ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, June 24, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wata Uku Da Kafa Dokar Ta-ɓaci: Har Yanzu Matsalar Tsaro Na Ci Gaba Da Ta’azzara

by Sani Anwar
4 months ago
Wata

Tsawon wata uku kenan yanzu, bayan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kafa dokar ta-ɓaci kan tsaro, amma har yanzu kashe-kashe da sace-sacen Ƴan Nijeriya ba su lafa ba.

Hasali ma, da alama an ta’azzara ayyukan ta’addanci, domin kuwa an samu ƙaruwar sace-sacen ƴan Nijeriya ko kuma kashe su a cikin waɗannan Ƴan watanni.

  • Kasar Sin Ta Bukaci Amurka Ta Soke Harajin Da Ta Kakaba Bayan Hukuncin Kotun Kolin Kasar
  • Tinubu Ya Sanya Hannu Kan Dokar Gyaran Zaɓe Duk Da Rikicin Tura Sakamako

A ranar Laraba, 26 ga watan Nuwambar 2025, shugaba Tinubu, ya ayyana dokar ta-ɓaci a dukkanin faɗin wannan ƙasa, tare da bayar da umarnin ƙara ɗaukar sabbin ma’aikata a rundunar soji.

ADVERTISEMENT

Har ila yau, an ɗauki matakin ne da nufin kawo ƙarshen sace-sacen jama’a da kashe-kashen da ƴan ta’adda da ƴan bindiga ke yi a sassan ƙasar.

Ya ce, “Gwamnatinmu za ta tallafa wa gwamnatocin jihohin da suka kafa jami’an tsaro, don kare jama’arsu daga ƴan ta’addan da ke da niyyar kawo cikas ga zaman lafiyar ƙasarmu.”

LABARAI MASU NASABA

Zargin Ɓata Suna: Kwankwaso Ya Yi Barazanar Neman Diyyar Naira Biliyan 10 Kan Wani Malamin Coci

Atiku Ya Soki Tsare El-Rufai, Ya Ce Sharuɗan Belinsa Sun Yi Tsauri

Shugaban ya kuma yi kira ga majalisar dokokin ƙasar, da ta fara duba dokokinmu, domin bai wa jihohin da ke buƙatar kafa Ƴan sandan a jihohinsu.

Ya kuma bayar da umarnin a ɗauki manya-manyan ma’aikata na jami’an tsaro a dukkanin faɗin Nijeriya, inda ya umarci Ƴan sanda da su ƙara ɗaukar ma’aikata 20,000, wanda ida aka haɗa za su kai kimanin 50,000 da ake ci gaba da ɗaukar.

Shugaba Tinubu ya kuma bayar da izinin mayar da sansanonin masu yi wa ƙasa hidima (NYSC), zuwa wuraren horar da ƴansanda na wucin gadi, sannan ya bayar da umarnin a janye jami’an da ke ba da kariya ga mutane na musamman (ɓIP), domin sake horar da su nan take kafin a tura su wuraren da ake fuskantar ƙalubalen tsaro.

Haka zalika, ya bai wa hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), damar tura ƙwararrun jami’an tsaron daji, domin fatattakar Ƴan ta’adda da Ƴan bindiga da ke ɓoye a cikin dazuzzukan, ya kuma umarci hukumar da ta ɗauki ƙarin jami’an da za su ƙarfafa aikin. “Ba za a ƙara samun mafakar masu aikata miyagun laifuka ba,” in ji shi.

Shugaban ya kuma yaba wa jami’an tsaron da suka samu nasarar kuɓutar da Ƴan mata 24 da aka yi garkuwa da su a Jihar Kebbi da kuma masu ibada 38 da aka yi garkuwa da su a Jihar Kwara, ya kuma ƙara da cewa; ana ci gaba da ƙoƙarin ceto sauran waɗanda aka yi garkuwa da su, ciki har da ɗaliban da aka sace a Jihar Neja.

Da yake jawabi ga rundunar sojojin, Tinubu ya yaba da jajircewarsu, tare da buƙatar su ci gaba da jajircewa a kamar yadda suka saba.

“Bai kamata a yi sulhu da Ƴan ta’adda ba, babu wani batu na haɗa kai da su, sannan ya kamata ku san cewa; al’ummar Nijeriya da ku suka dogara,” in ji shi.

