Ci Gaban Bangaren Ciniki A Kasar Sin Ya Nuna Yadda Kasar Ke Samar Da Damammaki Ga Kasashen Duniya
Alkaluman da hukumomin kasar Sin suka gabatar a jiya Juma'a sun nuna cewa, darajar kayayyakin da aka shigar da su...
Alkaluman da hukumomin kasar Sin suka gabatar a jiya Juma'a sun nuna cewa, darajar kayayyakin da aka shigar da su...
Ma'aikatar tsaron kasar Sin ta soki kokarin Japan na gangancin fadada karfin soji, tana mai bayyana hakan a matsayin barazana...
A babban taron AI na duniya na 2026, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar da cewa, Sin za ta samar wa kasashe 30 tsarin fasahar gargadin abkuwar bala’u daga indalahhi da ake kira “MAZU’ a cikin shekaru biyar masu zuwa. A halin yanzu kuwa, "MAZU" ta riga ta fara aiki a kasashe 7 ciki har da Jibouti, Habasha da Pakistan, kuma ta baiwa kasashe sama da 40 a duniya hidimomi ta yanar gizo. Afirka daya ce daga cikin yankuna mafi fama da sauyin yanayi a duniya, inda yanayi mai tsanani ke ci gaba da kawo cikas ga ci gaban tattalin arzikin nahiyar. Ma'aikacin tashar jiragen ruwa na Jibouti Mohamed Ali ya sha fuskantar rashin tabbas a kowace rana, wato zafi mai tsanani, iska mai karfi da ba zato ba tsammani, ruwan sama kamar da bakin kwarya na lokaci-lokaci da lalacewar kayan aiki da raunin jiki sun zama ruwan dare. Damina a Habasha tana haifar da ambaliya da zaftarewar kasa, wadda ke haddasa asarar rayuka da kuma gudun hijira. Shugaban hukumar kula da yanayi ta Kamaru ya bayyana cewa, "Yawancin kasashen Afirka ba su da isassun tashoshin sa-ido kan yanayi, kuma suna da karancin karfin lissafi na yanar gizo. Sai dai tsarin "MAZU" ta cika wannan gibin. A shekara ta 2025, Sin ta bai wa Jibouti kyautar tsarin fasahar "MAZU" samfurin 1.0. Tawagar kwararrun Sin ta yi bincike a wurin, tare da tsara tsarin gargadi na musamman ga tashar jiragen ruwa a wurin. Yanzu, ana iya ba da gargadin yanayi mai tsanani sa'o'i 24 kafin lokaci. Shugaban hukumar kula da yanayi ta Jibouti mai suna Nour ya ce: "'MAZU' tana da amfani sosai, kuma bangaren Sin ya horar da ma'aikata da dama ’ya’yan kasarmu." A watan Yulin bana, an mika "MAZU" Jibouti samfurin 2.0 a hukumance ga kasashen Afirka, inda aka inganta aikin hasashen yanayi, tsarin kuma yana dauke da fasahar AI, wadda ke iya tantance yanayi da kanta, da kuma ba da gargadi da kanta. Ta haka, an samar da dabarar daidaita matsala mai amfani, bisa tsarin "Bincike - sanarwa - gargadi". Sunan "MAZU" yana da ma'ana mai zurfi, MAZU a Turanci na wakiltar kalmomi 4, wato nau'ikan bala'i da yawa, gargadi, kawar da bambanci da kuma fa'ida ga kowa. Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya yaba wannan tsari da cewa, "Dandamali, tauraron dan adam da samfuran AI na Sin sun taimaka wa kasashe da dama wajen karfafa tsarin gargadi. Wannan ita ce hanyar hadin gwiwa da duniya ke bukata, wato taimaka wa kasashe su kare al'ummarsu ta hanyar samar da fasaha da gina karfin daidaita matsala na kansu." Ba wai kawai a fannin hasashen yanayi ba, fasahar AI ta Sin tana kara shiga cikin harkokin rayuwar al'ummar Afirka. Noma a matsayin sana’ar da ke daukar kashi 45-60% na guraben aikin yi a Afirka, kuma mai ba da gudunmawar kashi 15-20% na GDPn kasashen, tana matukar bukatar AI don yin hasashen matsalar kwari da cututtuka da kuma yawan amfanin gona da za a iya girba. Saboda haka matakan da Sin ta dauka suna biyan wadannan bukatun kai tsaye. "Sin tana nacewa ga manufar sanya muradun jama’a a gaban kome da kuma kokarin cika alkawarin rage gibin AI a duniya, matakin ya yi daidai da burin ci gaban AU," in ji farfesa Gaspard Banyankimbona na kwamitin ilimi, kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire na kungiyar kasashen Afirka ta AU, wanda ya yaba da rawar da Sin ke takawa wajen ba da jagora a bangaren AI a duniya. Daga ma'aikacin tashar jiragen ruwa na Jibouti da ya daina damuwa kan abkuwar bala’un yanayi kwatsam, zuwa samun karfin yin gargadi da kai a yankuna masu tsauni dake Habasha, har zuwa kokarin hadin gwiwar AI na Sin da Afirka, dukkan matakan suna rage gibin dijital da amfanar da al'umma. Wannan shi ne abin da ya fi jan hankali game da hadin gwiwar AI tsakanin Sin da Afirka, wato fasahar AI ta Sin tana amfanar da al'ummar Afirka a rayuwarsu ta yau da kullum.(Marubuciya: MINA)
A ’yan kwanakin baya bayan nan, wani rahoto daga rukunin masanan Amurka, ya yi ikirarin cewa matakin takaita baiwa dalibai...
