ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 25, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Dauda Lawal Ya Dukufa Wajen Farfado Da Darajar Jihar Zamfara

by Rabi'u Ali Indabawa and Sulaiman
6 months ago
Zamfara

Kafin Gwamna Dauda Lawal ya hau karagar mulki a matsayin Gwamnan Jihar Zamfara, jihar ta kasance tana tangal-tangal a kusan kowane ma’aunin ci gaba.

A hakikanin gaskiya, a farkon shekarar 2023, Jami’ar Radboud da ke Nijmegen tare da hadin gwiwar Shirin Ci Gaban Majalisar Dinkin Duniya (UNDP) sun fitar da bayanai da suka nuna cewa jihar ta samu maki 0.403, inda ta zo ta 34 cikin jihohi 36 na Nijeriya a Ma’aunin Ci gaban Dan’Adam (HDI). Halin kudaden jihar ke ciki ma ya fi muni, domin ta zo ta karshe a Nijeriya. Don a sauya wannan mummunan yanayi, al’ummar jihar suka dora makomarsu a hannun Lawal ta hanyar kada masa kuri’a da rinjaye sosai.

  • Yawan Fasinjojin Da Jiragen Kasa Suka Yi Jigilarsu a Kasar Sin Ya Zarce Biliyan 4.5 A Shekarar 2025
  • Ko Me Matakin Amurka Na Tusa Keyar Shugaban Venezuela Ka Iya Haifarwa?

Fiye da shekaru biyu bayan haka, ana cika bukatunsu yadda ya kamata, har ma a wasu lokuta an wuce yadda aka nema. Bisa ga gagaruman nasarorin da ya samu, a yanzu mutane na alfahari suna cewa jihar da a da aka fi saninta da rashin tsaro da koma-bayan ci gaba, tana tasowa daga cikin toka kamar tsuntsun phoenid. Kuma, kamar yadda gogaggun ‘yan banki ke da dabi’a, yana da irin basirar Midas wadda ke juyar da al’amuran Zamfara zuwa alheri da kowanne tsari na dabara da ya dauka. Cikin kwarewa da salo, da sabuwar farfadowa, yana fuskantar manyan kalubalen jihar tare da bude manyan damammaki da a baya ba a iya ganinsu ba.

ADVERTISEMENT

Lokacin da ya karbi ragamar mulki, rashin tsaro ya mamaye kusan kowane lungu na jihar, lamarin da ya gurgunta tattalin arzikinta. Ilimi ya rushe, yayin da kiwon lafiya ya zama kamar tatsuniya ga mutane da dama. Sai dai sabon gwamnan bai yi kasa a gwiwa ba. Da hangen nesa mai kyau da jajircewa mai karfi, ya kaddamar da shirinsa na “Rescue Agenda” (Ajandar Ceto), inda ya ba da fifiko ga tsaro, ilimi, kiwon lafiya, ababen more rayuwa, da farfado da tattalin arziki.

Sakamakon ya zama abin al’ajabi matuka.

LABARAI MASU NASABA

An Nemi Shugabanni Su Rungumi Tafarkin Adalci A Tsakanin Al’ummunsu

Ƴan Bindiga Sun Tilasta Wa Ƙauyukan Sakkwato Biyan Sabon Haraji

Kafa Rundunar Kare Al’umma ta rage ayyukan ‘yan bindiga matuka, inda aka dawo da zaman lafiya a al’umma tare da farfado da tattalin arziki.

Fannin ilimi kuma na samun kulawar da ake bukata, ta hanyar shirye-shiryen tallafin karatu, biyan kudin jarrabawa, da daukar sabbin malamai, tare da horar da su bisa ka’idojin ilimi na zamani da ake amfani da su a duniya.

Gwamnatin jihar ta kuma zuba jari sosai a fannin ababen more rayuwa, inda ta gina sabbin makarantu, ta gyara tsofaffi, tare da samar da muhimman kayan aiki kamar littattafai da kayan aikin dijital.

Fannin kiwon lafiya ma yana samun gagarumar kulawa da ya dade yana nema, domin ana ci gaba da gyaran asibitoci da kuma shirye-shiryen bayar da magani kyauta ga al’umma. Haka kuma, gwamnatin jihar ta bullo da sabbin tsare-tsaren kiwon lafiya na zamani, kamar asibitocin tafi-da-gidanka da shirye-shiryen inshorar lafiya, domin kara saukaka samun ingantaccen kiwon lafiya ga dukkan ‘yan kasa.

Ci gaban ababen more rayuwa na sauya fasalin jihar baki daya. Ana gina sabbin hanyoyi, samar da ruwan sha na inganta, kuma na sabunta birane na kirkiri wurare masu kayatarwa. Babban birnin jihar, Gusau, na samun sabon yanayi, inda ake gina sabbin tituna, sanya fitilun kan titi, da samar da muhimman kayayyakin more rayuwa na jama’a.

Shirye-shiryen karfafa tattalin arziki, kamar bayar da tallafin kudi ga mata da tsare-tsaren samar da ayyukan yi, na kara habaka ci gaba tare da rage talauci.

Jagorancin Gwamna Lawal mai karfi ya sanya sabuwar rayuwa a Zamfara. Jihar na barin baya mai cike da rikice-rikice, tana fitowa a matsayin alamar fata da ci gaba.

Abin kuma da ya dace a lura da shi shi ne shirin samar da ci gaban shekaru 10 da gwamnan ya kaddamar kwanan nan. Wannan shiri cikakkiyar taswira ce da aka tsara domin sauya tattalin arzikin jihar tare da inganta rayuwar al’ummarta.

