ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Aka Kashe Kanal Da Sojoji 7 A Sabon Harin Boko Haram

by Sani Anwar
5 months ago

Kwamandan Bataliya ta 242, da ke Monguno, Kanal I.A. Mohammed, da sojoji kusan aƙalla 10 ne suka rasa rayukansu a lokacin da wasu bama-bamai da ake kyautata zaton ƴan tada ƙayar baya ne suka dasa a Ƙaramar Hukumar Monguno ta Jihar Borno.

Majiyoyin cikin gida sun ce, an kashe Kanal Mohammed, a lokacin da yake wani aikin ƙarfafa gwiwa, bayan wani harin da aka kai da daddare a sansanin sojoji. An ce, lamarin ya faru ne a lokacin da jami’in sojan ya amsa kiran gaggawa daga sojojin da aka kai wa hari a wani sansanin sojoji na ‘Forward Operating Base’ (FOB), da ke da alaƙa da bataliya ta 242.

  • Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027
  • Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

A cewar majiyoyin, motarsa ta afka cikin bam ɗin ne a lokacin da yake gaggawar taimaka wa sansanin sojoji na FOB, bayan da wasu da ake zargin ƴan ta’adda ne suka ƙaddamar da farmakin haɗin gwiwa a daren Lahadi.

ADVERTISEMENT

Daily trust ta ruwaito cewa, lamarin ya faru ne kwana uku kacal bayan da wani Kwamandan runduna ta 29, Birgediya Janar Oseini Braimah tare da wasu sojoji aƙalla 17 ake zargin ƴan ta’addan da kashe su, a yayin harin da rundunar ta kai a Benisheikh da ke Ƙaramar Hukumar Kaga ta Jihar Borno.

Jami’in yaɗa labarai na rundunar haɗin gwiwa ta Arewa maso Gabas, ‘Operation HADIN KAI’, Laftanar Kanar Sani Uba, ya tabbatar da faruwar harin, inda ya ce; lamarin ya faru ne a yammacin ranar 12 ga watan Afrilu, lokacin da dakarun sashen 3 na OPHK, suka kai wa wani harin ta’addancin Tango saniyar ware a cibiyar Charlie 13 a Monguno.

LABARAI MASU NASABA

NDLEA Ta Cafke Ƴar Shekara 67 Da Hodar Iblis Da Aka Ɓoye A Cikin Ayaba

Gwamnatin Kaduna Ta Yaba Wa ONSA Kan Shirin Horon Masu Tsaron Daji ‘Forest Guards’

A cewarsa, bayan musayar wuta mai tsanani, sun fatattaki ƴan ta’addar tare da ci gaba da kula da wurin.

“Abin takaici, kwamandan rundunar, yayin da yake tafiya cikin ƙwarin gwiwa zuwa wurin da sojojin suke, domin tantance lamarin, ya ci karo da wata na’ura mai ɗauke da bama-bamai (IED), wacce ta yi wa motarsa mummunar illa, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa tare da wasu jami’an leƙen asiri guda shida.

Ya ce, ƙungiyar OPHK ta yi matuƙar alhinin rashin wannan babban jami’in da sauran jajirtattun ma’aikatan da suka sadaukar da rayuwarsu a hidimar ƙasa.

Sanarwar ta ƙara da cewa, ” sadaukarwar da suka yi za ta kasance abar tunawa da sojojin da kuma al’ummar da suka yi wa hidimar.”

Sani Anwar
+ postsBio
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Ko Kun San Amfanin Kwanciya Da Bangaren Hagu?
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    2027:Mata Shida Da Ke Takarar Neman Shugabancin Nijeriya
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Dambarwa A Kasuwancin Iyalan Indimi
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Illar Shan Taba Sigari Da Dangoginta

MASU ALAKA

Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Tsaro

NDLEA Ta Cafke Ƴar Shekara 67 Da Hodar Iblis Da Aka Ɓoye A Cikin Ayaba

July 11, 2026
Gwamnatin Kaduna Ta Yaba Wa ONSA Kan Shirin Horon Masu Tsaron Daji ‘Forest Guards’
Tsaro

Gwamnatin Kaduna Ta Yaba Wa ONSA Kan Shirin Horon Masu Tsaron Daji ‘Forest Guards’

July 9, 2026
Sojoji Sun Kama Mai Kai Wa Ƴan Ta’adda Kayan Aiki A Zamfara
Tsaro

Sojoji Sun Kama Mai Kai Wa Ƴan Ta’adda Kayan Aiki A Zamfara

June 25, 2026
Next Post
An Ƙirƙiro Da Shirin ‘Kano First’ Ne Don Sanya Wa Kanawa Kishin Jiharsu —Bala Gwagwarwa

An Ƙirƙiro Da Shirin 'Kano First' Ne Don Sanya Wa Kanawa Kishin Jiharsu —Bala Gwagwarwa

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.