Takardar tsaro ta farko da aka fitar bayan firaministar Japan Takaichi Sanae ta kama aiki, ta jawo suka daga al’ummomin...
An gudanar da bikin bude gadar kogin Nyong ta Kamaru, wadda kamfanin China First Highway Engineering Co., Ltd. (CFHEC) na...
Hukumar UNESCO da ke da hedkwata a birnin Paris na kasar Faransa, ta sanar a jiya Laraba cewa, bisa shawarar...
Ma'aikatar tsaro ta kasar Japan ta fitar da takardar bayani kan aikin tsaro na shekara ta 2026 a ranar Talata 4...
Mukaddashin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Sun Lei, ya kirayi a karfafa sarrafa sabbin fasahohin zamani yadda ya...
Idan an sa "ciniki tsakanin Afirka da Sin" a shafin Google don duba bayanai masu nasaba da kalmomin, to, za a ga bayanan da AI na Google ya samar, galibi bisa tushen labaran da kafofin yada labarai na kasashen yammacin duniya suka watsa, sun shafi "karuwar adadin ciniki", gami da "habakar gibin da kasashen Afirka ke fuskanta yayin da suke ciniki da kasar Sin". Kamar yin ciniki da kasar Sin zai sa kasashen Afirka gamuwa da hasara. Amma shin batun haka yake? Jimillar cinikin da aka yi tsakanin Afirka da Sin a shekarar 2025 sun nuna cewa, idan an tantance su bisa darajar kayayyaki, to, za a ga kaso 75% na kayayyakin da kasar Sin ta fitar zuwa kasashen Afirka, su ne injuna, da sassansu, da na'urorin latironi, da sinadaran da ake bukata wajen sarrafa wasu kayayyaki, da dai sauransu. Wadannan kayayyaki ana kiransu "kayayyaki na matakin tsakiya", domin ba su kai zama kayayyaki na karshe ba tukuna. Sa'an nan a masana'antun kasashen Afirka, an ci gaba da sarrafa wadannan kayayyaki, don mayar da su kayan karshe. Ta wannan hanya, an haifar wa kasashen Afirka karuwar GDP, da ci gaban masana'antu, da karin guraben aikin yi, gami da damar shiga tsarin samar da kayayyaki na duniya. Wani masanin ilimin tattalin arziki da ke aiki a jami'ar Abuja ta kasar Najeriya, Kennedy Kenchuks Chukwueme, ya taba gaya ma 'yan jaridan kasar Sin cewa, idan wata kasa ta fi shigar da "kayayyaki na matakin tsakiya" daga kasashen waje, to, ko da yake tana fuskantar gibin ciniki, hakan zai tabbatar da makomarta ta inganta bangaren masana'antu. Ya ce, misali, kayayyakin aikin gini, da injuna da ake shigar da su daga kasar Sin zuwa Najeriya, sun samar da damar tsimin kudi yayin da ake gina tashohin jiragen ruwa, da layin dogo a Najeriya, gami da taimakawa Najeriya raya masana'antu, da inganta aikin fitar da kayayyaki zuwa kasuwannin ketare. Yayin da ake tantance cinikin da ake yi tsakanin Afirka da Sin, bai kamata a lura da gibin ciniki da ake samu ba kawai, maimakon haka, ya kamata a kara mai da hankali kan yanayin taimakawa juna na tsare-tsaren tattalin arzikin Afirka da Sin. Afirka har yanzu tana wani mataki na farko a fannin raya masana'antu, saboda haka, nahiyar ta fi fitar da makamashi, da ma'adinai, da amfanin gona zuwa ketare. A nata bangare, kasar Sin ta kware a fannin masana'antu na zamani, don haka tana iya samar da dimbin "kayayyaki na matakin tsakiya" ga kasashen Afirka, a kokarin biyan bukatarsu ta raya masana'antu. Bisa hadin gwiwar Afirka da Sin, idan kasashen Afirka za su iya zamanantar da tsarin hada-hadar samar da kaya, da kyautata muhallin zuba jari a-kai-a-kai, to, tabbas za su samu sakamako mai gamsarwa, wanda zai kunshi ci gaban tattalin arzikin dukkan bangarorin Afirka da Sin, da damar tabbatar da moriyar junansu. (Bello Wang)
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.