ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 4, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Jiragen Iran Marasa Matuka Suka Sauya Yadda Ake Yaki A Duniya

by Rabi'u Ali Indabawa
1 month ago
A RAF Reaper UAV (Unmanned Aerial Vehicle) is pictured airborne over Afghanistan during Operation Herrick.

It is armed with a full complement of two GBU-12 226kg (500lb) laser-guided bombs and four Lockheed Martin AGM-114P Hellfire air-to-surface missiles.

The MQ-9 Reaper is a medium-to-high altitude, long endurance remotely piloted aircraft system. The MQ-9's primary mission is to act as an intelligence, surveillance and reconnaissance (ISR) asset, employing sensors to provide real-time data to commanders and intelligence specialists at all levels.

A RAF Reaper UAV (Unmanned Aerial Vehicle) is pictured airborne over Afghanistan during Operation Herrick. It is armed with a full complement of two GBU-12 226kg (500lb) laser-guided bombs and four Lockheed Martin AGM-114P Hellfire air-to-surface missiles. The MQ-9 Reaper is a medium-to-high altitude, long endurance remotely piloted aircraft system. The MQ-9's primary mission is to act as an intelligence, surveillance and reconnaissance (ISR) asset, employing sensors to provide real-time data to commanders and intelligence specialists at all levels.

Yayin da ake tsaka da yakin hadin gwiwa tsakanin Amurka da Isra’ila da kuma Iran, kwararren nan kan harkokin soji Akram Kharif ya wallafa wani littafi da aka yi wa suna “In the Shadow of Witness.”

A cikin littafin, ya bayyana tsari da kuma ci gaban da aka samu a fanni kera jirage mara matuka a masana’antar kere-kere da Iran, da kuma bayani kan hanyoyin da Iran ta bi ta zama daya daga cikn manyan masu karfin soji a duniya dun da takunkumin da Amurka ta sa mata.

An sanya bayanan jirage marasa matuka na Iran a rahoton yakin da ake yi na kan iyaka tsakanin Hezbollah da ke Lebanon da Isra’ila. Bayan an sami wasu baraguzan jiragen an yi nazari mai karfi a kansu, an gano akwai alaka tsakanin wadanda Houthi suke amfani da su a Yemen da wanda ake samarwa a Iran.

ADVERTISEMENT

A watan Satumbar 2022, duniya ta kadu da jin labarin cewa Iran ce ke bai wa Rasha jiragen soji maras matuka. Wannan ya biyo hoton jirage biyu da aka gani kirar (Shahed 136) suna shawagi a shararin samaniyar Keib babban birnin Ukraine.

Ta yaya kasar da aka sa mata takunkumi na sama da shekara 40 ta iya sauya fasalin girmanta a idanun duniya? mene ne ya ta samar kai wa ga wannan nasarar.

LABARAI MASU NASABA

Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili

Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

Takunkumin da aka sawa Iran a 1979 ya tilasta shugabannin Iran su nemo hanyoyin da za su iya magance matsalolinsu da kansu domin karya alkadarinsu. Wannan yanayi ya sanya su dogaro kan harkokin kere-kere, maimakon dogaro da masu kai musu dauki. Sakamakon takunkumin, Iran ta kirkiri wani kawance da kasashen waje domin biyan bukatarta.

Ta dogara ne kan abubuwan fasahar da take da shi na cikin gida ta yi hakuri da rashin wasu kayayyakin aikin zannan ta nuna juriya da jajurcewa.

Yayin da Mohammad Reza Pahlabi Shah na Iran ya bar kasar a Janairun 1979, ya barta a matsayin mafi karfin soji a yankin. Itama rundunar sojin saman Iran na da jirage kirare F-14 Tomcats, F-4 Phantoms, and F-5 Tigers.

A wannan lokacin sojin Iran na matsayi na biyar a duniya ta bangaren kayan aiki, bayan sojojin Amurka da Tarayyar Sobiyat da Burtaniya da kuma Faransa. A wannan lokaci ana ganin sojin Iran sun fi karfin na Jamus da China da abokiyar hamayyarta Isra’ila, tun da tana da jirgin F-14 Tomcat na yaki, wanda shi ne mafi makurar jirgin yaki a duniya a lokacin.

Amma kula da jiragen ya ta’allaka ne da yawan injiniyoyin Amurka da masana fasaha da ke Iran, sa’annan kayan gyaransa a Amurka ake samunsu a kamfanin Grumman. Saboda wadannan dalilai jiragen sun dogara ne kacokan kan Amurka domin tafiyar da su.

Bayan faduwan garkuwa Shah, mafi yawan kwamandojin Iran ko dai sun gudu sun bar kasar ko kuma an kashe su ko kuma an daure su a gidajen yari. Sai injiniyoyin Amurka da masana fasaharsu suka bar Iran, kuma kamfanonin Amurkan suka warware alkarsu da sabuwar gwamnatin Iran.

