ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Illolin Yakin Gabas Ta Tsakiya Za Su Shafi Nijeriya

by Leadership Hausa
6 months ago
Nijeriya

Kazamin yakin da ake ci gaba da gabzawa a Gabas ta Tsakiya, na ci gaba da haifar da damuwa a fadin duniya, musamman duba da yadda aka fara ganin ilolinsa, na shafar wasu kasashen duniya.

Kafin a fara gaba yakin, misali a Nijeriya, ana sayar da Man Fetur lita daya a tsakanin Naira 839 zuwa lita daya kan Naira 875, am bayan fara yakin, yanzu ana sayar da lita daya daga tsakanin Naira 937 zuwa Naira 975.

  • Kasar Sin: Kashe Shugabanni Da Hare-Hare Kan Fararen Hula A Iran Abu Ne Da Ba Za A Lamunta Ba
  • Rawar Da Sashen Ayyukan Hidimomi Da Biyan Bukatu Ke Kara Takawa A Kasar Sin 

Za a iya alakanta hakan ne, kan yadda farashin danyen Mai a duniya ke kara saurin tashi, miaamman Ganga daya ta kai dala 80.

ADVERTISEMENT

Masu fashin baki a fannin sun yi hasashen cewa, matukar yakin ya di gaba da gudana, ba makawa, farashin Man kan lita daya, zai iya kaiwa Naira 1,000.

Nijeriya dai, ba ta da alaka, da wannan yakin amma, duba da yadd yakin zai iya shafar yadda ake safarar danyen Man na kasar nan zuwa kasuwar duniya, shi ne, babban batun, musamman duba da yadda a yanzu, rikicin ya shafi mashigar gudanar da hada-hadar kasuwanci ta Hormuz.

LABARAI MASU NASABA

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

Bugu da kari, wannan mashigar ta Hormuz, a kullim, akalla ana amfani da ita, wajen safarar Gangunan Danyen Mai miliyan 20, inda wannan adadin ya kai kaso 20, na Danyen Man da ake amfani da shi, a fadin duniya.

Kazalika, masu fashin baki a kamfanonin Goldman Sachs da Barclays, sun yi gargadi cewa, matukar aka ci gaba da yakin, farashin Danyen Mai samfarin Brent, duk Gang a daya, zai iya kai wa dala 100.

A nan, kan wannan batun, ra’ayin wannan Jaridar shi ne, ya zama wajibi ‘yan Nijeriya su fara daura damarar fuskantar matsin tattalin arziki da yakin zai iya jefa su ciki.

Kazalika, wannan dai, ba lokaci ne na batun siyasa da zahirin abinda ke a bayyana ba, amma kamata ya yi, Gwamnatin Tarayya, musamman ta fara daukar matakai da za su samarwa da ‘yan kasar, musamman talakawa, sauki, saboda yadda illolin yakin zai shafi rayuwarsu.

A irin halin da ake ciki a yanzu na yadda farashin Man Fetur a kasar ke tafiya kusan kafada da kafa da farashin shirytakaici, inda kuma a gefe daya, ya zama wajibi, Gwamnatin ta lalubo da mafita, na magance matsalolin rashin tsaro a kasar.

Sai dai, a nan muna maraba kan umartar rudunonin ‘yansanda da ke a daukacin fadin kasar da Babban Sifeta Janar na ‘Yansanda Olatunji Disu ya yi na su tabbatar da sun kara tsarara tsaro.

Kazalika, a ra’ayin wannan Jaridar, a kasar nan an shafe shekaru ana kirkiro da kyawawan tsare-tsare da kuma shirye-shiye masu kyau amma abin takaici a karshe sai a gaza wanzar da su yadda ya kamata.

Wannan dai, shi ne akasarin kalubalen da harkar gudanar da shugabanci, da kasar ke ci gaba da fuskanta.

Duba da yadda lamarin ke tafiya a yanzu, ba kamata a yi wani sako-sako na daukar matakai da suka da ce, kan wannan matsalar ta rashin tsaro a kasar, musamman duba da cewa, rikicin na Gabas ta Tsakiya na iya, zai iya shafar tattalin arzikin kasar.

Muna shawarar ‘yan siyasar kasar cewa, kar su kuskura su siyasantar da batun da ke a was, a yanzu a kasar.

Wannan Jaridar na ganin wasu na son yin amfani da wata manufar su ta siyasa domin su cimma wani burin na kashin kansu, musamman duba da irin kalubalen na rashin tsaro a kasar.

Bugu da kari, y zama wajibi, a bangaren kafafen yada labarai da ke a kasar nan su bayar da ta su gudunmawar ta hanyar yada labarai kan yadda za a dakile yuwuwar illolin da yakin na Gabas ta Tsakiya, zai iya ahafar kasar nan da kuma shafar rayuwar’yan kasar.

A kan yadda zahirin abin ya ke a yanzu, mun zayyano manyan batutuwan da a wannan sharhin na Teburin Edita, muka iya gani, musamman domin mu  ankarar da Gwamnatin Tarayya da sauran masu ruwa da tsaki domin su san matakan da ya kamata su daika, domin a kaucewa fadawa cikin wata gagarumar matsala a kasar nan, kan wannan batun na yakin na Gabas ta Tsakiya.

Nijeriya
Leadership Hausa
Website |  + postsBio
  • Leadership Hausa
    Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja
  • Leadership Hausa
    Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed
  • Leadership Hausa
    Batun Dawo Da Tallafin Mai Da Atiku Ya Yi Na Ci Gaba Da Tayar Da Kura
  • Leadership Hausa
    Batun Guguwar Kakar Yakin Neman Zabukan 2027 A Nijeriya

MASU ALAKA

Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi
Manyan Labarai

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

September 8, 2026
Next Post
Karamar Sallah: Sallar Idi A Wajen Musulmi…

Karamar Sallah: Sallar Idi A Wajen Musulmi…

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.