ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wace Dama Ce Ta Ragewa Arsenal?

by Abba Ibrahim Wada
5 months ago
Arsenal

Masu sharhi a kwallon kafa suna ci gaba da bayyana ra’ayinsu a kan halin da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal take ciki na yiwuwar rasa gasar firimiya ta Ingila bayan da Arsenal din ta sake tsintar kanta a wani yanayi na rashin tabbas a karshen kakar wasa duk da cewa ana ganin har yanzu Arsenal din tana da damar lashe gasar.

Duk da cewa ana ganin Arsenal din ba za ta iya ba, amma har yanzu magoya bayan Arsenal na ci gaba da alhinin rashin nasarar da kungiyar ta yi a wasanta da Manchester City na ranar Lahadi. Rashin nasarar da kungiyar ta yi da ci 2-1 ya sake jefa ta cikin babbar barazanar gaza lashe Kofin Premier da ta shafe fiye da shekara 20 tana kishirwarsa.

A shekarun baya-bayan nan kungiyar kan nuna alamun lashe kofin ta hanyar hawa teburin gasar tare da bayar da tazara mai yawa, amma ana zuwa karshen kakar sai komai ya sukurkuce mata. Hakan ce ma ta sa masu bibiyar kwallon kafa, musamman masu hammaya da ita ke yi mata kirari da ”Kofi Haram”.

ADVERTISEMENT

A wannan kaka kungiyar ta yi yunkurin goge wannan kirari, musamman ganin yadda ta jima a kan teburin gasar ta tazara mai yawa da ta bai wa City ta biyu. To sai dai da alama da wuya hakar kungiyar ta cimma ruwa, bayan shan kaye da 2-1 a hannun AFC Bournemouth da kuma 2-1 a hannun City, lamarin da ya rage tazarar makin da ke tsakaninsu zuwa uku, yayin da Manchester City ta je ta doke kungiyar kwallon kafa ta Burnley a kwantan wasan da take da shi kuma ya ba ta damar komawa mataki na daya.

A yanzu da ya rage wasa biyar a karkare gasar tambayar da mafi yawan masu bibiyar kwallon kafa ke yi ita ce ko Arsenal za ta iya karya bakin kirarin da ake yi mata na Kofi Haram? ko kuwa dai tarihi zai ci gaba da maimaita kansa?

LABARAI MASU NASABA

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana

A wajen magoya bayan Arsenal, watan Afrilu ya ci gaba da kasancewa wata mafi tsanani a wajensu. Alkaluma sun nuna cewa a wannan watan ne Arteta ke yawan rashin nasara a wasannin Premier, wani abu da alamu ke nuna cewa zai maimaita kansa a wannan shekarar ma, kasancewar ta yi rashin nasara biyu zuwa yanzu a cikin watan.

Wasu suna ganin akwai rashin kwarewa a wajen mai horarwa Mikel Arteta musamman ta juriya da mayar da hankali saboda ana ganin ba za a hada shi da Pep Guardiola ba wanda shi ne ya koya wa Arteta aiki kuma ya zama mataimakinsa a Manchester City kafin daga baya Arsenal din ta dauki Arteta ya koma mai horar da ‘yanwasanta.

A watan Afrilun shekarar 2021, Arsenal karkashin Arteta ta yi wasa hudu, inda ta ci daya kawai, ta yi rashin nasara biyu tare da kunnen doki daya.

Haka ma a Afrilun shekara ta 2022, kungiyar ta buga wasa 5, ta ci biyu daga ciki ta kuma yi rashin nasara uku. A Afrilun shekara ta 2023 ma, Arsnela ta buga wasa 5, inda ta ci guda daya tare da yin kunnen doki a uku da kuma rashin nasara daya.

To amma a shekara ta 2024, abubuwa sun sauya, inda ta buga wasanni 6, ta ci 5 daga ciki da rashin nasara daya. Amma a Afrilun 2025 da ya gabata sai aka sake komawa gidan jiya, inda ta buga wasa 5, ta ci 2 da kunnen doki 3.Sai dai duk da haka Arteta na da kwarin gwiwa, kamar yadda ya bayyana a taron manema labarai da ya gabatar bayan wasan da suka yi rashin nasara a filin wasa na Ettihad.

Arteta ya ce sun yi rashin nasara a wasa mai muhimmanci, amma har yanzu suna da kwarin gwiwa kuma suna da yakinin cewa za su lashe gasar ta bana.

Wasanni 5 da suka rage wa Arsenal

Newcastle United (Gida). Fulham (Gida). West Ham United (Waje). Burnley (Gida). Crystal Palace (Waje).

Wasanni 6 da suka rage wa City

Burnley (Waje). Eberton (Waje). Brentford (Gida). AFC Bournemouth (Waje). Crystal Palace (Gida). Aston Billa (Gida)

Arsenal
Abba Ibrahim Wada
Website |  + postsBio
  • Abba Ibrahim Wada
    Yaushe Za A Fara Kofin Zakarun Turai
  • Abba Ibrahim Wada
    Messi Ya Yi Ritaya A Argentina: Da Me Za Mu Iya Tuna Gwarzon Duniyar?
  • Abba Ibrahim Wada
    Su Waye ‘Yan wasan Nijeriya Da Za Su Buga Gasar Firimiyar Ingila Ta Bana?
  • Abba Ibrahim Wada
    Chelsea A Ƙarƙashin Xavi Alonso

MASU ALAKA

Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana
Wasanni

Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana

September 8, 2026
Kofin Duniya: Yau Falconets Za Su Kece Raini Da Spain
Wasanni

Kofin Duniya: Yau Falconets Za Su Kece Raini Da Spain

September 7, 2026
Next Post
An Kaddamar Da Ginin Tashar Ruwa Ta Kiwon Kifi Bisa Tallafin Sin A Saliyo

An Kaddamar Da Ginin Tashar Ruwa Ta Kiwon Kifi Bisa Tallafin Sin A Saliyo

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.