ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, July 15, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wane Taimako Rasha Da China Za Su Bai Wa Iran Idan Ta Fara Yaƙi Da Amurka?

by Rabi'u Ali Indabawa
5 months ago
Rasha

A duk lokacin da Iran da Amurka suka nuna wa juna yatsa, babbar tambaya ita ce:

Wane mataki China da Rasha za su ɗauka idan musayar yawu ta rikiɗe zuwa yaƙi?

Shin Iran za ta iya dogara da ƙasashen biyu masu ƙarfi ko kuwa ƙawancen da ke tsakanin Iran da waɗannan ƙasashe biyu taron dangi?

ADVERTISEMENT

Amsar waɗannan tambayoyi ta dogara ga irin dangantakar da ke tsakanin Iran da Moscow da kuma Beijing.

Masana dangantakar ƙasashe sun bayyana ƙawance a matsayin ƙulla yarjejeniyar tsaro yayin da aka kai wa ɓangare guda hari.

LABARAI MASU NASABA

Yadda Jana’izar Ruhullah Khomeini Ta Shiga Kundin Tarihi Na Guinness

Iran Ta Harba Wa Jiragen Ruwa Makamai Masu Linzami A Mashigar Hormuz

  • An Shirya Bikin Share Fagen Shirin Talibijin Na CMG Na Murnar Sabuwar Shekarar Gargajiyar Kasar Sin A Kasashen Rasha da Faransa Da Brasil Da Kuma Koriya Ta Kudu
  • Ministar Wajen Madagascar Ta Yi Kiran Inganta Alakar Kasarta Da Kasar Sin Kafin Bikin Bazara Na Sinawa

Babu irin wannan yarjejeniya tsakanin Tehran da waɗannan ƙasashe masu ƙarfi.

Wata yarjejeniya da aka ƙulla tsakanin Tehran da Moscow a watan Janairun shekara ta 2024 duk da ta ƙunshi batun tsaro da haɗin kai a ciki amma babu batun kai taimakon sojoji yayin da aka kai wa wani ɓangare hari.

Hamidreza Azizi, masanin alaƙar ƙasashe ya shaida wa Sashen Farsi na BBC cewa ƙawancen soji shi ne ƙololuwar dangantaka tsakanin ƙasashe, sannan babu wannan a tsakanin Iran da China da kuma Rasha.

”Yayi imanin cewa ko a lokacin yaƙi zai yi wuya Moscow da Beijing su kai wa Iran wata muhimmiyar gudummawa. Za su iya bayar da gudunmawarsu amma a matakin diflomasiyya.

 

Nahiya: Me ya sa taimakon zai yi wahala?

Wani abin la’akari shi ne yanki ko nahiya abubuwan dubawa ne; Chaina da Rasha na da kyakkyawar alaƙa a Gabas ta Tsakiya.

Beijing babbar abokiyar hulɗar tattalin arziƙi ce ga Saudiyya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da kuma Isra’ila.

Moscow na hulɗa kai tsaye da Tehran da Tel Aɓiɓ da kuma wasu ƙasashen Larabawa.

Shiga yaƙi kai tsaye tare da Iran zai iya zama ƙalubale cikin wannan haɗaka.

Dukkan ƙasashen masu ƙarfi na gasa da Amurka. Rasha na yaƙi da Ukraine don haka sojojinta da siyasarta a takure suke.

Ita ma Chaina ta mayar da hankali wajen gasa da Amurka musamman a gabashin yankin Asiya da kuma batun Taiwan.

Don haka buɗe babin sabon rikici a Gabas ta Tsakiya ko da kai tsaye ne ba zai hafar musu da ɗa mai ido ba.

Yulia Roknifard farfesa a jami’ar Taylor da ke Malaysia ta shaida wa BBC cewa ”Rasha da China za su iya kallon wannan sabon lamari a matsayin damar da za su yi amfani da ita wajen goyon bayan abokin hulɗar da ya fi muhimmanci a tsakaninsu, Iran mamba ce a ƙungiyar BRICS kuma mamba a ƙungiyar Shanghai Cooperation Organization don haka Moscow da Beijing ba za su zuba ido a lalata ɗaya daga cikin mambobinsu ba.”

 

Yaƙin ”kwanaki 12” da iyakokinsa

Misali guda da za a iya bayarwa zai bada hoton matsayin Chaina da Rasha lokacin da Jamhuriyar Musulunci ta fuskanci barazana daga waje.

A sake duba kwanaki goma 12 na yaƙin Iran da Isra’ila a lokacin tsakanin Moscow da Beijing ba wanda ya taimaka wa Jamhuriyar Musulunci sai a matakin siyasa. Babu wani taimakon soji daga ƙasashen biyu.

Kodayake ita ma Iran ta dage cewar ba ta nemi taimakon ƙasashen biyu ba.

