ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Zargin Barin Almakashin Tiyata Acikin Wata Mata Ya Yi Ajalin Mutuwarta A Kano

by Sulaiman
8 months ago
Kano

Wani dangi a Kano ya zargi Asibitin ‘Abubakar Imam Urology’ da sakaci bayan mutuwar wata matar aure a dangin mai suna Aishatu Umar, wacce ake zargin ta sha fama da matsanancin ciwon ciki na tsawon watanni bayan tiyatar da aka yi mata inda aka bar mata almakashi a cikin cikinta.

Wani ɗan uwanta, Abubakar Mohammed, ya bayyana hakan a wani rubutu da ya yi a shafukan sada zumunta inda ya ɗora hoton marigayiyar da kuma hoton na’urar haske da aka ɗauka wanda ya nuna almakashin da ake zargin an manta da shi a jikin matar bayan tiyatar.

ADVERTISEMENT
  • Tawagar Likitocin Sin Ta Kaddamar Da Horo Kan Tiyatar Zamani Ga Likitocin Ghana
  • Bayan Shawu Kan Zanga-zanga: Trump Ya Ƙaƙabawa Duk Ƙasar Da Ke Cinikayya Da Iran Haraji

Mohammed ya ce, Aishatu ta rasu da misalin karfe 1 na dare a ranar Litinin bayan ta sha fama da ciwon da ya daɗe yana damunta tun bayan tiyatar da aka yi mata a asibitin a watan Satumban 2025.

LABARAI MASU NASABA

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

A cewarsa, matar wacce ‘yar uwar matarsa ce, ta kamu ne da rashin lafiya a Kano, inda kuma aka kai ta cibiyar kula da cututtukan da suka shafi mafitsara don yi mata tiyata. Ya yi iƙirarin cewa, jim kaɗan bayan tiyatar, Aishatu Umar ta fara jin matsanancin ciwon ciki inda ta riƙa komawa asibitin akai-akai.

“Bayan tiyatar, ta sha fama da matsanancin ciwon ciki. Duk lokacin da ta koma asibitin, maganin rage raɗaɗi kawai suke bata,” in ji Mohammed.

Mohammed ya ƙara da cewa, kwana biyu kacal kafin mutuwarta aka gudanar da gwaje-gwajen lafiya wanda ya kai ga ɗaukar hoton na’urar haske, wanda ya nuna cewa an bar almakashi a cikin jikinta a lokacin tiyatar watan Satumba.

Ya ce, an fara shirye-shiryen yin tiyatar gyara, amma Aishatu ta mutu a ranar Litinin, 12 ga Janairu, 2026, kafin a yi tiyatar.

Bayan zarge-zargen, Hukumar Kula da Asibitoci ta Jihar Kano ta ba da umarnin a gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

Kano
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan
  • Sulaiman
    ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto
  • Sulaiman
    PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

MASU ALAKA

Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila
Manyan Labarai

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Next Post
Wang Yi Ya Yi Bayani Game Da Ziyarar Aikinsa A Wasu Kasashen Afirka

Wang Yi Ya Yi Bayani Game Da Ziyarar Aikinsa A Wasu Kasashen Afirka

LABARAI MASU NASABA

Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.