ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 4, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tinubu Ya Gudanar Da Ayyukan Raya Kasa Da Dama A Arewa A 2025 —Abdul’aziz Abdul’aziz

by Leadership Hausa
5 months ago

A tattaunawar da Editanmu Bello Hamza ya yi da mai ba shugaban kasa shawara na musamman a bangaren kafafen yada labarai, Malam Abdul’azizs Abdul’azizs ya bayyana irin ayyukan ci gaban kasa da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gudanar a yankin arewacin kasar nan a cikin shekarar 2025. Ya kuma yi alkawarin cewa gwamanti ta shirya gudanar da wasu ayyukan ci gaba a cikin wannan shekara mai kamawa. Ga dai yadda hirar tamu ta kasance:

 

A wadannan shekaru, mu dauki shekarar da muke shirin bankwana da ita. Me za a iya haskawa al’ummar Nijeriya na irin abin da suka ribata karkashin ita gwamnatin?

ADVERTISEMENT

Kamar yadda ka ce yanzu muna bankwana da watan 12 na shekara ta 2025. Akwai abubuwa da yawa da suka faru idan za mu yi waiwayen baya. Zan iya cewa kamar an ratso daji ne, an ratso wani surkuki wanda yake mawuyaci wana za a iya cewa kamar ma ba a iya fita ba, kuma cikin ikon Allah da dagiya da dagewar shugabanni Allah ya taimake mu yanzu mun doshi haske gadan-gadan kan cewa mun shiga cikin haske din.

Duk wanda ya tuna yadda ya aka fara wannan gwamnatin, an san cewa akwai lokacin da za a iya cewa an shiga rudani, an shiga koke-koke, an shiga hali na rashin tabbas. Saboda bayan zuwan wannan gwamnatin, shi shugaban asa Bola Tinubu ya zo da wani irin tunani da ba a saba gani ba. Mene ne tunanin da ba a saba gani ba? Shi ne na farko dan siyasa kullum burinsa ya yi farin jini, a yi masa tafi, a yi masa sowa duk inda ya bi. Kuma mene ne yake kawo tafi da shewa? Shi ne ka yi abin da mutane ko da ba mai kyau ba ne za su ji dadinsa.

LABARAI MASU NASABA

Har Yanzu Ana Yin Allah-wadai Da Cin Amanar Da Aka Yi Wa Kwankwaso – Hon. MB Aliyu

Dalilin Da Ya Sa PDP Ke Cikin Rikici, Za Ta Dawo Da Karfin Ta —Saraki

Misali an zo an tarar da boda a rufe, ka zo ka ce an bude boda, ko da wannan abin ba shi da kyau. Ko kuma a’a an tarar da man fetur a kudi kaza, kamar yadda wasu gwamnatoci a baya suka yi, ka zo ka ce a’a ai kai ka rage don ‘yan kasa su ji dadi.

To duk irin wadannan abubuwan wasu abubuwa ne wadanda za su iya jawo maka farin jini na takaitaccen lokaci ko kuma na lokacin da kake kan mulki. Amma kuma ba abubuwa bane da lallai za su taimaki kasa.

To shi shugaba Bola Tinubu ya zo da wani tunani cewa zaman karya da ake yi na shekara da shekaru, zaman tunanin cewa komai lafiya ne, bayan tubali na ginin kasar yana rarukewa, ana samun gara na cinye wannan harsashin ginin, ya ce ba zai yiwu ba. Duk da za a iya samun rashin jindadi na dan wani lokaci, kamar yadda mawakin siyasa Rarara yake cewa; likitan kwarai ba ya shakkar ya yi gaskiya, saboda ba za a ka yi gyara ba na irin mikin ciwon da Nijeriya take da shi a lokacin da aka zo, sai in ka rufe ido ka jure ihun majinyaci. A nan zan iya cewa kamar ‘yan Nijeriya domin kawo gyaran da zai taimaki mutane. Shiyasa aka shiga cikin wadannan hali musamman a farkon wannan gwamnatin.

Amma alhamdulillahi daga shekarar bara an soma ganin sauyi. Misali; sai dai ya zama na cewa kusan kowa ba ya son kasuwanci da ‘yan Nijeriya, saboda matsalar farashin kudin mu ma ba a san nawa ba ne. ‘Yan kasuwar mu suna jin tsoron shigo da kaya. Akwai mutane da na sani da yawa suka daina shigo da kaya daga waje saboda rashin tabbas. Za ka je kasuwa ka yi siyayya sai an yi kira. Ni din nan na je kasuwa zan yi siyayya sai an kira an ji farashin dala kafin a gaya maka kudin a naira. Saboda ‘yan kasuwa sun shiga halin rashin tabbas.

An kai lokacin da kayan abinci da sauran kayayyakin masarufi suka yi tsada suka yi tashin gwauron zabi, amma idan ka duba yau Alhamdulillah wadannan abubuwan mu wuce su. Dala yanzu ba ka da haufi za ka iya siyo kaya a kowanne lokaci. A nan kasashen waje za su shigo da kudin su su iya fitar da su.