Dole uwar na ki

A Satumbar 1980, dakarun Iraki suka afkawa Iran, fara yaki tsakanin kasashen biyu sai da ya kai shekara takwas ana yi. An yi amfani da munanan makamai wajen lalata abubuwa da kisa ciki har da amfani da makamai masu munanan sinadarai, kuma an kashe kimanin mutum miliyan daya a lokacin.

A farkon wannan yaki, dakarun Iraki sun fi dama a hannunsu saboda daukakarsu. Sojjin Iraki sun sayi wasu jirage daga Tarayyar Sobiyet kuma sun rika amfani da tauraron dan’Adam din Tarayyar wajen sanin inda makiyansu suke da kuma motsinsu.

Amma a bangaren Iran sojojinta na yaki ne cikin yanayi mara dadi kuma an hana su damar kai wa da kawowa da samun rahotannin leken asiri.

Don haka Iran na bukatar ci gaban fasaha domin rayuwa a tsakanin kasashen da suke yi mata barazana a kullum. Kuma takunkumin tattalin arziki da aka sa mata ya hana ta damar gyara kanta.

Don haka suka yi wa kansu alkawarin fara samar da abubuwan kirkire-kirkire a cikin gida, mai makon sayowa daga wasu wurare.

Tunanin cikin sauki: Idan ya zama ba za a iya tuka jiragen sama da za su iya nuna wuraren makiya ba da motsinsu, watakila wata karamar fasahar da za a iya iko da ita daga gida ta yi wannan aikin. Wannan fasahar na da sauki, tana da wuyar ganewa, sannan tana samar da bayanai masu amfani sosai.

Tun daga 1981, Iraniyawa suka fara tunani kan wannan na’urar da yadda za a sa masu kyamara mai daukar bayanai. An fara samar da wannan tunanin ne a jami’ar Isfahan kuma wasu daliban da ke karantar injiniya ne suka fara zuwa da ita suka aiwatar da ita a radin kansu. Sun fara samar da ainihin sangalalon abin kafin daga baya su bunkasa ta, sannan suka gabatar da ita ga shugabannin kasar.

Bayan shekarun gwaji, ana tsaka da gazawa, sai wasu matasa uku na jami’ar Isfahan suka hada na’urar suka gwada ta a jirgin kasar Khuzestan: a matukin jirgin farar hula da ake kira Farshid, da daliban fiziks da suka hada da Saeed da Masoud sune suka yi aikin.

Da aka kawo bayanan gwajin na’urar ga sojoji wasu ma izgili suka rika yi mata. Tafi kama da ‘yar tsanar wasan yara ko saboda an hada ta daga wani sinadari da ba a saba gani ba. Fankar da aka hada ta da ita, wadda aka hada da hannu ce, sannan tankin man an hada shi ne da irin ledar jakar asibiti da ake sa magunguna.

Jirgin soji maras matuki na farko

A shekarar 1983, jirgin da aka raina ya yi tafiyar kilomita 40 zuwa sansanin sojin Iraki inda ya duko hotunan da suka fita kal na wuraren da soji da kuma kai wa da kawowarsu. An rika bashi umarni ne daga Thunder Battalion daga nan kuma aka aura zimmar fara samar da jirage marasa matuki a hukumance.

An auke wannan shiri daga hannun wadannan dalibai zuwa hannun gwamnati. Domin samun abubuwan da ake bukata na dole wajen hada jirage marasa matuki, dole suka kaucewa wasu takunkumai suka shiga mu’amala da wasu kasashe domin samun wadannan abubuwa.

IRGC sun kirkiri wani kamfani a Dubai amma ta hannun wani kamfani daga Singapore ya rika saya musu kayan aiki daga gwammnan kasashe.

Haka aka rika kawo kayan zuwa jami’ar Isfahan ana hada su a nan. Wannan ya isa misali kan wata na’ura da aka cire a jikin Shahed 136 wanda aka harbo a Ukraine.

Jirage marasa matukan an rika amfanin da su a yakin da Iran ta yi da Iraki a 1983. Injiniyoyi a Bataliyar Raad suka fara tunanin samar da jirgin soji marar matuki a 1987. Jirgin da ya tashi ya dauki hotonan makiya da motsinsu, amma hakan na bukatar wasu ci gaban fasaha daga baya kuma Raad suka samar da wannan fasahar da aka yi wa suna “Mohajir”.

A shekarar 1988, Iran na cikin kasashen da suka fara amfani da “jirgin soji maras matuki” (UCAB), abin da ake kira Drone a yau. Amurka da Turkiyya da Isra’ila sun yi fice wajen samar da irin wadannan jirage, amma dai Iran ita ce kan gaba wajen samar da su.

