ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2027: Yusuf Buhari Ya Samu Tikitin Takarar Majalisar Wakilan Nijeriya A Jam’iyyar APC

by Muhammad
4 months ago

Yusuf Buhari, ɗan tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya samu tikitin jam’iyyar APC domin tsayawa takarar kujerar Majalisar Wakilai ta tarayya mai wakiltar mazabar Daura/Sandamu/Mai’adua a zaɓen 2027.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa (NAN) ya ruwaito cewa Yusuf ya samu tikitin ba tare da hamayya ba, bayan wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Jihar Katsina a ranar Talata, 28 ga Afrilu, inda aka amince da shi baki ɗaya a matsayin ɗan takarar jam’iyyar.

Shugaban Kwamitin Yarjejeniya na Yankin Daura, Alhaji Ahmed Dangiwa, tsohon Ministan Gidaje da Raya Birane, ne ya sanar da wannan matsaya.

ADVERTISEMENT

Da yake jawabi bayan amincewa da Yusuf, Mannir Musa, Shugaban APC na Ƙaramar Hukumar Mai’adua, ya buƙaci mambobin jam’iyyar su karɓi sakamakon cikin kwanciyar hankali.

“Na roƙi dukkan mutanenmu da su yi biyayya su karɓi matsayar da kwamitin da masu ruwa da tsaki suka cimma cikin fahimta mai kyau. Ya kamata mu haɗa kai domin haɗin kan jam’iyya da cigaban al’ummarmu,” in ji shi.

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

Ya kuma roƙi Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, da ya tallafa wa waɗanda ba su samu tikiti ba domin su ci gaba da yi wa al’ummarsu hidima.

Musa ya buƙaci waɗanda aka ba tikiti ta hanyar yarjejeniya da su yi aiki tukuru domin wakiltar al’ummarsu yadda ya kamata idan aka zaɓe su.

Ya ƙara da cewa sauran ‘yan takarar da suka samu tikiti kai tsaye sun haɗa da Nasir Yahaya domin kujerar Sanatan Daura, da Mustapha Musa domin kujerar Majalisar Dokokin Jihar Katsina mai wakiltar Mai’adua.

A nasa jawabin, Yusuf Buhari ya gode wa mambobin jam’iyyar bisa amincewar da suka nuna masa, tare da alƙawarin yin wakilci nagari idan aka zaɓe shi.

Muhammad
+ postsBio
  • Muhammad
    Yadda Na Tsira Daga Cutar Mashaƙo A Katsina: “Na Fara Da Tsartuwar Jini Tare Da Yawu”
  • Muhammad
    An Naɗa Yusuf Nasidi Nasir A Matsayin Talban Barayan Kano
  • Muhammad
    Wani Kamfani Ya Tallafa Wa Masu Sana’ar Shayi A Kano
  • Muhammad
    Kosan Waka Ya Rasu, Gwamnan Kano Ya Jajanta Wa Iyalansa

MASU ALAKA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027
Siyasa

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi
Manyan Labarai

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

September 8, 2026
Siyasa

Muna Da Yan Takarar Gwamna A Jihohi 28 Don Shiga Zaben 2027

September 6, 2026
Next Post
Jami’in MDD Ya Yaba Da Manufar Soke Harajin Kwastam Ta Kasar Sin A Matsayin Kyakkyawan Ci Gaba

Jami’in MDD Ya Yaba Da Manufar Soke Harajin Kwastam Ta Kasar Sin A Matsayin Kyakkyawan Ci Gaba

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.