ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Sake Samun Gawar Wani Dan Nijeriya A Gidansa Da Ke Burtaniya

by Rabi'u Ali Indabawa
5 months ago
Nijeriya

Kusan mako guda bayan rasuwar wata uwa ‘yar Nijeriya mai ‘ya’ya uku sakamakon cutar daji a kasar Burtaniya, an sake samun wani lamari mai ban tausayi inda wani uba dan Nijeriya mai ‘ya’ya uku, wanda aka bayyana sunansa da Herbert kawai, aka same shi a mace a cikin gidansa.

Marigayin ya bar mata da ‘ya’ya uku kanana, yayin da iyalansa ke neman tallafin kudi domin gudanar da jana’izarsa da kuma mayar da gawarsa gida Nijeriya.

Rahotanni sun nuna cewa Herbert, wanda ke zaune a Thornaby, ya mutu ne a cikin barci a makon da ya gabata, lamarin da iyalansa suka bayyana a matsayin abin girgiza da radadi.

ADVERTISEMENT

Wani mai amfani da dandalin D mai suna “The Stress Manager” ya bayyana cewa marigayin yana fuskantar matsananciyar damuwa ta zuciya da ta kudi bayan rasuwar mahaifinsa a Nijeriya kwanaki kadan kafin mutuwarsa.

Ya ce: “Herbert mutum ne mai nutsuwa kuma uba mai kula da iyalinsa. Ya rasu kwatsam a cikin barci a Thornaby.

LABARAI MASU NASABA

Direbobi 123 A Kano Suna Fuskantar Tuhuma Kan Laifin Keta Dokokin Amfani Da Lambar Mota

‘Yansanda Sun Kama Mutum Biyu Kan Zargin Damfarar Wayar Salula A Jihar Adamawa

“Kwanaki kadan kafin rasuwarsa, yana cikin jimamin rasuwar mahaifinsa a Nijeriya. Bai samu damar zuwa jana’izar ba, amma ya kashe duk abin da yake da shi domin ganin an yi masa jana’iza mai kyau. Wannan ya jefa shi cikin matsananciyar damuwa da rashin kudi.

“Sai ga abin da ba a zata ba ya faru—Herbert ya rasu a ranar da aka binne mahaifinsa.”

An kuma bayyana cewa abin ya fi muni saboda ‘ya’yansa ne suka fara gano gawarsa da safe, yayin da matarsa ba ta gida a lokacin.

A halin yanzu, matarsa na fuskantar nauyin kula da ‘ya’yansu uku tare da wahalar kudin jana’iza da mayar da gawar gida.

Tsohon shugaban ‘yan Nijeriya a Birtaniya, Benjamin Kuti, ya tabbatar da rasuwar Herbert tare da kira ga al’ummar ‘yan Nijeriya da su taimaka wa iyalansa.

An kuma kaddamar da wani shirin tara kudi domin tallafa wa iyalan, inda zuwa lokacin rubuta rahoton an tara fam £2,633 daga cikin burin £7,000.

A baya dai, an ruwaito rasuwar wata uwa ‘yar Nijeriya mai ‘ya’ya uku, Omotayo Abioye, wadda ta mutu sakamakon cutar sankarar mama tana da shekaru 40, lamarin da ya kara jefa al’umma cikin jimami.

Nijeriya
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

Direbobi 123 A Kano Suna Fuskantar Tuhuma Kan Laifin Keta Dokokin Amfani Da Lambar Mota
Kotu Da Ɗansanda

Direbobi 123 A Kano Suna Fuskantar Tuhuma Kan Laifin Keta Dokokin Amfani Da Lambar Mota

July 18, 2026
An Kama Matashi A Kano Kan Zargin Kashe Abokinsa
Kotu Da Ɗansanda

‘Yansanda Sun Kama Mutum Biyu Kan Zargin Damfarar Wayar Salula A Jihar Adamawa

July 18, 2026
Disu
Kotu Da Ɗansanda

IGP Disu Ya Hana Jami’an Ƴansanda Yin Amfani Da TikTok Da Instagram Da Sauransu

June 26, 2026
Next Post
Farfesa Abdalla Uba Adamu Ya Yi Ritaya Bayan Shekaru 46 Na Aiki

Farfesa Abdalla Uba Adamu Ya Yi Ritaya Bayan Shekaru 46 Na Aiki

LABARAI MASU NASABA

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026
Zabe: Gwamnatin Kano Ta Taƙaita Zirga-zirgar Mutane Da Ababen Hawa

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.