Jiragen sojin Iran na da muhimmanci sosai kuma an kirkire su ne a 1988, kuma ba sa wuce tazarar kilomita 50. Amma a 2026, Jiragen Iran da aka inganta sukan haura saman kasashe da dama su kai hari cikin Isra’ila inda nan aka nufa, kuma tun daga cikin Iran din.

A takaice Isra’ila ce ta fara amfani da jiragen da ake kira Drones da zummar hare-haren soja, tun kan Amurka ta fara. Ta fara amfani da su a 1973 lokacin yakinta da Masar.

A shakarar 1982 lokacin da suka mamaye Lebanon, Isra’ila ta yi amfani da nau’in Scott da Mustif domin kai hari kan inda makaman masu linzamin Syria suke a Bekka Balley. Wannan ne karon farko da aka yi amfani da jirage marasa matuki a rikicin soji.

Samar da jirgi maras matuki daya yana cin dalar Amurka 20,000, amma hakan Iran ta rika harba jiragen sama da 100 afarkon rikicin.

Ba a yi jirage marasa matuki ba da karfi, amma an tsara shi da sauri rashin nauyi da zafin kai hari. Dan haka harin jiragen suna tsayi sosai, kuma makamai masu linzafi suna fin jiragen tsada wajen hadawa da kashi 10 zuwa 20.

Harin da aka kai wa kamfanin mai na Saudiyya Aramco a 2019, ya nuna fitinar da ke tattare da sabon jirgi mara matuki da irin su Iran ke da shi, tun da tsarin kariyar samaniya na Amurka ma ba ya iya hana jiragen da aka hada a Iran. Duk da cewa dai HOuthi ne suka yi ikirarin kai harin, amma dai abin dubawa shi ne jiragen an harba su ne daga Iran ko Iraki.

Barnar da harin ya janyo ta lakumi biliyoyin Dala, yayin da kudin da aka kashe aka kai harin bai fi miliyoyin dala ba. Wannan kuma ya isa ya gwada wanda ya yi nasara da wanda ya fadi a yakin da ake yi na jirage marasa matuka a duniya a yanzu.

Jiragen
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    NSCDC Ta Cafke Mutum 10 Da Ake Zargi Da Satar Kayan Gwamnati Da Kuma Fashi A Kano
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƴansanda Su Ƙi Karɓar Cin Hancin Naira Miliyan 500 Daga Hannun Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙasashen DR Congo Uganda Da Sudan Sun Haɗa Kai Domin Yaƙar Ibola
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Zafin Rana Ya Yi Ajalin Mutum 16 A Indiya

MASU ALAKA

Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili
Manyan Labarai

Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili

June 4, 2026
Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro
Manyan Labarai

Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

June 3, 2026
Gwamnatin Zamfara Ta Shirya Tallafa Wa Mata Da Masu Ƙaramin Ƙarfi Fiye Da Miliyan Ɗaya
Manyan Labarai

Gwamnatin Zamfara Ta Shirya Tallafa Wa Mata Da Masu Ƙaramin Ƙarfi Fiye Da Miliyan Ɗaya

June 3, 2026
Next Post
Gombe 2027: Pantami Ya Dakatar da Hadiminsa Kan Wani Rubutu a Facebook

Gombe 2027: Pantami Ya Dakatar da Hadiminsa Kan Wani Rubutu a Facebook

Discussion about this post

LABARAI MASU NASABA

Atiku Ne Ya Fi Dacewa Da Tikitin Takara A ADC Amma Ya Kamata Ya Janye — Baba-Ahmed

2027: Kasancewa Ɗan Arewa Kaɗai Ba Zai Tabbatar Da Samun Ƙuri’u Ba – Baba-Ahmed

June 4, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Ofishin NAGGW Zuwa Kano Domin Yaƙi Da Hamada

Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Ofishin NAGGW Zuwa Kano Domin Yaƙi Da Hamada

June 4, 2026
Mambobin NYSC 4, Soja da Mutum 1 Sun Rasu A Hatsarin Mota A Adamawa

Mambobin NYSC 4, Soja da Mutum 1 Sun Rasu A Hatsarin Mota A Adamawa

June 4, 2026
Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili

Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili

June 4, 2026
Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

June 3, 2026
Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

June 3, 2026
Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

June 3, 2026
Majalisa Ta Nemi Tinubu Ya Canza Dabarun Yaƙi Da Ta’addanci Don Kawo Ƙarshen Kashe-kashe

’Yan Majalisar Tarayya 3 Sun Fice Daga APC Zuwa ADC da PRP

June 3, 2026
An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos

An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos

June 3, 2026
Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

June 3, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.