ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 25, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Neman Kudi Ido Rufe Ya Shafi Al’ummar Wannan Zamanin

by Sulaiman and Sani Anwar
2 months ago
Neman kudi

Al’ummar wannan zamani, ta tsinci kanta a wani mawuyacin hali na tsantsar son duniya da bauta wa kudi, wanda hakan ya jefa ta cikin halin kaka-na-ka-yi ta fuskoki daban-daban da suka hada da rashin gaskiya, cin amana, zamba cikin aminci, ha’inci, aikata muggan laifuka da sauran makamantansu.

Idan aka yi wa al’ummar kallo na tsanaki, babu abin da yake wahalar da ita tamkar rashin wadatar zuci da gaggawa da hassada da kuma son kece raini. Ba ki da gashin wacce, amma kina son kitson wacce, wannan shi ne babban abin da yake ta faman wahalar da al’ummar.

Zamantakewa

ADVERTISEMENT

Son duniya da bautar kudi, sun lalata zamantakewar al’ummar wannan zamani kwata-kwata. A da, an fi kulla alaka bisa mutuntaka da girmama juna, amma yanzu al’ummar ta fi raja’a a kan abin duniya, iya kudinka, iya mutuncinka. Babu wani abu da ake kokarin yi tsakani da Allah, mutane sun dimauce, sun fita daga hayyacinsu, rayuwa ta koma ta-kai-ta-kai.

Wadannan dalilai ne suka sanya zumunci ya yi karanci, aka kuma yi wasarairai da hakki a tsakanin makwabta, babu wani da yake girmama wani tsakani da Allah, sai don abin duniya ko wani abu makamancinsa. Shi yasa wahalhalu suka yi yawa, abubuwa suka tabarbare, aka kasa samun bakin tsaren.

LABARAI MASU NASABA

Zargin Ɓata Suna: Kwankwaso Ya Yi Barazanar Neman Diyyar Naira Biliyan 10 Kan Wani Malamin Coci

Atiku Ya Soki Tsare El-Rufai, Ya Ce Sharuɗan Belinsa Sun Yi Tsauri

Kasuwanci

Shubuha da haramci da algus da cin amana da gaggawa su ne suka dabaibaye kasuwanni da kasuwancinmu a wannan lokaci. Yanzu haka, babu ruwan ‘yan kasuwarmu da riba ko haramci a harkokin kasuwancinsu, in dai har za a samu kudi, to komai ma ta-fanjama-fanjan.

Amana ta yi karanci a tsakanin su kansu ‘yan kasuwar, domin kuwa a baya, dan kasuwa yana iya bai wa dan’uwansa dan kasuwa kaya, babu ko sisin kwabo, bayan ya sayar ya cire ribarsa ya dawo masa da kudinsa, amma yanzu abubuwan sun canza, saboda rashin amana a tsakaninsu.

Har ila yau, ‘yan kasuwa da dama na kokawa a kan yaransu na shago, wadanda suke taya su wajen gudanar da kasuwancin nasu. Mafi yawan lokaci, wadannan yaran shago, saboda gaggawa da kokarin ganin sun tara kudi a cikin dan kankanin lokaci, ba sa iya tsayawa su bi a hankali wajen koyon kasuwancin, domin cin ribarsa.

Akwai yaron shagon da ya rika dibar kudin shagon maigidansa, yana kai wa wani malami, wai ya yi masa addu’a ya fi maigidan nasa kudi, saboda gaggawa da kawazuci. Irin haka, na faruwa kwarai da gaske, maimakon yaro ya tsaya ya mayar da hankali a kan yadda zai fahimci kasuwanci, sai buge da neman hanyar da zai bi ya sha gaban uban gidansa a dare daya, ba tare da lissafin cewa; uban gidan nasa shi ma ba dare daya ya zama abin da ya zama ba.

A harkar kasuwanci, kusan kowa so yake ya shiga gaban kowa, burin maigida ya bautar da yaransa, ta hanyar gallaza musu da bautar da su, kullum sai dai su yi ta tara masa kudi. Haka nan, su ma yaran, ba su da burin da ya wuce ganin suna cutar da maigidan nasu, ta hanyar yi masa sata da zamba cikin aminci, ma’ana dai, kowa na neman sa’a a kan kowa. 

Ma’aikatan Gwamnati

Gurbacewar zamani, ta sa ma’aikatan gwamnati ba su da gaskiya da amana kwata-kwata. Sata da cuta da zamba da cin hanci da rashawa, sun dabaibaye aikin baki-daya, rashawa ta zama tamkar wani ado a aikin na gwamnati. Kowa dama yake nema, so yake a kai shi wajen da zai yi cuwa-cuwa, yana zare ido yana hura hanci.

An daina tsoron haramun kwata-kwata, yanzu ta kai ga neman ta ake yi ido rufe. Babu kunya, babu tsoron Allah, babu tsoron abin da ka iya zuwa ya dawo. Har ila yau, yanzu har ta kai ga shi kansa aikin, saya ake yi. Haka nan, karin matsayi da tura ma’aikaci wuri mai gwabi-gwabi, shi ma duka saya ake yi a biya, duk da sunan neman kudi.