To sai dai kuma, tun bayan wannan sanarwar, da alamun kashe-kashe da sace-sacen jama’a na ƙara ta’azzara, koda-yake, hukumomin tsaro sun dage cewa; suna kan gaba wajen shawo kan al’amarin taɓarɓarewar tsaron.

Alal misali, hedikwatar tsaro ta ce; ta fara jigilar dakaru na musamman da kayan aiki zuwa yankuna masu nisa.

Rundunar sojin Nijeriya ta kuma yi iƙirarin cewa; ta tura ƙarin dakaru na musamman Jihohin Benuwe, Plateau, Nasarawa da Taraba, domin ƙarfafa ayyukan yaƙi da ta’addanci.

A cewar hukumomin sojin, waɗannan matakan sun kai ga kawar da Ƴan ta’adda da dama da suka haɗa da wasu shugabanninsu.

A baya-bayan nan, daraktan yaɗa labarai na tsaro, Manjo Janar Michael Onoja, ya bayyana cewa; an kashe shugabanin Ƴan ta’adda da dama, yayin da wasu suka miƙa wuya ga sojoji a sansanoni daban-daban.

Ya ƙara da cewa, a cikin watan Janairu kaɗai, sojoji sun kashe Ƴan ta’adda da dama, tare da kame mutum sama da 270 da ake zargi da kuma kuɓutar da mutum 230 da aka yi garkuwa da su a wani samame a yankin Arewa.

Wata

Daga cikin waɗanda aka kawar, a cewar hedikwatar tsaron, akwai Munzir, wanda aka fi sani da Baa Yanziye, tare da wasu a yayin hare-haren ta sama. Bugu da ƙari, an kama ƴan ta’adda kimanin 34 a cikin makwanni biyu a yankin Arewa maso Gabas.

Har ila yau, an ce; wani shugaban Ƴan ta’adda mai suna Yakubu Adamu, ya miƙa wuya ga sojoji da makamai da alburusai a yankin Azir Wajiroko.

Sojojin sun ƙara damƙe mutum 34 da ake zargi, tare da ceto mutum 17 da aka yi garkuwa da su, da dai sauran nasarorin da aka samu a aikin farmakin.

Rashin Tsaro Na Barazana Ga Mazauna Kudancin Taraba

Jihar Taraba, ga dukkan alamu an kasa kawo ƙarshen kashe-kashe da kwanton ɓauna da kuma hare-haren wuce gona da iri a kan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, musamman a kudancin jihar.

LEADERSHIP ta tattaro cewa, kusan kowace rana a faɗin al’ummomin da abin ya shafa, mazauna Kudancin Taraba na yin gudun hijira, domin tsira da rayukansu, kazalika, ana ci gaba da samun rahotannin yin fyaɗe da satar kayayyaki jama’a masu matuƙar tsada.

Bayan kashe-kashen, bincike ya nuna cewa; an ƙona gidaje tare da amfanin gona, inda ake zargin masu aikata laifin sun mamaye wuraren da al’ummomin ke zaune.

Lamarin da ya zama kusan abin da za a iya cewa; ya zama ruwan dare a kullum, wanda hakan ya sa mutane da dama suka rasa matsugunai, tare da kashe mutane da dama, a wani abin da mazauna yankin suka bayyana a matsayin hada-hadar hare-hare kan manoman yankin.

Duk ƙoƙarin da wakilinmu na Jalingo ya yi, domin jin ta bakin kwamandan birgediya ta 6 na sojojin Nijeriya da kuma kwamishinan Ƴan sandan jihar, abin ya ci tura.

Muƙaddashin Daraktan hulɗa da jama’a na rundunar, Laftanar Umar Muhammad, bai amsa kiran waya da saƙon da aka aike masa ba, yayin da muƙaddashin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar Ƴansandan, ASP ɓictor Mshelizah, ya ce; ba shi da ikon cewa komai a kan al’amarin.

Sai dai, jami’in hulɗa da jama’a na hukumar tsaro ta farin kaya ta Nijeriya (NSCDC), CSC Samalia Iliya, ya tabbatar da cewa; rundunar sojin Nijeriya ce ke kan gaba a rundunar ‘Operation Safe Jalingo’.