Saboda abubuwan da suka faru a mulkin baya, mun zo mun tarar da masu kamfanunnukan jiragen sama kadai na kasashen waje suna bin Nijeriya dala biliyan kusan goma sha wani abu, na kudin da suka siyar da tikiti a naira amma mun kasa biyan kudin a dala. Sai da wannan gwamnatin ta zo aka rika rage wannan kudin. Har sai da ya sa wadansu jirage suka daina zuwa Nijeriya. Saboda wannan matsalar cewa kudin su ya makale da yawa a nan ba za su ci gaba da rakiyar asara ba. Suna yin abin da yake ba shi da tabbas ba. Kamar yadda na ce yanzu mun wuce wannan mataki.

Farashin kayayyakin abinci yanzu daidai misali kowa dan Nijeriya zai iya zuwa kasuwa ya siya abinci saboda farashin ya sauka. Buhun shinkafa ‘yar gwamnati sai da ta kai kusan dubu casa’in ma a wadansu wurare, amma yanzu Alhamdulillah ta dawo kusan dubu sittin. To duka wadannan wasu abubuwa ne wadanda wahala ce mun sani an yi mursisi, amma abu ne da zai amfani mutane a karshe.

Kuma na sani kila kaima za ka yi tambayar kamar yadda mutane suke cewa; ina kudin suke kaza da kaza? Na tabbata duk mai yin tafiye-tafiye wanda ba zaman gida kawai yake yi ba ba inda yake zuwa sai kasuwa, inda kana tafiya gari, gari, to kana ganin yadda ake amfani da kudaden da ake samu wajen yin ayyukan ababen more rayuwa; ayyukan da za su taimaki ‘yan Nijeriya. Ayyukan da za su bunkasa mana tattalin arziki.

Misali idan ka dauki hanyar da ake yi daga Sakkwato, sabuwar hanya ake yi fil daji aka bude ta aka share, ake yin hanya wacce ta tashi daga Sakkwato za ta je har Legas; hanya ce wacce za ta taimaki kauyuka daruruwa; domin hanya ce mai tsawon kilomita dubu daya. Kuma akwai garuruwa da kauyuka da yawa da suke wannan hanya. Wanda yanzu haka ana yin aikin hanyar nan gadan-gadan, wani bangaren ta ma yanzu an fara hawa ta wurin Sakkwato da Jihar Kebbi.

Idan ka tafi yanzu, hanyar Zariya, zuwa Gusau zuwa Sakkwato, ana nan ana ta yin aikin wannan hanyar. Yanzu nan idan ka taso daga hanyar da ta tafi daga Abuja zuwa Kano, ita ma ana nan an yi mata dibar karen mahaukaciya ko ta ko’ina ana yin aikin. Domin shugaban asa ya bayar da umurnin cewa lallai yana so ya ga an gama wannan hanyar.

Idan ka zo ka shiga bangaren Jigawa, zuwa Daura, ko daga Kano zuwa Katsina, ko daga Kaduna zuwa Kano, za ka ga ana ta hanyar layin dogo, layin jirgin kasa. Wanda zai hada wadannan yankuna. Jirgin kasan da zai tashi daga Kaduna, ya je Kano, daga Kano ya tafi Katsina, daga nan zai je Jigawa, daga Jigawa zai je Daura, zai bi ta Kazaure ya je Daura, ya hade ya shiga Maradi, jamhuriyyar Nijer. Wannan aikin ana yinsa gadan-gadan, ba karamin abu ba ne na ci gaba da ake yi.

Aikin gas: daya daga cikin abin shi ne duniya ta canza daga amfani da fetur da sauran mai masu gurbata yanayi, kuma gas din nan muna da shi a Nijeriya, kuma ya fi sauki. Shiyasa ma tunda aka cire tallafin man fetur gwamnati ta mayar da hankali a kan bunkasa amfani da iskar gas, to yanzu aikin iskar gas din nan, bututun gas da ya taso daga Ajaokuta, zuwa Abuja, Kaduna, Kano, yana nan ana gab da kammalawa. Insha Allah cikin shekarar da za mu shiga za a kammala shi. Yawanci wadannan ayyukan da nake lissafa maka, cikin shekarar da za mu shiga duka za a kammala su.

Wasu ‘already’ ma an kammala, yanzu idan daga Abuja idan ka tashi za ka Makurdi, hanya ce mai kyau, ana nan ana yin hanyar Jos zuwa Bauchi; duk wadannan ayyuka ne da ake yi sakamakon karin samun kudin shiga da gwamnati ta yi. A wancan lokacin da gwamnatin nan ta zo fa, a tuna fa harma an daina bai wa Nijeriya bashi, saboda matsalolin mu na tattalin arziki.

Yanzun ana daukar ma’aikata, jami’an tsaro kawai, za a dauki dubu hamsin da bakwai, na baya-bayan nan ke nan, akwai kuma kusan dubu talatin na hukumomin shige da fice, ‘cibil defense’ da na ‘prison’ wanda za a dauka. Har sun fara aikin daukar tun watannin baya.

