ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 25, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tsayuwa Da Ƙafa Biyu Ya Fi Tsayuwa Da Kafa Ɗaya

by Rabi'u Ali Indabawa and Sulaiman
3 months ago
Tsayuwa

Lokacin da na karbi ragamar aiki a matsayin Ministan Tsaro, na yi alkawarin karfafa tsarin tsaron kasar. Na jaddada cewa, da farko, a matsayinmu na ‘yan Nijeriya dole ne mu dauki alhakin daukar nauyin da kalubalen da kasarmu ke fuskanta.

 

Wannan ba kawai magana ba ce, illa kira ne zuwa aiki. Ina kuma tsaye daram wajen tabbatar da cewa mun fuskanci kalubalen tsaronmu kai tsaye ta hanyar amfani da falsafar “hadin kai da manufa daya”, wadda ke nufin mu yi aiki tare a matsayin kungiya guda, maimakon kowanne bangare ya yi aiki shi kadai kamar rundunar da ke zaman kanta. ”

ADVERTISEMENT

 

“Wannan ita ce falsafar da na bi a duk tsawon aikina na hidimta wa kasa a mukaman jagoranci da na ma’aikata a cikin aikin sojin Nijeriya. Wannan tunani ya ci gaba da kasancewa tare da ni har zuwa yau.

LABARAI MASU NASABA

An Nemi Shugabanni Su Rungumi Tafarkin Adalci A Tsakanin Al’ummunsu

Ƴan Bindiga Sun Tilasta Wa Ƙauyukan Sakkwato Biyan Sabon Haraji

 

Na kuma saba da bai wa jami’ai kwarin gwiwa da ke karkashina su fahimci muhimmancin wannan tunanin na dabarun tsaro, tare da aiwatar da shi a duk inda suka tsinci kansu a cikin aikinsu.

 

Matsayin da nake rike da shi a yau yana da nufin karfafa tsarin tsaron kasar, bisa ga umarnin da Bola Ahmed Tinubu, Babban Kwamandan Askarawan Nijeriya, ya ba ni.

 

Ina da cikakken kuduri da himma wajen mayar da fata da burin ‘yan Nijeriya su zama gaskiya ta hanyar kawo karshen ta’addanci a kasar.”

 

Daidaitawar Soji Da Farar Hula

“A lokacin da nake hidima a matsayin jami’in soja, daya daga cikin kalubalen da na fuskanta shi ne daidaita tunanin soja da al’adun farar hula. Akwai lokuta da dama da dole ne mutum ya saurari ra’ayin farar hula wajen magance matsalolin tsaro yayin da suke faruwa.

 

A lokutan da na bi ra’ayin farar hula, na ga sakamakon da na samu a matsayin kwamanda ya burge ni matuka. Duk da na san cewa wasu daga cikin shawarar da na yanke ba su yi wa wasu daga cikin sojojina dadi ba, amma a matsayina na kwamanda, dole ne su amince da hukuncin da na yanke.

 

A koyaushe ni nake daukar alhakin wadannan shawarwari. Idan na waiwaya baya yanzu, ina farin ciki da na yanke wadannan matakai domin sun tabbatar da cewa suna da amfani sosai.”

 

Haramtaccen Yaki Da Ingantacce

Yakin da bai da daidaito ba za’a auna shi da yawan ‘yan ta’adda da aka kashe a daji kawai ba, amma da yawa akwai mutanen da aka ‘yanto daga shiga ta’addanci ko aka fito da su daga daji. Wannan yana nuna juriya a yaki, wato daga kirga gawarwaki zuwa halastaccen mulki.

 

Yakin da ‘yan ta’adda ke yi yana da wahala kuma sau da yawa yana taba yunkurin dakaru ne kawai, wanda hakan zai kai ga jama’a su gaji da jinkirin samun sakamako. Amma halattaccen yaki yana mai da hankali kan gano tushen matsalolin da ke haddasa rikicin. Saboda haka, dabarun aikina sun ginu ne a kan hada wadannan hanyoyi biyu domin samun sakamako mai dorewa.

 

Nadin da aka yi min daga baya a matsayin Babban Hafsan Tsaro (CDS) ya ba ni damar fadada gano abin da ake kira “tsarin Borno” a cikin ayyukan soji..