Bayan yaƙin kakakin Dakarun Juyin Juya Halin Iran IRGC ya sanar cikin watan Nuwamban shekara ta 2025 cewar:

”Babu wata yarjejeniyar da aka ƙulla da waɗannan ƙasashe biyu a matakin sojoji sannan babu buƙatar neman taimako.”

Hamidreza Azizi ya yi imani tasirin ƙasashen biyu mambobi a Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya abin dubawa ne a rikicin.

Kafofin Yaɗa Labarai da suka haɗa da CNN da mujallar Financial Times sun fidda rahoto a shekarar da ta gabata inda suke ce ganau daga Hukumar Tattara Bayanan Ƙasashen Yamma sun bayyana yadda Chaina ta aika da man da jiragen yaƙi za su yi amfani da shi Iran.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Chaina ta mayar da martani inda ta ce ba ta da masaniya game da wannan labari sannan ta yi watsi da abin da ta kira ”zargi maras tushe,” ta kuma ƙara da cewar sinadarin sodium perchlorate ba shi da wata ƙa’ida a Chaina kuma fidda shi ba laifi ba ne a ƙasar.

Mista Azizi ya yi imanin idan rikicin ya yi tsanani akwai yiwuwar a samu taƙaitaccen samun bayanan sirri ko taimakon na’urori ba tare da Chaina da Rasha sun shiga yaƙi kai tsaye da Amurka ba.

Yulia Roknifard ta yi imanin Rasha da Chaina ba sa buƙatar sanar da taimakon da suke bai wa Iran a fili kamar yadda Iran ta ɓoye irin taimakon da ta bai wa Rasha a farkon yaƙi da Ukraine.

 

Fargabar sauyin gwamnati?

Wasu masu sharhi na ganin sauyin gwamnati a Iran zai sauya tunanin Moscow da Beijing.

Iran dai mamba ce a Ƙungiyar BRICS da Shanghai Cooperation Organization don haka tana da muhimmanci a tsakiyar Asiya da kuma Gabas ta Tsakiya.

Daga wannan mahanga za a fahimci rusa siyasar Tehran zai haifar wa Moscow da Beijing komabaya a yunƙurinsu na ƙarawa kansu ƙarfi.

Yulia Roknifard ta ce rusa gwamnatin Musulunci da samar da sabuwar gwamnati mai goyon bayan Amurka barazana ce ga Rasha da Chaina

Sai dai masu sanya ido na ganin koda an kafa sabuwar gwamnati, ba za su bayar da taimakon soji ba amma za su iya taimaka wa tattalin arziƙi da bayanan sirri da kuma makamai.

Amma shigar su yaƙi kai tsaye zai yi wahala.

 

Tattalin arziƙi: Abin da Iran ta fi buƙata

Ƙarfin tattalin arziƙi zai iya sa gwamnati ta jure a Tehran ya yin da karyewar tattalin arziƙi zai haifar da tarzoma.

A wannan gaɓa ne kuma Chaina zata taka muhimmiyar rawa kodaye abubuwan da suka faru a shekarun baya-bayan nan sun sa Beijing na taka tsan tsan.

Sabbin rahotannin sun bayyana yadda Beijing ta rage siyan man Iran a watannin baya bayan nan.

Ƙididdiga daga kamfanonin mai ta nuna a baya Chaina na sayen mai daga Iran da ya kai ganga miliyan 1.4 kowacce rana a shekarar da ta gabataa, amma a yanzu ta na sayen ganganr mai kusan 800,000 zuwa 900,000 kowacce rana a makonnin baya- bayan nan.

Komabayan ya biyo bayan takunkumin da Amurka ta sanyawa harkar fito. Lamarin da zai iya hana Iran samun isassun kuɗaɗen shiga idan rikicin ya yi tsanani.

A baya bayan nan Rasha ma ta nuna haɗin kan da ta ke bai wa Iran na wucin gadi ne. Daga cibiyar makamashi ta Bushehr da isar da na’urorin kare kai daga farmaki, an ga yadda Rasha ta ke jinkirtawa tare da sanya siyasa a al’amarin.

 

‘Akwai taimako amma ban da lokacin yaƙi’

Gabaɗaya akwai yiwuwar idan rikici ya rincaɓe ko kuma taƙaitaccen rikici ya ɓarke tsakanin Iran da Amurka, China da Rasha za su bi tsari ɗaya: Adawar diflomasiyya da Washington da yunƙurin kwantar da rikicin da kuma wataƙila bayar da haɗin kai a bayanan sirri da Tehran.

Amma shiga yaƙin kai tsaye zai yi wahala idan aka yi la’akari da abin da ya faru a baya.

Yulia Roknifard ta ƙara da cewa : “A yanzu babban burin Chaina da Rasha shi ne aikawa da saƙonnin da za su dakatar da Amurka jibge dakaru a yankin.”

Hamidreza Azizi ya ce idan yaƙi ya ɓarke, kar a yi tsammanin Chaina ko Rasha za su taimakwa Iran da sojoji.

