ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, June 24, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Kashe Wani Mamba Na NYSC A Harin Fashi Da Makami A Abuja

by Rabi'u Ali Indabawa
2 months ago
Mamba

Wani dan bautar kasa, Abdulsamad Jamiu, ya rasa ransa bayan ya shiga tsakiyar musayar wuta tsakanin sojoji da wasu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne a yankin Dei-Dei da ke Abuja.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Asabar a unguwar Shagari E da ke yankin.

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar soji, Odunola Olawuyi, ya fitar a ranar Lahadi, ya ce sojojin rundunar Kuick Response Group suna sintiri na dare ne lokacin da suka karbi kiran gaggawa kan harin fashi da makami.

ADVERTISEMENT

Ya ce da zuwansu wurin, ‘yan fashin da ke gudu suka bude musu wuta, wanda ya haifar da musayar wuta tsakanin bangarorin biyu.

A cikin wannan musayar wuta ne Abdulsamad Jamiu ya tsinci kansa cikin harsasai.

LABARAI MASU NASABA

Gwanjon Kadarori: Kotun Daukaka Kara Ta Kori Karar Da Sani Sha’aban Ya Shigar

’Yansanda Sun Ceto Yaro Mai Shekara Shida Da Aka Sace, Sun Cafke Wanda Ake Zargi A Borno

Rundunar sojin ta bayyana cewa duk da kokarin da sojoji suka yi na tabbatar da tsaro da kare jama’a, dan bautar kasar ya rasu sakamakon raunin da ya samu.

Sojojin sun bayyana lamarin a matsayin abin takaici, suna masu cewa yanayin lokacin ya kasance mai tsanani yayin da ake kokarin fatattakar ‘yan fashin tare da kare mazauna yankin.

Kwamandan Rundunar Guards Brigade, hafsoshi da sojoji sun mika sakon ta’aziyyarsu mai zurfi ga iyalan marigayin, NYSC, da kuma duk wadanda wannan babban rashi ya shafa. Sun ce suna tare da su cikin wannan bakin ciki mai tsanani.

Sanarwar ta kara da cewa an kai gawar mamacin Asibitin Gwamnati na Kubwa a Babban Birnin Tarayya.

Rundunar sojin ta kuma bayyana cewa an fara bincike domin gano ainihin yadda lamarin ya faru, tare da tabbatar da cewa za a bayyana sakamakon binciken ga jama’a.

Haka kuma rundunar ta ce tana nan daram wajen jajircewa wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a a Babban Birnin Tarayya.

Ta kara da cewa za ta ci gaba da duba hanyoyin gudanar da ayyukanta domin kara inganta tsaron fararen hula, yayin da dakarunta ke ci gaba da fuskantar masu aikata laifi da ke barazana ga zaman lafiyar al’umma.

An bukaci mazauna yankin su kwantar da hankalinsu tare da ba hukumomin tsaro cikakken hadin kai.

Da yake mayar da martani kan lamarin, wata kafar da ke bibiyar ayyukan soja da tsaro a Nijeriya mai suna Nigerian Armed Forces Diary, ta wallafa a shafinta na Facebook a ranar Lahadi, inda ta yi Allah-wadai da abin da ya faru tare da kira da a gudanar da gaggautaccen bincike.

Kafar ta ce: “Wannan matashin da kuke gani a hoton nan ya rasu! Har zuwa rasuwarsa, yana cikin masu yi wa kasa hidima na NYSC. A cikin dakin sa da ke Shagari Kuarters, Dei-Dei, Abuja, jami’an sojoji sun harbe shi har ya rasa ransa, suna ikirarin cewa ‘kuskure ne’.

“Marigayi Samad ba don laifi ba ne. Yana kawai yi wa kasarsa hidima ne, amma ya rasa ransa a hannun wadanda aka dauka domin kare shi.

“Muna bukatar shugabancin soja ya gaggauta bincike kan wannan lamari, a hukunta wadanda ke da hannu, kuma a tabbatar an yi wa iyalansa adalci. Allah ya kare irin wannan abu daga sake faruwa,” in ji sakon.

A wani labarin kuma, jaridar PUNCH Metro ta ruwaito cewa a ranar 23 ga Afrilu, an kashe wani dan bautar kasa, Ben Agir, bayan da wasu ‘yan sa-kai suka doke shi har lahira a karamar hukumar Buruku ta Jihar Benuwe .

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a yankin Anibros yayin sintirin dare da ‘yan sa-kan ke yi.

Sojoji Sun Ceto Wanda Aka Yi Garkuwa Da Shi, Sun Kuma Kwato Naira Miliyan 8 A Filato

Rahotanni sun bayyana cewa aikin ceto ya biyo bayan samun bayanan sirri da dakarun soji suka yi amfani da su wajen kai farmaki ga maboyar masu garkuwa da mutane.

Sojojin sun kuma yi nasarar kama wasu daga cikin wadanda ake zargi da aikata laifin, yayin da ake ci gaba da bincike domin kamo sauran mambobin kungiyar.

Rundunar ta jaddada kudirinta na ci gaba da yaki da masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata laifuka, tare da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a a yankin.

Dakarun Operation Enduring Peace sun ceto wata da aka yi garkuwa da ita tare da kwato Naira miliyan 8 da aka biya a matsayin kudin fansa a Karamar Hukumar Kua’an Pan ta Jihar Filato .

An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar hadin gwiwa ta Operation Enduring Peace, Kyaftin Chinonso Polycarp Oteh, ya sanya wa hannu a ranar Lahadi.

