma taimakawa a lamurran da suka shafi zaman takewa, al’adun gargajiya, tattalin arziki, ilimi, da kuma siyasar da ta shafi kasa. Tsofaffin daliban Barewa Kwalej sun maida hankalinsu wajen yi wa kasa hidima. Domin kuwa maganar gaskiya, sahun farko na Shugabannin siyasar Arewa, harkokin mulki, ilimi, harkar tsaro sannu a hankalin daga Barewa Kwalej su ke. Mashahuran daliban da suka yi Kwalejin Barewa sun taka muhimmiyar rawa da kuma bada gudunmawa a fannoni daban- daban na taron tsarin mulki da aka yi a Ingila wanda shi ne ya bada haske danagane da samun ‘yancin Nijeriya a shekara ta 1960.

Ita Kwalejin Barewa ko Barewa Kwaleji tana alfahari da kan ta, saboda yawan mutanen da suka zama wani abu a yau Nijeriya ta fannoni daban- daban, mutane ko mazaje wadanda suka yi ma kasa aiki, musamman a lokuttan da take da bukatar ayi mata hakan..

Bayan da ta hanyar ta ne aka samu su mashahuran mutanen ‘yan Nijeriya,har ila yau Barewa Kwalej ta samar da Gwamnonin Jiha, Sakatarorin gwamnatoci da kuma Shugabannin ma’aikata, Shugabannin kotun koli ta kasa, Shugabannin kotun daukaka kara, Ministoci, mataimakan Shugabannin  jami’oi, manyan Sakatarori na ma’aikatu na gwamnatin tarayya, da Shugabannin  hukumomi da sassa- sassa masu yawa .

Don haka shi yasa wannan ba wani abin mamaki ba ne da ake cewa Barewa Kwalej tamkar ma wata ma’ajiya ce ta Shugabannin Nijeriya a bangarorin rayuwa daban- daban.

An Samo Mukalar Ne Daga Shafin BOBA

Barewa
Idris Aliyu Daudawa
+ postsBio
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Hukumar NCCE Ta Yi Tsare-tsaren Bunƙasa Horar Da Malamai
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Abubuwan Da Ya Kamata Magidanci Ya Sani Bayan Matarsa Ta Haihu
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Tarihin Shugaban Makaranta Na Farko A Arewa Hedimasta (2)
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Yadda Gidajen Abinci Ke Wasa Da Rayuwar Al’umma Ta Amfani Da Ruɓaɓɓen Tumatir

MASU ALAKA

Hukumar NCCE Ta Yi Tsare-tsaren Bunƙasa Horar Da Malamai
Ilimi

Hukumar NCCE Ta Yi Tsare-tsaren Bunƙasa Horar Da Malamai

May 31, 2026
Abubuwan Da Ya Kamata Magidanci Ya Sani Bayan Matarsa Ta Haihu
Ilimi

Abubuwan Da Ya Kamata Magidanci Ya Sani Bayan Matarsa Ta Haihu

May 30, 2026
Layya Babbar Ibada A Musulunci Na 1
Bakon Marubuci

Layya Babbar Ibada A Musulunci Na 1

May 27, 2026
Next Post
Rikicin ADC: Kwankwaso Zai Jagoranci Tawagar Sauya Sheƙa Zuwa NDC

Rikicin ADC: Kwankwaso Zai Jagoranci Tawagar Sauya Sheƙa Zuwa NDC

Discussion about this post

LABARAI MASU NASABA

Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili

Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili

June 4, 2026
Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

June 3, 2026
Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

June 3, 2026
Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

June 3, 2026
Majalisa Ta Nemi Tinubu Ya Canza Dabarun Yaƙi Da Ta’addanci Don Kawo Ƙarshen Kashe-kashe

’Yan Majalisar Tarayya 3 Sun Fice Daga APC Zuwa ADC da PRP

June 3, 2026
An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos

An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos

June 3, 2026
Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

June 3, 2026
Gwamnatin Beijing Ta Amince Da Kafa Cibiyar Kirkire-Kirkiren Fasahar Lissafi Mai Nasaba Da Sararin Samaniya

Gwamnatin Beijing Ta Amince Da Kafa Cibiyar Kirkire-Kirkiren Fasahar Lissafi Mai Nasaba Da Sararin Samaniya

June 3, 2026
Za A Fara Buga Gasar Kofin Sarkin Gombe Bayan Masu Ruwa Da Tsaki Sun Cimma Matsaya

Za A Fara Buga Gasar Kofin Sarkin Gombe Bayan Masu Ruwa Da Tsaki Sun Cimma Matsaya

June 3, 2026
Hada Kai Da ’Yan Awaren Yankin Taiwan Ba Zai Haifar Da Ɗa Mai Ido Ba

Hada Kai Da ’Yan Awaren Yankin Taiwan Ba Zai Haifar Da Ɗa Mai Ido Ba

June 3, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.