Kakakin rundunar ya ce, an kafa rundunar ne a daidai lokacin da ake fama da rashin tsaro a jihar.

CSC Iliya, wanda ke wakiltar kwamandan NSCDC na jihar, Anthony Bala Bitrus, ya ce; rundunar tana aiki babu dare babu rana tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro, domin tabbatar da zaman lafiya, musamman a kudancin jihar.

“Dukkanin hukumomi suna aiki tare don tabbatar da ganin cewa; jihar ta kasance cikin zaman lafiya da walwala.

“A shekarar da ta gabata, an kama masu garkuwa da mutane da sauran matsalolin tsaro a Jalingo, an kuma samu kama tare da kashe Ƴan bindiga a unguwar Chanchagi da ke Takum da kuma Ƙananan Hukumomin Karim-Lamido da Wukari.

“Koda-yake, ban isa in yi magana mai zurfi a kan hakan ba, saboda ana gudanar da ayyuka ta ɓangarori biyu, ‘Operation Whirl Stroke’ ne ke kula da ayyukan a Takum, musamman Chanchagi. Ina tabbatar muku cewa, an kashe wasu daga cikin masu laifin, an kuma kama wasu.

“Hukumar NSCDC, tana shiga cikin dukkan ayyukan gwamnatin tarayya a Taraba, wanda sojojin Nijeriya ke gudanar da su.

“A Ƴan kwanakin nan, mun samu labarin afkawar Ƴan bindiga da rikicin ƙabilanci a kudancin jihar, amma da aka tura jami’an tsaro, an shawo kan lamarin.

“Ya zuwa yau, yawancin ƙananan hukumomi, suna da isasshen tsaro, sannan kuma laifuka sun ragu sosai, sai dai, a ƙananan hukumomi biyu.”

Ya gode wa Gwamna Agbu Kefas, da ya bayar da tallafin kayan aiki, inda ya ce; an samu nasarorin da aka samu sakamakon haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro.

An Kashe Sama Da Mutum 80, 90,000 Kuma Sun Rasa Muhallansu A Hare-haren Taraba

Cocin Katolika na Wukari, ya yi kira da a kai ɗaukin gaggawa, sakamakon hare-haren da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 80, tare da raba sama da mutum 90,000 daga muhallansu, tun a watan Satumban 2025.

Da yake yin jawabi bayan wata zanga-zangar lumana a Jalingo, ɓicar Pastoral, Reɓ. Fr. James Yaro, ya bayyana tashin hankalin a matsayin wani mummunan tashin hankali, musamman a unguwar Chanchanji da ke Ƙaramar Hukumar Takum, da kuma wasu sassan Ƙananan Hukumomin Ussa da Donga.

Ya yi zargin cewa, wasu da ake zargin Ƴan bindiga ne ke da alhakin hare-haren da suka jikkita al’ummomi da coci-coci sama da 200.

“Hare-haren, na faruwa ne da sanyin safiya lokacin da mutane ke tsaka da yin ɓarci, maharan suna kashe mutane babu gaira, babu dalili, suna ƙona gidaje tare da lalata kayan amfanin gonar da aka girbe,” in ji shi.

Ya bayar da misali da wani harin baya-bayan nan, a ƙauyen Mchia, inda aka ce; an kashe sama da mutum 10 da misalin ƙarfe 4:00 na safe, ranar 10 ga watan Fabrairun 2026.

Fr. Yaro ya yi kira da a tura ƙarin jami’an tsaro cikin gaggawa, a kuma gurfanar da waɗanda suka aikata wannan aika-aika tare da tattaunawa da juna, domin dawo da zaman lafiya mai ɗorewa.

Haka zalika, ya kuma yi gargaɗin cewa; idan ba a bayar da cikakkiyar kulawa da kariya ba, cocina na iya neman ƙasa da ƙasa su shiga tsakani.

Kwara: Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutum 171 Tare Da Sace 231,

Ga dukkan alamu, Jihar Kwara da ke shiyyar Arewa ta tsakiya, ta zama wata sabuwar cibiyar hare-haren ta’addanci da Ƴan bindiga ke farwa. A Ƴan kwanakin nan, an ce an yi garkuwa da mutane aƙalla 231 a faɗin jihar.