 

Ina tuna cewa a lokacin da nake CDS, a taron Kwamandojin Rundunar Hadin Gwiwa na CDS mai taken Inganta hadin Kai A Sansanin Soji”, na jaddada muhimmancin hadin kai wajen aiki, amfani da dabaru, da kuma hada al’umma baki daya wajen magance matsalolin tsaro.

 

Misali, canza sunan aikin hadin gwiwar soja a Jihar Filato daga ‘Operation Safe Haben’ zuwa ‘Operation Enduring Peace’ wanda an yi shi ne domin samar da sabon hangen nesa ga sojoji da al’ummomin yankin kan muhimmancin yin aiki tare domin samar da zaman lafiya mai dorewa a Jihar Filato.

 

Ina alfahari da cewa wannan dabarar tana aiki a jihar da kuma a sauran wuraren da sojojin Nijeriya ke gudanar da ayyukansu a fadin kasar.

 

Dabarun Hada Kan Al’umma

Akwai wani abu da na fahimta wanda nake son jaddadawa. Ba kasafai ake ganin sa a fili a cikin al’umma. A halin yanzu muna yaki ne da rikici mai sassa da dama. Kungiyoyin ta’addanci kamar Boko Haram, ISWAP, da Lakurawa da wasu kungiyoyin masu tashin hankali sun hada kai, sun ajiye sabanin da ke tsakaninsu domin su yi aiki tare su kai hare-hare. A wasu lokuta ma suna musayar bayanan sirri a tsakaninsu.

 

Wannan gaskiya ce, kuma shi ya sa ake bukatar abin da ake kira “tsayuwa da kafafu biyu”, wato hada dabarun karfi na soja da kuma dabarun da ba na soja ba a cikin ayyukan tsaronmu, domin samar da daidaito da ake bukata wajen kayar da ta’addanci.

 

Idan kungiyoyin ta’addanci na iya hada kai, me zai hana jama’ar kasa su hada kai da sojoji? Ba za mu iya kayar da ta’addanci da bindigogi da harsasai kawai ba. Wannan shi ne ainihin sakon da nake son isarwa a wannan rubutu.

 

Kwarewata a matsayin Kwamandan Yanki da Babban Hafsan Tsaro har yanzu tana da tasiri sosai a tunanina. Na kalli matsalolin daga matsayi na jagoranci da na ma’aikata. Misali, yanke shawarar bin ra’ayin farar hula ta hanyar yin hadin kai ba tare da tangarda ba da gwamnatin Jihar Borno ya haifar da gagarumar nasara a yaki da ta’addancin Boko Haram.

 

Wannan kuma yana karfafa hujjata ta cewa tsaro nauyi ne da kowa ke dauka. Wannan shi ne tsarin aiki a kasashen da suka ci gaba. Ban yarda cewa tsarinmu ya kamata ya bambanta ba.

 

Wannan shi ne tsarin da Ma’aikatar Tsaro ke aiwatarwa. Ina farin cikin ganin cewa dukkan sassan sojojin Nijeriya sun daidaita da wannan dabarar. Haka kuma ma’aikatar tana yin hadin gwiwa da masu ruwa da tsaki a cikin al’umma, cibiyoyin addini da na gargajiya, kafofin yada labarai, kungiyoyin farar hula, da sassan kasuwanci na musamman domin shiga cikin dabarar “Hadin Kan Al’umma Gaba daya” wajen magance kalubalen tsaro na kasa.

 

Mun tsara wani samfurin aika sako wanda ya dace da kowane matsayi na al’umma, har ma da mazauna karkara. Manufar ita ce samar da wayar da kai cewa idan muka hada kai, za mu iya kai da ta’addanci kasa idan muka dage a kan hakan.

 

Akwai abubuwa da dama da ke haifar da rashin tsaro, amma akwai hanya daya da za ta iya dakatar da shi. Kuma wannan hanya ita ce lokacin da ’yan Nijeriya suka dauki nauyin hakan, ba tare da la’akari da al’adu ko qabila ba. Wannan nauyi ne na tilas domin juya yanayi a kan wadanda ba sa fatan alheri ga kasarmu.

