ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yaushe Za A Gane Kungiyar Da Za Ta Lashe Gasar Premier?

by Sulaiman and Abba Ibrahim Wada
4 months ago
Premier

Wasu mintuna 13 a wasan Everton da Manchester City na daren ranar Litinin, inda aka sharara kwallo 6, zai iya zama babbar zagon kasa da masu masaukin bakin suka yi a gasar Premier ta bana.

City, karkashin Guardiola ce ta shige gaba da kwallo daya kafin zuwa hutun rabin lokaci, sai dai daga baya Eberton sun haye sama, inda suka zura wa City kwallo daddaya har uku.

Duk da cewa Erling Haaland ya sake cin wata kwallon, sannan kuma Jeremy Doku ya sake mayar da ta uku, aka tashi 3-3, wannan y asa City ta rasa matayinta ga Arsenal, wadda a yanzu ta yi dare-dare saman teburi.

ADVERTISEMENT

Hakan ya sanya yanzu Arsenal ce ke da wuka da nama a kann wanda zai lashe kofin Premier na wannan shekara.

Dama an yi hasashen cewa wannan wasa zai iya zama mai wahala ga City, ganin cewa Eberton na fafutikar samun gurbin buga gasar Turai.

LABARAI MASU NASABA

Yaya Toure Na Dab Da Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

A karshen wasan, kocin City Pep Guardiola ya ce “gara canjaras da rashin nasara.”

”Yanzu kofin ba ya hannunmu, a baya yana hannunmu, amma yanzu ya kubuce. Muna da sauran wasanni a gaba, za mu ga yadda za ta kaya,” in ji Pep.

A yanzu Arsenal ta san cewa ita ce ke da kofi idan har ta lashe dukkanin wasanninta uku da suka rage, kuma idan ta yi nasarar hakan wannan zai zama karon farko da ta lashe kofin tun daga 2004.

Bayan yin canjaras da Eberton, yanzu mafi yawan jimillar maki da Manchester City za ta iya samu shi ne 83, inda ta lashe dukkanin wasannin gasar da suka rage mata.

Ita kuwa Arsenal a halin yanzu tana da maki 76, saboda haka idan kungiyar ta lashe dukkanin wasanninta na gasar za ta kare ne da maki 85, kuma hakan zai tabbatar musu da nasara lashe kofin Premier.

Haka nan yanzu Arsenal ce a gaba idan ana magana kan kwallye, inda take gaba da kwallo 4 a gaban City.

Amma akwai abin da zai faru a tabbatar wa Arsenal nasarar lashe gasar Premier tun daga ranar Laraba 13 ga watan Mayu.

Idan Arsenal ta yin nasara a kan West Ham a ranar Lahadi, ita kuma Manchester City ta yi rashin nasara a karawarta da Brentford a ranar Asabar, sannan City ta sake yin rashin nasara a hannun Crystal Palace a wasanta na gaba, Arsenal za ta lashe kofin Premier kafin wasanta biyu na karshe.

To amma idan dukkanin kungiyoyin biyu suka ci gaba da samun nasara a wasanninsu, ba za a san wanda zai lashe kofin ba har sai a ranar karshe ta gasar.

“Hakin da ake ciki Manchester City na cikin tsaka mai wuya, amma dole ne su natsu, su fuskanci abin da ke gabansu,” in ji tsohon dan wasan Blackpool Charlie Adam a tattaunawarsa da gidan rediyon BBC 5 Libe.

Amma kuma har yanzu akwai abubuwan mamaki da za su iya faruwa.

Premier
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
  • Sulaiman
    Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba
  • Sulaiman
    Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa
  • Sulaiman
    Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy
Premier
Abba Ibrahim Wada
Website |  + posts Bio
  • Abba Ibrahim Wada
    Yaushe Za A Fara Kofin Zakarun Turai
  • Abba Ibrahim Wada
    Messi Ya Yi Ritaya A Argentina: Da Me Za Mu Iya Tuna Gwarzon Duniyar?
  • Abba Ibrahim Wada
    Su Waye ‘Yan wasan Nijeriya Da Za Su Buga Gasar Firimiyar Ingila Ta Bana?
  • Abba Ibrahim Wada
    Chelsea A Ƙarƙashin Xavi Alonso

MASU ALAKA

Yaya Toure Na Dab Da Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai
Wasanni

Yaya Toure Na Dab Da Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai

September 9, 2026
Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana
Wasanni

Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana

September 8, 2026
Next Post
An Kama Bello Bodejo Bayan Ya Yi Wa Magoya Bayansa Jawabi A Taraba

An Kama Bello Bodejo Bayan Ya Yi Wa Magoya Bayansa Jawabi A Taraba

LABARAI MASU NASABA

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.