A tsawon lokacin da ake bitar, Ƴan ta’adda sun kashe mazauna garin Woro su kimanin 170 a Ƙaramar Hukumar Kaiama. Haka kuma, wasu Ƴan bindiga sun kashe wani jami’in tsaron daji a ƙauyen Koro da ke Ƙaramar Hukumar Ekiti.

Har ila yau, an sace masu ibada 35 daga Cocin Christ Apostolic (CAC) da ke Eruku a Ƙaramar Hukumar Ifelodun.

An kuma yi garkuwa da wasu mutum 176 a yankin Nuku da Woro na Ƙaramar Hukumar Kaiama.

Haka zalika, an sace wasu ma’aikatan gini su shida a gundumar Owa Onire da ke Ƙaramar Hukumar Ifelodun, an kuma yi garkuwa da mutum tara a unguwar Adanla da ke ƙaramar hukumar, yayin da aka yi garkuwa da wasu biyar kuma a hanyar Omu-Aran zuwa Isanlu.

Duk da cewa, wasu da aka yi garkuwa da su, sun samu Ƴancin kuɓuta, amma har yanzu waɗanda aka yi garkuwar da su 176 daga Kaiama, suna hannunsu, har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto.

Batun Tserewa Da Rufe Makarantu

Sakamakon hare-haren, kimanin iyalai 2,080 makiyaya ne suka rasa matsugunansu a Oro-Ago da ke Ƙaramar Hukumar Ifelodun.

An tilasta musu tserewa ne, biyo bayan ayyukan tabbatar da tsaro da nufin korar masu aikata laifukan ta’addancin a Oro-Ago da kewayenta.

A yayin gudanar da ayyukan, an bayar da rahoton cewa; tashin bama-bamai ta jiragen sama, ya lalata matsugunan makiyaya, lamarin da ya yi sanadiyyar tarwatsa jama’a da lalata gidaje da kuma asarar dabbobi.

Kazalika, iyalan Ƴan gudun hijirar, sun yi kira ga Gwamnatin Jihar Kwara da kuma gwamnatin tarayya, da su gaggauta shiga tsakani, domin samun sauƙin dawowarsu da sake gina gidajensu da kuma maido da rayuwarsu kamar yadda take a da.

LEADERSHIP ta tattaro cewa, ayyukan Ƴan bindiga, sun kai ga rufe makarantun firamare 57 a yankin Kwara ta Kudu, a daidai lokacin da rikicin ya ɓarke. An rufe Kwalejin Ilimi ta Jiha, Oro; Kwara, Malete; da kuma Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Ilorin, an kuma rufe na wani ɗan lokaci ne.

Sai dai kuma, an sake buɗe cibiyoyin, bayan da aka samu rahotannin inganta tsaro a yankunansu.

Tsokacin Hukumomin Tsaro

A ci gaba da ƙoƙarin kare jihar, kwamandan hukumar tsaro ta farin kaya (NSCDC) a jihar Kwara, Mista Bala Bawa Bodinga, ya bayyana cewa; daga yanzu rundunar za ta samar da tsaro a masallatai da coci-coci a ranakun Juma’a da Lahadi.

“Mun kuma sanya matakan kare muhimman kadarorin ƙasa da kuma rayuka da dukiyoyin al’ummar Jihar Kwara.

“Za a tura mutanenmu sintiri na dare, domin tabbatar da tsaro na sa’o’i 24 a faɗin jihar,” in ji Bodinga.

Ko’odinetan ƙungiyar tsaro ta haɗin guiwa mai kula da yankin Kwara ta Kudu, Elder Oyin Zubair, ya ce; al’amuran tsaro na ƙara inganta a gundumar.

A cewarsa, “Da alama shiga tsakani da shugaba Tinubu ya yi na haifar da sakamako mai kyau, inda sojoji suka ƙaddamar da ‘Operation India’ domin magance hare-haren ta’addanci a yankin Kwara ta Kudu. Aikin ya ƙunshi tura bataliyar sojoji yankunan da abin ya shafa, kuma jami’an tsaro suna aiki tare, domin samar da yanayi tsaro mai da kuma inganci.” Sai dai, mazauna yankin da dama sun dage cewa; har yanzu lamarin bai daidaita ba.