A taƙaice abin da ke tsakanin Tehran da Moscow da kuma Beijin ya fi ƙarfin haɗin kan tsaro, wani haɗin kai ne da aka ƙirƙira sakamakon matsin lambar ƙasashen ‘yamma

 

Rasha
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Wasu Fusatattun Mutane Sun Lakaɗa Wa Mutum Biyu Duka Har Lahira A Kaduna
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Mun Ɗauki Nauyin Karatun Masu Digiri Ta Hanyar Sayar Da Ƙosai Da Ƙuli-ƙuli —Wasu Ƴan Kasuwa
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Adadin Mutanen Da Tsananin Zafi Ya Kashe A Turai Ya Haura Dubu 1,300 —WHO
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Pakistan Ta Kashe Mutum 36 A Hare-haren Da Ta Kai Kan Iyakarta Da Afghanistan

MASU ALAKA

Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Kasashen Ketare

Yadda Jana’izar Ruhullah Khomeini Ta Shiga Kundin Tarihi Na Guinness

July 10, 2026
Iran Ta Harba Wa Jiragen Ruwa Makamai Masu Linzami A Mashigar Hormuz
Manyan Labarai

Iran Ta Harba Wa Jiragen Ruwa Makamai Masu Linzami A Mashigar Hormuz

July 7, 2026
Adadin Mutanen Da Tsananin Zafi Ya Kashe A Turai Ya Haura Dubu 1,300 —WHO
Kasashen Ketare

Adadin Mutanen Da Tsananin Zafi Ya Kashe A Turai Ya Haura Dubu 1,300 —WHO

July 5, 2026
Next Post
Trump Ya Yi Kira Ga Iraniyawa Su Fara Yunƙurin Sauya Gwamnati

Trump Ya Yi Kira Ga Iraniyawa Su Fara Yunƙurin Sauya Gwamnati

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Yusuf Ya Bai Wa Masu Kula Da Akwatinan Zaɓe Na APC Filaye 1,540 Da Tallafin Miliyan 100

Gwamna Yusuf Ya Bai Wa Masu Kula Da Akwatinan Zaɓe Na APC Filaye 1,540 Da Tallafin Miliyan 100

July 15, 2026
Sabbin Ministoci

Rashin Tsaro: Majalisar Dattawa Ta Bukaci A Tura Ƙarin Sojoji da ’Yansanda Zuwa Benuwe

July 15, 2026
GDPn Sin A Rabin Farko Na Shekarar 2026 Ya Karu Da Kashi 4.7% Idan Aka Kwatanta Da Na Kwatankwacin Lokacin Bara

GDPn Sin A Rabin Farko Na Shekarar 2026 Ya Karu Da Kashi 4.7% Idan Aka Kwatanta Da Na Kwatankwacin Lokacin Bara

July 15, 2026
‘Yansanda Sun Tsaurara Tsaron Iyakokin Kano Bayan Hare-haren ‘Yan Bindiga 

Atiku Ya Nuna Damuwa Kan Kasafin Naira Biliyan 6.44 Don Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026

July 15, 2026
Masana Kandagarkin Cututtuka Na Sin Sun Tashi Zuwa Kasar Uganda Don Aikin Hadin Gwiwar Magance Cutar Ebola

Masana Kandagarkin Cututtuka Na Sin Sun Tashi Zuwa Kasar Uganda Don Aikin Hadin Gwiwar Magance Cutar Ebola

July 15, 2026
‘Yan Ƙasar Turkiyya Sun Nuna Jarumta Da Kare Dimokuraɗiyya Mafi Girma A Tarihi – Erdoğan

‘Yan Ƙasar Turkiyya Sun Nuna Jarumta Da Kare Dimokuraɗiyya Mafi Girma A Tarihi – Erdoğan

July 15, 2026
Majalisa Ta Ba da Tallafin ₦50m Ga Iyalan Malamai Da Jami’an Tsaro Da Aka Kashe A Aikin Ceto A Oyo

Majalisa Ta Ba da Tallafin ₦50m Ga Iyalan Malamai Da Jami’an Tsaro Da Aka Kashe A Aikin Ceto A Oyo

July 15, 2026
Xi Ya Bukaci A Mayar Da Hankali Kan Bukatun Jama’a Yayin Rangadin Da Ya Yi A Shanghai

Xi Ya Bukaci A Mayar Da Hankali Kan Bukatun Jama’a Yayin Rangadin Da Ya Yi A Shanghai

July 15, 2026
Katsina: Kotu Ta Yanke Wa Hauwa’u Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Taimaka Wa ’Yan Bindiga

Lalata Da Ƙaramar Yarinya: Kotu Ta Yanke Wa Tsoho Mai Shekara 75 Hukuncin Ɗaurin Shekara 10 A Ribas

July 15, 2026
Ci Gaban Fasaha Na Hidimtawa Jama’a Cikin Kowane Yanayi A Kasar Sin

Ci Gaban Fasaha Na Hidimtawa Jama’a Cikin Kowane Yanayi A Kasar Sin

July 15, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.