Sanarwar ta ce an gudanar da aikin ne a ranar Asabar, 25 ga Afrilu, 2026, inda dakarun da ke Sektor 9 Shendam suka yi nasarar ceto wanda aka yi garkuwa da shi tare da kwato kudin fansa da iyalansa suka biya.

A cewar sanarwar, an yi garkuwa da matar ne a ranar 19 ga Afrilu, 2026, a yankin Bauna da ke karamar hukumar Shendam.

Ta kara da cewa ta hanyar tattara bayanan sirri da kuma tambayar wani da aka kama wanda ya amsa laifin, dakarun sun gano inda aka boye ta a dajin Padam da ke Karamar Hukumar Kua’an Pan, inda suka same ta suka ceto ta.

Sojojin sun kuma bayyana cewa an kwato kudin fansa da aka biya wato Naira miliyan 8, wanda aka mayar wa iyalan wanda aka sace bayan ceto ta.

Bayan an ceto ta, an kai ta asibitin gwamnati na Shendam domin duba lafiyarta kafin daga bisani a mika ta ga iyalanta.

Sanarwar ta kuma ce dakarun na ci gaba da gudanar da bincike da farmaki a maboyar ‘yan garkuwa da mutane a yankin Kua’an Pan da Shendam domin kama sauran mambobin kungiyar.

Rundunar ta kuma yabawa jama’a bisa hadin kai, tare da kira a ci gaba da bayar da bayanai cikin gaggawa domin taimakawa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro.

Mamba
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Nijar Ta Rattaba Hannu A Kan Dokar Haramta Auren Jinsi
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Za Mu Iya Sayar Da Manmu Ba Tare Da Wata Matsala Ba -Iran
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Dattawan Arewa Sun Buƙaci Tinubu Ya Ayyana Dokar Ta-baci Kan Tabarbarewar Tsaro
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Nijeriya Ta Karbi Ƴan Nijeriya 268 Da Suka Tsero Daga Afirka Ta Kudu

MASU ALAKA

Katsina: Kotu Ta Yanke Wa Hauwa’u Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Taimaka Wa ’Yan Bindiga
Kotu Da Ɗansanda

Gwanjon Kadarori: Kotun Daukaka Kara Ta Kori Karar Da Sani Sha’aban Ya Shigar

June 18, 2026
‘Yansanda Sun Ceto Mutum 21 Da Aka Sace, Sun Kwato N4.8m Kuɗin Fansa
Kotu Da Ɗansanda

’Yansanda Sun Ceto Yaro Mai Shekara Shida Da Aka Sace, Sun Cafke Wanda Ake Zargi A Borno

June 13, 2026
An Cafke Mutum Uku Kan Kisan Mawaki Dan Asalin Nijeriya Da Birtaniya
Kotu Da Ɗansanda

An Cafke Mutum Uku Kan Kisan Mawaki Dan Asalin Nijeriya Da Birtaniya

June 13, 2026
Next Post
Cutar Maleriya Na Ci Gaba Da Yi Wa ‘Yan Nijeriya Kisan Mummuke

Cutar Maleriya Na Ci Gaba Da Yi Wa ‘Yan Nijeriya Kisan Mummuke

Discussion about this post

LABARAI MASU NASABA

An Kashe Mutum 2, 8 Sun Jikkata Yayin Rikici A Bauchi

An Kashe Mutum 2, 8 Sun Jikkata Yayin Rikici A Bauchi

June 24, 2026
Tsohon Shugaban APC Na Kebbi Ya Rasu A Hannun ’Yan Bindiga

Tsohon Shugaban APC Na Kebbi Ya Rasu A Hannun ’Yan Bindiga

June 24, 2026
Ya Kamata Sin Da Birtaniya Su Yi Aiki Tare Don Ci Gaba Da Inganta Dangantakarsu

Ya Kamata Sin Da Birtaniya Su Yi Aiki Tare Don Ci Gaba Da Inganta Dangantakarsu

June 23, 2026
Firaministan Sin Ya Jaddada Muhimmancin Kara Azamar Bunkasa Kirar Kayayyakin Aikin Masana’antu Na Zamani

Firaministan Sin Ya Jaddada Muhimmancin Kara Azamar Bunkasa Kirar Kayayyakin Aikin Masana’antu Na Zamani

June 23, 2026
Gombe Ta Zabge Farashin Taki Da Kashi 50 Cikin 100

Gombe Ta Zabge Farashin Taki Da Kashi 50 Cikin 100

June 23, 2026
Wang Yi Ya Gana Da Babban Sakataren Majalisar Tsaron Masar Da Ministan Fadar Gwamnatin Afirka Ta Kudu A Indiya

Wang Yi Ya Gana Da Babban Sakataren Majalisar Tsaron Masar Da Ministan Fadar Gwamnatin Afirka Ta Kudu A Indiya

June 23, 2026
‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi

’Yansanda Sun Kama Mutane 57 Da Ake Zargi Da Ayyukan Ta’addanci A Adamawa

June 23, 2026
Li Qiang Ya Gana Da Firaministan Kasar Guinea

Li Qiang Ya Gana Da Firaministan Kasar Guinea

June 23, 2026
Maniyyatan Nijeriya

Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Jigilar Alhazan Nijeriya Daga Saudiyya

June 23, 2026
Kamfanin Sin Ya Kammala Babban Aikin Samar Da Ruwa A Babban Birnin Nijeriya

Kamfanin Sin Ya Kammala Babban Aikin Samar Da Ruwa A Babban Birnin Nijeriya

June 23, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.