Wannan matsala ta neman kudi ko ta halin kaka, kullum sake mayar da wannan kasa baya take yi, babu yarda da amince a tsakanin masu mulki da talakawan da suke mulka. Haka zalika, babu wani abu da yake tafiya bisa doron gaskiya da cancanta, domin kuwa an siyasantar da komai.

Babban abin takaici shi ne, yadda sannu a hankali wannan matsala ta samu kutsawa tare da dabaibaye manyan makarantun gwamnati. A da, ko dan wane ne kai, ba za ka samu gurbin shiga jami’a ba, har sai ka cika dukkannin ka’idojin da ake bukata, amma yanzu abin haushi da takaici, gurbin shiga jami’ar ma sayen sa ake yi.

Malamai sun lalace da neman kudi, idan dalibi yana da kudi, ya je ya kwanta ya sha barcinsa. Komai ya zama kudi don masifa, shi ya sa abin yake kara zama abin tsoro, musamman ganin yadda wannan fannin na ilimi mai zurfi, shi ma ya shiga halin-ha’ula’i.

Haka nan, shi ma fannin lafiya, in dai aka ce asibiti na gwamnati ne, to sai dai idan ka san wani ko kuma kana da kudin da za ka ba da cin hanci, kafin likita ya saurare ka. Shi ya sa mutane suke mutuwa, saboda rashin bayar da kulawar da ta dace, musamman masu karamin karfi, wadanda ba za su iya bayar da na goro kafin a duba lafiyarsu ba.

Ita kuma gwamnati ta kawar da kai, kullum sai karairayi a gidajen yada labarai, amma kusan kamar ma ba su san halin da al’umma suke ciki ba. Domin kuwa a asibitocin, babu isassun likitoci, magunguna, gadajen kwanciya, na’urar kula da numfashi (odygen), wutar lantarki, ruwan sha da sauran amfani da sauran makamantansu.

Haka mutane suke shan bakar wahala, da almajiri da wanda ba almajiri ba, duk sun zama almajirai, saboda rashin tabbas na masu mulki. Kullum tunaninsu shi ne yadda za su samu kudi ko ta halin kaka, don biyan bukatunsu, ba yadda za su kyautata rayuwar al’ummar da suke mulka ba.

Gurbacewar Tarbiyyar Matasa

Tarbiyya ita ce ginshikin rayuwar dan’adam, da zarar an rasa ta, kusan za a iya cewa; an rasa komai na kyautatuwar wannan rayuwa, musamma ma ga matasanmu. Halin da aka tsinci kai yanzu, na neman kudi ko ta halin kaka, ya sake jefa matasa cikin mawuyacin hali.

Kowane matashi, so yake ya ga ya samu kudi da wuri-wuri, cikin sauki ba tare da ya sha wahala ba. Wannan dalili, ya sa matasanmu afkawa cikin mummunan hadari na aikata muggan laifuka da suka hada da kisan kai, garkuwa da mutane, zamba cikin aminci (419), fashi da makami, sace-sace da sauran makamantansu.

Kwanan nan, aka samu wani matashi ya hallaka mahaifiyarsa har lahira, saboda kudin gado a babban birnin tarayya Abuja. Haka nan, akwai wani matashi da ake zarge da kashe matarsa a Kano, a ‘yan kwanakin nan, domin ya ci gadon da mahaifinta da tsohon mijinta suka bar mata, kuma abin haushin ma shi ne, dududu auren bai wuce wata biyu ba.

Haka zalika, akwai matar da aka samu ta yi garkuwa da kanta, domin karbar kudin fansa daga wurin mijinta. Akwai kuma ‘ya’yan da ake samu su ma sun yi garkuwa da kawunansu, domin karbar kudin fansa daga wurin iyayensu. Abin ya zama tamkar wata almara.

Idan za a iya tunawa, a ‘yan watannin da suka gabata ne, wasu matasa a Kano, suka je har gida suka kashe mata da ‘ya’yanta, duk da sunan samun gado kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Bugu da kari, matasa maza da mata sun afka cikin aikata miyagun laifuka, domin kawai su samu kudi. Baya ga sace-sace da 419 da sauran makamantansu, ‘yan mata da zawarawa da dama sun zama muzinata, wasu kuma sun zama ‘yan Yahu-yahu, babu tsoro kwata-kwata a tare da su, in dai za su samu kudi, babu ruwan da abin da ka je ya zo.

Akwai wata yarinya a Kano, dududu shekarunta ba su haura ashirin da biyar ba, amma ana tuhumar ta da yin zamba cikin aminci na kimanin naira miliyan dari bakwai. Ta karbi kudade daga hannun mutane daban-daban da sunan kasuwanci, amma babu uwar kudin, babu kuma riba. Sannan, iyayenta suna nan a raye, amma saboda dan abin da take ba su, ya sa suka daure mata gindi ta yi ta cin karenta babu babbaka.