Wasu da suka zanta da LEADERSHIP, sun bayyana takaicinsu kan yadda ake ci gaba da kai hare-hare. Yayin da suka nuna amincewa da ƙoƙarin gwamnati, sun kuma ci gaba da cewa; dole ne a ƙara ƙaimi wajen kawar da masu aikata laifuka daga faɗin jihar.

Ya Kamata Hukumomin Tsaro Su Ƙara Ƙaimi – Abdullahi

Wani shugaban al’umma, kuma ko’odinetan ƙungiyar ‘Muslim Media Watch Group of Nigeria’ (MMWG) na ƙasa, Alhaji Ibrahim Abdullahi, ya yi kira da a ƙara ƙaimi wajen tura jami’an soji da Ƴansanda, domin yaƙar Ƴan bindiga yadda ya kamata.

“Masu aikata muggan laifuka, suna cin karensu babu babbaka, sakamakon rashin isassun ofisoshin Ƴansanda a lunguna da saƙo na ƙasar nan, tare da ci gaba da yi wa al’umma ɓarna, amma idan aka samu ƙarin ma’aikata da kayan aiki da tallafin sabbin jami’an tsaron dazuzzukan da aka horar, ko shakka babu, matsalolin rashin tsaron da muke fuskanta a Nijeriya za su yi matuƙar raguwa.

“Yayin da shugabannin ƙasar ke ci gaba da bayar da kuɗaɗe masu tarin yawa a duk shekara, rashin tsaro kuma na ci gaba da ƙaruwa, wanda abubuwa da dama su ne ke da alhakin faruwar hakan, ɗaya daga cikinsu shi ne, yadda jami’an tsaronmu ke mayar da martani a kai.

“An daɗe da ɗaukar nauyin makiya al’umma da ƙasar, amma ba a yin la’akari da masu ɗaukar nauyin nasu, ko kaɗan ba za su iya mamaye ƙasar nan ba, matuƙar jami’an tsaronmu sun yi aiki yadda ya kamata da dukiyoyin da ake ba su, sannan kuma dole ne jami’an tsaron namu su ɗauki wannan yaƙi da waɗannan miyagu a hankali, maimakon mayar da martani ta hanyar kashe-kashe,” in ji shi.

Babban mai taimaka wa gwamna na musamman kan harkokin tsaro, Alhaji Muhideen Aliyu, ya ce; gwamnatin jihar, ba ta bar wani abu ba a ƙoƙarinta na kawar da waɗannan miyagu daga jihar ta Kwara ba.

Ya ce, bayan ɗaukar aiki da horas da masu gadin gandun daji kusan 2,000, gwamnati na bayar da fifikon jin daɗin Ƴan banga na yankin da ke taimaka wa jami’an tsaro.

Muhideen ya bayyana cewa, fadar shugaban ƙasa ta tura cikakkun dakarun soji zuwa Kwara ta Arewa da Kwara ta Kudu, yankunan da Ƴan bindigar suka fi shafa.

Ya ƙara da cewa, Gwamna AbdulRazaƙ ya ci gaba da tattaunawa da fadar shugaban ƙasa da kuma ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, domin kawo ƙarshen ayyukan Ƴan bindiga a jihar.

Bayan Kafa Dokar Ta-ɓacin An Kashe Sama Da Mutum 60 A Neja

Tun lokacin da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kafa dokar ta-ɓaci kan tsaro a shekarar da ta gabata, an kashe mutum aƙalla 60 tare da yin garkuwa da sama da 100 a wurare daban-daban a yankin Neja ta Arewa.

A watan Nuwamban shekarar da ta gabata, jim kaɗan bayan sako ɗalibai da ma’aikatan makarantar Papiri, Ƴan bindiga sun yi garkuwa da mazauna ƙauyuka kusan 30 a watan Disamba, tare da kashe wasu mutum uku.

A watan Janairu, Ƴan bindiga sun kashe wani ɗan ɗariƙar octogenari tare da yin garkuwa da mutane da dama a yankin Borgu da ke kusa da Agwara.

Haka zalika, an ce an kashe mutanen ƙauyuka 45 a kasuwar Daji da ke Ƙaramar Hukumar Borgu, tare da sace wasu da dama.

