Tsohon Ministan Sufuri kuma ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Rotimi Amaechi, ya yi zargin cewa tsauraran manufofin tattalin arziki na gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu sun taka rawa wajen mutuwar mahaifiyarsa, Mary Amaechi.
Amaechi ya bayyana hakan ne a yayin wata hira da aka yi da shi a shirin ‘Politics Today’ na gidan talabijin na Channels TV, inda ya bayyana cewa matsin tattalin arziƙi da hauhawar farashin magunguna sun sa ya zama da matuƙar wuya a ci gaba da sayen magungunan da mahaifiyarsa ke buƙata domin kula da lafiyarta.
Ya bayyana cewa kafin zuwan gwamnatin Tinubu a shekarar 2023, mahaifiyarsa tana cikin ƙoshin lafiya, amma sauye-sauyen tattalin arziƙi sun jefa iyalai da dama cikin ƙunci. Ya ce: “Manufofin gwamnati na kashe mutane. Na rasa mahaifiyata ne sakamakon waɗannan manufofi. Kafin Tinubu, mahaifiyata tana da ƙoshin lafiya, amma bayan zuwansa ya zama abu mai matuƙar wahala a iya sayen magungunanta.”
Haka kuma, tsohon gwamnan na Jihar Ribas ya kafa hujja da alƙaluman Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS), inda ya nuna cewa faɗuwar darajar Naira da dogaro da shigo da kayayyaki daga ƙasashen waje ciki har da kashe Naira biliyan 200 wajen shigo da magunguna ya sa harkokin kula da lafiya sun fi ƙarfin talaka.
Daga ƙarshe, Amaechi ya ƙalubalanci gwamnatin tarayya kan inda kuɗaɗen da aka tara bayan cire tallafin man fetur suka tafi, yana mai jaddada cewa manufar janye tallafin ita ce inganta rayuwar al’umma, amma har yanzu ƴan Nijeriya ba sa jin wani sauƙi a rayuwarsu ta yau da kullum.













