Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya soki matakin Shugaba Bola Tinubu na neman sabon bashi a ƙasar waje na dala miliyan 516, yana mai bayyana hakan a matsayin rashin tsari a harkokin kuɗi a daidai lokacin da Nijeriya ke fama da nauye nauye-nauyen bashi.
Shugaban Tinubu ƙasa ya aike da buƙatar ga Majalisar Ƙasa domin amincewa da bashin da za a yi amfani da shi wajen aikin titin Sokoto–Badagry.
Da yake mayar da martani, Atiku ya nuna damuwa kan yadda gwamnatin tarayya ke ci gaba da dogaro da bashin waje ba tare da isasshen bayani na gaskiya ba kan Sharuɗɗa da yadda za a biya. Ya ce wannan mataki na tada tambayoyi masu yawa kan gaskiyar gwamnati wajen kula da dukiyar al’umma.
Ya kuma yi gargadin cewa tara ƙarin bashi ba tare da ingantaccen tsarin biya ba na iya ƙara tabarbarewar tattalin arziƙi tare da ɗora wa al’umma, musamman na masu tasowa, wani nauyi mai tsanani. A cewarsa, wajibi ne gwamnati ta rungumi tsauraran matakan kula da kuɗi da kuma nemo wasu hanyoyin samar da kuɗaɗe.
Atiku ya buƙaci gwamnati da ta bayyana cikakkun bayanai kan bashin da kuma tasirinsa ga ƙasa. Duk da cewa aikin titin Sokoto–Badagry ana kallonsa a matsayin muhimmin shiri na inganta haɗin kai da tattalin arziki, har yanzu batun yadda za a biya bashin na ci gaba da jawo muhawara a tsakanin masu tsara manufofi da masana tattalin arziki.















Discussion about this post