 

Su jami’an tsaron nan dubu hamsin da doriya; wani rukuni ne?

Akwai ‘yan sanda, akwai sojoji wadanda suke dubu hamsin da bakwai din nan. To kuma ga dubu talatin wadancan. Sannan banda sauran ma’aikatu da kullum ake daukar aiki. Yanzu kullum idan ka bude jarida za ka ga wannan jami’a na daukar ma’aikata, wannan makaranata tana neman ma’aikata. Wannan hukuma tana neman ma’aikata, ana ta daukar aiki a wurare daban-daban.

Duk wadannan daukar aikin kuma, saboda akwai kudin ne. Albashi ma a daidai lokacin da gwamnatin nan ta zo, akwai jihohin da ana bin su bashin albashi. Gwamnatin tarayya da kan ta da kyar take biyan albashi. Amma yanzu alhamdulillahi jihohi da yawa idan ka je ana ayyuka. Kudin nan gwamnonin nan musamman na mu na jihohin arewa, ba su suke samar da kudin ba, kudi ne da yake zuwa daga gwamnatin tarayya, kuma saboda kudin sun karu ne; shiyasa har.

 

Wato da bazarsa yake rawa ke nan ba a bin da yake samu daga jiharsa ba?

Kwarai kuwa. Gwamnoni da bazar abin da ake samu daga gwamnatin tarayya suke rawa. Kuma da bazar shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu saboda ya bube musu hanyoyin karuwar samun kudi. Jiha da a da take samun misali miliyan 25, yanzu za ka ga tana samin miliyan 40 da wani abu. Wata har 50 da wani abu. Kudinsu ya nunku. Su da kansu su kan fito su fadi hakan.

Za mu ci gaba a mako mai zuwa

Leadership Hausa
Website |  + postsBio
  • Leadership Hausa
    Yadda Arsenal Ta Lashe Gasar Firimiya Bayan Shekara 22
  • Leadership Hausa
    Bukatar Kawo Karshen Akidar Kyamar Baki A Kasar Afirka Ta Kudu
  • Leadership Hausa
    Ikirarin Cewa Sanata Abdul’aziz Yari Abubakar, Marafan Sokoto, Nauyi Ne Ga Jihar Zamfara Da Jam’iyyar APC Ba Ta Da Tushe
  • Leadership Hausa
    Nazarin Kisan Gillar Da ‘Yan Kato Da Gora Suka Yi Wa Wani Matashi A Biniwe

MASU ALAKA

Har Yanzu Ana Yin Allah-wadai Da Cin Amanar Da Aka Yi Wa Kwankwaso – Hon. MB Aliyu
Tattaunawa

Har Yanzu Ana Yin Allah-wadai Da Cin Amanar Da Aka Yi Wa Kwankwaso – Hon. MB Aliyu

April 10, 2026
 Saraki Zai Jagoranci Kwamitin Gyara Jam’iyyar PDP 
Tattaunawa

Dalilin Da Ya Sa PDP Ke Cikin Rikici, Za Ta Dawo Da Karfin Ta —Saraki

April 4, 2026
Zan Hada Hannu Da Gwamnati Wajen Bunkasa Yanki Na —Sarkin Tilden Fulani
Tattaunawa

Zan Hada Hannu Da Gwamnati Wajen Bunkasa Yanki Na —Sarkin Tilden Fulani

March 28, 2026
Next Post
NNPP Ta Rushe Shugabancinta A Kano Biyo Bayan Jita-jitar Sauya Sheƙar Abba Zuwa APC

NNPP Ta Rushe Shugabancinta A Kano Biyo Bayan Jita-jitar Sauya Sheƙar Abba Zuwa APC

Discussion about this post

LABARAI MASU NASABA

Mambobin NYSC 4, Soja da Mutum 1 Sun Rasu A Hatsarin Mota A Adamawa

Mambobin NYSC 4, Soja da Mutum 1 Sun Rasu A Hatsarin Mota A Adamawa

June 4, 2026
Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili

Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili

June 4, 2026
Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

June 3, 2026
Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

June 3, 2026
Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

June 3, 2026
Majalisa Ta Nemi Tinubu Ya Canza Dabarun Yaƙi Da Ta’addanci Don Kawo Ƙarshen Kashe-kashe

’Yan Majalisar Tarayya 3 Sun Fice Daga APC Zuwa ADC da PRP

June 3, 2026
An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos

An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos

June 3, 2026
Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

June 3, 2026
Gwamnatin Beijing Ta Amince Da Kafa Cibiyar Kirkire-Kirkiren Fasahar Lissafi Mai Nasaba Da Sararin Samaniya

Gwamnatin Beijing Ta Amince Da Kafa Cibiyar Kirkire-Kirkiren Fasahar Lissafi Mai Nasaba Da Sararin Samaniya

June 3, 2026
Za A Fara Buga Gasar Kofin Sarkin Gombe Bayan Masu Ruwa Da Tsaki Sun Cimma Matsaya

Za A Fara Buga Gasar Kofin Sarkin Gombe Bayan Masu Ruwa Da Tsaki Sun Cimma Matsaya

June 3, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.