Kamar yadda labari ya iske mu, har aikin hajji yarinyar ta biya wa mahaifinta, amma fa duk da kudin mutane. Don haka, babu dalilin da zai sa a kwabe ta ko a bincika, domin jin abin da take ciki. Haka rayuwar ta zama, indai yara za su samu kudi, to fa babu ruwan iyaye da bincikar abin da suke ciki. Da wani a dangi zai zo ya yi magana, nan take iyeyen za su ce hassada ake yi wa ‘ya’yan nasu.

Akwai ‘yan mata da zawarawa da dama da ba sa kwana a gidajen iyayensu, amma tun da suna kawo kudin da za a yi cefane da sauran bukatu na yau da kullum, iyayen nasu ko kadan ba su damu ba.

Saboda haka, a nan ya zama wajibi, gwamnati, iyaye, malamai da sauran masu fada a ji, su jajirce tare da mikewa tsaye wajen gyara wadannan al’amura. Dole ne gwamnati, ta sauke nauyin da ke wuyanta, ta hanyar magance cin hanci da rashawa da kuma kyautata rayuwar al’umma. Haka zalika iyaye, su ma ya zama wajibi su sauke nauyin da Allah ya dora musu na kula da tarbiyyar ‘ya’yansu da sauran makamantansu.

Har ila yau, su ma malamai akwai nasu nauyin na fadakar da al’umma da ita kanta gwamnati, abin da Allah da Manzonsa suka ce, dangane da abubuwan da suka shafi rayuwa da zamantakewa a tsakanin al’umma. Kazalika, su ma sauran shugabannin al’umma, wajibi ne su fito su bayar da tasu gudunmawar, domin samun al’umma tagari.

A karshe kuma, ya kamata kowa ya sani cewa; arziki na Allah, shi ne yake azurtawa kuma shi ne mai talautawa. Duk abin da Allah ya kaddarawa bawansa samu, babu abin da zai hana shi samu, ba sai ya yi cuta ko aikata wani mummunan laifi ba. Bababn kiranmu ga matasa shi ne, su zama masu tsoron Allah da neman na kansu ta hanyar halak, ba ta hanyar haramun ba.

Neman kudi
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace
  • Sulaiman
    ’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin
  • Sulaiman
    Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi
  • Sulaiman
    Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”
Neman kudi
Sani Anwar
+ posts Bio
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Tattalin Arziƙin Ƙasa: Masana Sun Buƙaci Tinubu Ya Yi Hattara Da Shawarar IMF
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Cututtukan Da Aka Fi Fama Da Su Lokacin Damina Da Yadda Za A Kauce Musu (2)
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Cututtukan Da Aka Fi Fama Da Su Lokacin Damina Da Yadda Za A Kauce Musu (1)
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Talauci Ya Sake Karuwa Da Kashi 63 Duk Da Sauye-sauyen Tattalin Arzikin Da Gwamnati Ta Yi – IMF

MASU ALAKA

Yadda Na Sayar Da Kadarori Na Don Ɗaukar Nauyin Ɗalibai A Ƙasashen Waje – Kwankwaso
Manyan Labarai

Zargin Ɓata Suna: Kwankwaso Ya Yi Barazanar Neman Diyyar Naira Biliyan 10 Kan Wani Malamin Coci

June 24, 2026
Tinubu Ya Gaza Wajen Magance Matsalar Tsaro A Nijeriya — Atiku
Manyan Labarai

Atiku Ya Soki Tsare El-Rufai, Ya Ce Sharuɗan Belinsa Sun Yi Tsauri

June 24, 2026
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta
Manyan Labarai

’Yansanda Sun Kama Wani Mutum da Harsasai 174 A Nasarawa

June 24, 2026
Next Post
Shugaba Tinubu Ya Umarci A Samar Da Sabuwar Kwalejin ‘Yansanda A Kudancin Nijeriya

Shugaba Tinubu Ya Umarci A Samar Da Sabuwar Kwalejin ‘Yansanda A Kudancin Nijeriya

LABARAI MASU NASABA

Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace

Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace

June 24, 2026
’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin

’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin

June 24, 2026
Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

June 24, 2026
Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

June 24, 2026
Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi

Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi

June 24, 2026
Kasar Sin Na Kara Zama Babban Ginshikin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya Na Gaba

Kasar Sin Na Kara Zama Babban Ginshikin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya Na Gaba

June 24, 2026
Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma

Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma

June 24, 2026
Sabbin Ministoci

Kafa ‘Yansandan Jihohi: Majalisa Ta Amince Da Tsarin ‘Yar Tinƙe Wajen Kaɗa Ƙuri’a 

June 24, 2026
Sin Ta Gabatar Da Tsarin Karfafa Kwarin Gwiwar Kamfanoni Masu Jarin Waje

Sin Ta Gabatar Da Tsarin Karfafa Kwarin Gwiwar Kamfanoni Masu Jarin Waje

June 24, 2026
Shugaban Kasar Burundi: Dangantakar Afirka Da Sin Misali Ce Ta Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa

Shugaban Kasar Burundi: Dangantakar Afirka Da Sin Misali Ce Ta Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa

June 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.