 

‘Yan Kallo Da Ba Sa Kawo Dauki

Kwanan nan na gabatar da jawabi na musamman a taron shekara-shekara na Kungiyar Tsoffin Daliban Kwalejin Tarayya ta Kaduna a matakin duniya. Na jaddada cewa:

 

“Tarihi yana koya mana cewa babu wata kasa da za ta kasance mai tsaro idan ’yan kasarta suna zama masu kallo da ba sa shiga tsakani.”

 

Na ba da misali cewa manomi a Sakkwato, mai kasuwanci a Legas, da malami a Enugu suna zama layin farko na tsaro a kasa. Wannan yana kama da motsa muhawara kan tsaro daga sansanonin soja zuwa tituna, yana nuna cewa tsaro nauyi ne da ke wuyan kowa. Sojoji ba za su iya kasancewa a ko’ina ba. Saboda haka, ya zama dole ’yan Nijeriya su kasance masu shiga tsakani cikin tsarin tsaro, ba masu kallo marasa shiga tsakani ba.

 

Wannan rubutu na zaba masa take mai sauki wato “Tsayuwa da kafafu biyu ya fi tsayuwa da kafa daya”. Wannan dabara ce da ta dace da sabon tunani da muke kokarin gabatarwa.

 

Ina son sakon ya kai ga kowa, daga mai POS a Ibadan, mai dinki a Kaduna, har zuwa ma’aikacin gwamnati a Port Harcourt. Wannan wajibi ne, kuma yana dauke da alkawari zuwa ga ’yan Nijeriya na “tsayuwa da kafafu biyu” a yaki da ta’addanci.

 

Na dauki wannan alkawari ne a ranar 21 ga Satumba, 1991, lokacin da aka ba ni Kwamishinan Shugaban Kasa don aiki a Rundunar Sojan Nijeriya a matsayin jami’in soja na kasa. Dole ne mu hada kai don canza al’adar tsaro ta kasa.

Tsayuwa
Rabi'u Ali Indabawa
+ posts Bio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Nijar Ta Rattaba Hannu A Kan Dokar Haramta Auren Jinsi
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Za Mu Iya Sayar Da Manmu Ba Tare Da Wata Matsala Ba -Iran
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Dattawan Arewa Sun Buƙaci Tinubu Ya Ayyana Dokar Ta-baci Kan Tabarbarewar Tsaro
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Nijeriya Ta Karbi Ƴan Nijeriya 268 Da Suka Tsero Daga Afirka Ta Kudu
Tsayuwa
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace
  • Sulaiman
    ’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin
  • Sulaiman
    Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi
  • Sulaiman
    Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

MASU ALAKA

Nijeriya
Rahotonni

An Nemi Shugabanni Su Rungumi Tafarkin Adalci A Tsakanin Al’ummunsu

June 20, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Gidaje 14,940 A Sokoto
Rahotonni

Ƴan Bindiga Sun Tilasta Wa Ƙauyukan Sakkwato Biyan Sabon Haraji

June 20, 2026
IMF
Rahotonni

Tattalin Arziƙin Ƙasa: Masana Sun Buƙaci Tinubu Ya Yi Hattara Da Shawarar IMF

June 20, 2026
Next Post
gombe

Gwamnonin Arewa Sun Yi Allah-wadai Da Hare-haren Ƙunar Baƙin Wake A Maiduguri

LABARAI MASU NASABA

Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace

Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace

June 24, 2026
’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin

’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin

June 24, 2026
Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

June 24, 2026
Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

June 24, 2026
Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi

Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi

June 24, 2026
Kasar Sin Na Kara Zama Babban Ginshikin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya Na Gaba

Kasar Sin Na Kara Zama Babban Ginshikin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya Na Gaba

June 24, 2026
Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma

Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma

June 24, 2026
Sabbin Ministoci

Kafa ‘Yansandan Jihohi: Majalisa Ta Amince Da Tsarin ‘Yar Tinƙe Wajen Kaɗa Ƙuri’a 

June 24, 2026
Sin Ta Gabatar Da Tsarin Karfafa Kwarin Gwiwar Kamfanoni Masu Jarin Waje

Sin Ta Gabatar Da Tsarin Karfafa Kwarin Gwiwar Kamfanoni Masu Jarin Waje

June 24, 2026
Shugaban Kasar Burundi: Dangantakar Afirka Da Sin Misali Ce Ta Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa

Shugaban Kasar Burundi: Dangantakar Afirka Da Sin Misali Ce Ta Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa

June 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.