A garuruwan Mariga da Magama wasu Ƴan bindiga sun kai hari a cikin al’umma, inda suka kashe mutum 10 tare da yin awon gaba da wasu da dama.

Wata
Sani Anwar
+ postsBio
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Tattalin Arziƙin Ƙasa: Masana Sun Buƙaci Tinubu Ya Yi Hattara Da Shawarar IMF
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Cututtukan Da Aka Fi Fama Da Su Lokacin Damina Da Yadda Za A Kauce Musu (2)
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Cututtukan Da Aka Fi Fama Da Su Lokacin Damina Da Yadda Za A Kauce Musu (1)
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Talauci Ya Sake Karuwa Da Kashi 63 Duk Da Sauye-sauyen Tattalin Arzikin Da Gwamnati Ta Yi – IMF

MASU ALAKA

Yadda Na Sayar Da Kadarori Na Don Ɗaukar Nauyin Ɗalibai A Ƙasashen Waje – Kwankwaso
Manyan Labarai

Zargin Ɓata Suna: Kwankwaso Ya Yi Barazanar Neman Diyyar Naira Biliyan 10 Kan Wani Malamin Coci

June 24, 2026
Tinubu Ya Gaza Wajen Magance Matsalar Tsaro A Nijeriya — Atiku
Manyan Labarai

Atiku Ya Soki Tsare El-Rufai, Ya Ce Sharuɗan Belinsa Sun Yi Tsauri

June 24, 2026
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta
Manyan Labarai

’Yansanda Sun Kama Wani Mutum da Harsasai 174 A Nasarawa

June 24, 2026
Next Post
Wata

Da Ilimi, Duk Abin Da Ke ɓoye Ya Fito Sarari

LABARAI MASU NASABA

Yadda Na Sayar Da Kadarori Na Don Ɗaukar Nauyin Ɗalibai A Ƙasashen Waje – Kwankwaso

Zargin Ɓata Suna: Kwankwaso Ya Yi Barazanar Neman Diyyar Naira Biliyan 10 Kan Wani Malamin Coci

June 24, 2026
Li Qiang Ya Halarci Bikin Bude Dandalin Tattalin Arzikin Duniya Na Davos Na Shekarar 2026

Li Qiang Ya Halarci Bikin Bude Dandalin Tattalin Arzikin Duniya Na Davos Na Shekarar 2026

June 24, 2026
Xi Ya Yi Kiran Daukar Matakan Zamanantar Da Aikin Gona Da Yankunan Karkara

Xi Ya Yi Kiran Daukar Matakan Zamanantar Da Aikin Gona Da Yankunan Karkara

June 24, 2026
Tinubu Ya Gaza Wajen Magance Matsalar Tsaro A Nijeriya — Atiku

Atiku Ya Soki Tsare El-Rufai, Ya Ce Sharuɗan Belinsa Sun Yi Tsauri

June 24, 2026
Trump Ne Zai Jagoranci Bayar Da Kofin Duniya A Wasan Ƙarshe – Infantino

Trump Ne Zai Jagoranci Bayar Da Kofin Duniya A Wasan Ƙarshe – Infantino

June 24, 2026
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

’Yansanda Sun Kama Wani Mutum da Harsasai 174 A Nasarawa

June 24, 2026
Sojoji Sun Kama Ɗan Fashi Da Makami A Taraba

Sojoji Sun Kama Ɗan Fashi Da Makami A Taraba

June 24, 2026
An Kashe Mutum 2, 8 Sun Jikkata Yayin Rikici A Bauchi

An Kashe Mutum 2, 8 Sun Jikkata Yayin Rikici A Bauchi

June 24, 2026
Tsohon Shugaban APC Na Kebbi Ya Rasu A Hannun ’Yan Bindiga

Tsohon Shugaban APC Na Kebbi Ya Rasu A Hannun ’Yan Bindiga

June 24, 2026
Ya Kamata Sin Da Birtaniya Su Yi Aiki Tare Don Ci Gaba Da Inganta Dangantakarsu

Ya Kamata Sin Da Birtaniya Su Yi Aiki Tare Don Ci Gaba Da Inganta Dangantakarsu

June 23, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.