An gina shirin ne bisa ginshikai guda shida: Tattalin Arziki, Ababen More Rayuwa, Walwalar Jama’a, Ci gaban Dan’Adam, Mulki, da Dorewar Muhalli.

Shirin ya mayar da hankali kan cin gajiyar karfin Zamfara a fannin noma da albarkatun kasa ta hanyar hadin gwiwa da hukumomi kamar Ma’aikatar Kudi (MoFI) da Bankin Raya Afirka.

Manufar hakan ita ce habaka noma na zamani, sarrafa amfanin gona, da gina darajar kayayyaki, wanda zai samar da ayyukan yi, inganta wadatar abinci, bude kasuwanni, tare da rage rashin tsaro da ke da nasaba da talauci.

Wannan shirin ci gaban shi ne na farko irinsa a tarihin Zamfara na baya-bayan nan, cikakken shiri na dogon lokaci da aka gina bisa ingantattun bayanai, shigar dukkan masu ruwa da tsaki, da kuma daidaituwa da tsare-tsaren ci gaba na kasa da na duniya, ciki har da Manufofin Ci gaba Mai Dorewa (SDGs), Shirin Ci gaban Kasa na Nijeriya zuwa 2050, da Ajandar Tarayyar Afirka ta 2063.

Shirin ya fayyace fifikon kowane bangare, sakamakon da za a iya auna su, da kuma tsarin sa ido da tantancewa da ke tabbatar da gaskiya da rikon amana a kowane mataki na aiwatarwa.

Gwamna Lawal na da hangen nesa na ganin Zamfara ta zama abin koyi wajen bunkasar tattalin arziki mai sauyi, ba a Nijeriya kawai ba, har ma a fadin Afirka.

Yayin da Zamfara ke ci gaba da tasowa, al’ummar jihar suna fara girbar amfanin kyakkyawan mulki da nagartaccen shugaba. Ci gaban tattalin arzikin jihar na jawo hankalin masu zuba jari, yana samar da ayyukan yi tare da inganta rayuwar jama’a. Mutane na da kyakkyawan fata game da makomarsu, kuma amincewarsu ga gwamnati na kara karfi.

A karkashin jagorancin Gwamna Lawal, Zamfara na kan hanyar zama abin koyi wajen ci gaba a Nijeriya, tana nuna cewa da hangen nesa, jajircewa, da manufofin da suka mayar da hankali kan jama’a, ko da mafi wahalar yanayi za a iya sauya su.

Hanyar gaba tana da tsawo, amma gwamnatin Gwamna Lawal ba ta nuna gajiya ba. Suna aiki dare da rana domin gina kyakkyawar makoma ga dukkan ‘yan Zamfara, tare da tabbatar da cewa an yi amfani da dimbin albarkatun jihar domin amfanin kowa da kowa. Yayin da al’ummar Zamfara ke duban gaba, zuciyoyinsu sun cika da fata da kwarin gwiwa, suna sane da cewa gwamnan su ya kuduri aniyar samar da haske da kyakkyawar gobe.

Zamfara
Rabi'u Ali Indabawa
+ posts Bio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Nijar Ta Rattaba Hannu A Kan Dokar Haramta Auren Jinsi
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Za Mu Iya Sayar Da Manmu Ba Tare Da Wata Matsala Ba -Iran
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Dattawan Arewa Sun Buƙaci Tinubu Ya Ayyana Dokar Ta-baci Kan Tabarbarewar Tsaro
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Nijeriya Ta Karbi Ƴan Nijeriya 268 Da Suka Tsero Daga Afirka Ta Kudu
Zamfara
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace
  • Sulaiman
    ’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin
  • Sulaiman
    Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi
  • Sulaiman
    Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

MASU ALAKA

Nijeriya
Rahotonni

An Nemi Shugabanni Su Rungumi Tafarkin Adalci A Tsakanin Al’ummunsu

June 20, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Gidaje 14,940 A Sokoto
Rahotonni

Ƴan Bindiga Sun Tilasta Wa Ƙauyukan Sakkwato Biyan Sabon Haraji

June 20, 2026
IMF
Rahotonni

Tattalin Arziƙin Ƙasa: Masana Sun Buƙaci Tinubu Ya Yi Hattara Da Shawarar IMF

June 20, 2026
Next Post
An Gudanar Da Taron Shawarwari Kan Manyan Tsare-Tsare Tsakanin Sin Da AU

An Gudanar Da Taron Shawarwari Kan Manyan Tsare-Tsare Tsakanin Sin Da AU

LABARAI MASU NASABA

Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace

Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace

June 24, 2026
’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin

’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin

June 24, 2026
Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

June 24, 2026
Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

June 24, 2026
Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi

Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi

June 24, 2026
Kasar Sin Na Kara Zama Babban Ginshikin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya Na Gaba

Kasar Sin Na Kara Zama Babban Ginshikin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya Na Gaba

June 24, 2026
Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma

Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma

June 24, 2026
Sabbin Ministoci

Kafa ‘Yansandan Jihohi: Majalisa Ta Amince Da Tsarin ‘Yar Tinƙe Wajen Kaɗa Ƙuri’a 

June 24, 2026
Sin Ta Gabatar Da Tsarin Karfafa Kwarin Gwiwar Kamfanoni Masu Jarin Waje

Sin Ta Gabatar Da Tsarin Karfafa Kwarin Gwiwar Kamfanoni Masu Jarin Waje

June 24, 2026
Shugaban Kasar Burundi: Dangantakar Afirka Da Sin Misali Ce Ta Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa

Shugaban Kasar Burundi: Dangantakar Afirka Da Sin Misali Ce Ta Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa

June 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.