ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Zaben 2027: Akwai Bukatar A Yi Takatsantsan Domin Samun Cikakkiyar Nasara

by Leadership Hausa
5 months ago
Zabe

Alamu na nuna cewa, akwai matukar bukatar, a yi takatsantsan, duba da yadda wasu al’amura suka fara bayyana a yayin da zabukan 2027 ke kara kunnu kai.

Duk da cewa, batun yamutsa hazon siyasar kasar, ba su fara bayyana a zahirance ba, amma wasu ‘yan kasar sun fara bayyana fargabarsu, kan Kasancewar sahihancin hukumar zabe a matsayin ta na mai cin gashin kanta da kuma nauyin da ke a kanta, inda kuma a gefe daya, jami’iyyun kasar, ke ta faman kai komo, domin rike madafun iko.

Lamarin dai, ba wai batun kada kuri’a bane, amma za a gudanar da sahiahi kuma karbabben zabe da ya yi daidai da masu zaben suka zaba.

ADVERTISEMENT

Amma matukar aka saba hakan, zai janyo jefa rashin yarda da sakamakon zabukan  da haifar da rikici a cikin kasar.

Tuni dai, a kasar a ka fara ganin rikicin cikin gida a wasu jami’iyyun kasar, musamman na hakilon samun shugabantar jami’iyyunsu da kuma yadda sauya sheka, ya zama ruwan dare, a tsakanin jami’iyyun.

LABARAI MASU NASABA

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

Hakan ya sanya, jami’iyyun sun yi hannun Riga kan akidar da aka kafa su na tabbatar da ainahin kima da daraja da kuma ginshikin mulkin dimokiradiyya.

Nijeriya dai ta kasance an kafa ta ne, tun a jamhuriya ta farko a kan  turbar jami’iyyu da dama, amma kusan za a iya cewa, batun ya sauya ganin yadda kasar ke neman komawa, kan turbar jami’iyyar daya tilo.

Sai dai, an ruwaito shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, a kashin kansa, ya yi watsi da ikirarin cewa, gwamnatin sa, na kokarin yin uwa da makarbiya, na dora turbar siyayar kasar, a matakin mai bin tsarin siyasa daya tilo.

Duk da wannan watsin da Tinubu ya yi na ikirarin, amma jami’iyyun adamwar kasar, sin dage kai da fata, suna ci gaba sukar shugaban da kuma jami’iyyar sa ta APC, kan kokarin su na namaye daukacin fagen siyasar kasar, da kuma mayar da Nijeriya a tsarin kasa, mai bin jami’iyya daya.

Ko ma dai menene batun gaskiya kan wannan musayar yawun a tsakanin ‘yan adawar da kuma bayanin shugaban, amma babban abinda dubawar shi ne akwai bukatar a bayar da damar da za ta bai wa masu ruwa da tsaki kwarin guwair su ma a dama da su, domin a kawar da duk wani shakku a tafiyar da siyasar kasar.

Bugu da kari, a bangaren hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC tana ci gaba Kasancewa, a cikin tsaka mai wuya, musamman duba da cewa, kundin tsarin mulkin kasar, ya dora mata babban nauyin tabbatar da kare kimar tsarin gudanar da sahihi kuma amintacen  zaben da kowanne dan kasar, zai yi na’am da shi.

Hakazalika, hukumar ba wai nauyin sanya ido kan zabuka ne kawai, nauyin da ke a kanta ba, dole ne kuma ta tabbatar da ta yi adalci, a tsakanin sauran  jami’iyyun adawar kasar.

Kazalika, a gafe daya kuma batun kalubalen samar da kayan gudanar da zabe da matsalar  rashin tsaro lamuran nuna  bangaranci da batun addini, na daga cikin abubuwan da za su iya taka rawa, a zabukan na 2027.

A bangaren Shari”a kuwa, akwai gaganurmar gudunmawar da za ta taka, musamman wajen yanke hukunci, a cikin lokaci a kutunan da ke karbar korafin zabuka, musamman duba da yadda a wasu Shari’un baya, ake zargin kotun, da jan kafa, wajen yanke hukunci a kan lokaci da kuma yanke hukunci, na wasu shari’un zabukan da ke da matukar sarkakiya.

A saboda haka, ya zama wajibi a bangaren Shari’a, a tabbatar da an yi gaskiya wajen yanke hukunci, musamman domin alummar kasar, su ci gaba ganin kimar bangaren ba Shari’a da kuma aminta da bangaren.

Kazalika, suma masu ruwa da tsaki a fannin siyasar kasar, akwai rawar da za su iya takawa na kiyaye sharudda da ka’idojin zabe musamman wajen kaucewa yiwa juna habaici da furta kalaman da zai iya tayar da zaune tsaye, lokacin zabukan da kuma bayan sa.

A bangaren jami’iyyun kasar, suma ya zama wajibi, su tabbatar da suna gudanar da siyasar su ta cikin gida, a cikin yin da’a da gujewa aikata ayyukan da za su iya janyo yamutsa hazon siyasar kasar.

Ita kuwa hukumar zabe ta kasa INEC, ita na ya zama wajibi ta tabbatar da ta yi gaskiya wajen gudanar da ayyukan ta, musamman a bangaren yiwa ‘yan kasar da suka kai munzalin jefa kuri’a, domin su ma, a yi masu rijista da tattara sakamakon zabe tare da kuma yin amfani da fasahar kimiyyar zamani wajen gudanar da zabukan.

Hakazalika, a bangaren ‘yan kasar, suma akwai nauyi a kansu, wajen fitowa su kada kuri’unsu.

Har yanzu, lokaci bai kure wa Nijeriya ba, musamman, wajen karfafa ginshikin turbar dimokiradiyyar kasar, kafin zuwan lokacin gudanar da zabukan na 2027.

Zabe
Leadership Hausa
Website |  + postsBio
  • Leadership Hausa
    Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja
  • Leadership Hausa
    Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed
  • Leadership Hausa
    Batun Dawo Da Tallafin Mai Da Atiku Ya Yi Na Ci Gaba Da Tayar Da Kura
  • Leadership Hausa
    Batun Guguwar Kakar Yakin Neman Zabukan 2027 A Nijeriya

MASU ALAKA

Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi
Manyan Labarai

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

September 8, 2026
Next Post
Oyedele Ya Karɓi Ragamar Ministan Kuɗi Da Tattalin Arziƙi Daga Edun

Oyedele Ya Karɓi Ragamar Ministan Kuɗi Da Tattalin Arziƙi Daga Edun

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.