Tinubu Ya Yaba Da Ceto ’Yan NYSC 15 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Kogi
Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana farin cikinsa da jin labarin ceto mambobin NYSC 15 da wasu ’yan Nijeriya...
Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana farin cikinsa da jin labarin ceto mambobin NYSC 15 da wasu ’yan Nijeriya...
Peng Liyuan, uwargidan shugaban kasar Sin, Xi Jinping, da Aigul Japarova, uwargidan shugaban kasar Kyrgyzstan, Sadyr Japarov, sun ziyarci gidan...
Hukumar Kula da Yanayi ta Nijeriya (NiMet) ta yi hasashen yanayi daban-daban na tsawon kwanaki uku, ciki har da rana,...
Da yammacin yau Litinin 31 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping wanda ke halatar taron kolin kungiyar hadin gwiwa...
A daidai lokacin da ake gudanar da taron koli na kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO), daga yau 31 ga...
Shahararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa na duniya, Lionel Messi, ya sanar da yin ritaya daga buga wa ƙasar Argentina ƙwallon...
An ceto masu yi wa kasa hidima 10 (NYSC) da wasu ’yan bindiga suka yi garkuwa da su daga dajin...
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Guo Jiakun, ya jagoranci wani taron manema labarai a yau Litinin...
Shugaban kasar Sin, Xi Jinping, ya isa birnin Bishkek a yau Lahadi domin halartar taron kolin Kungiyar Hadin Gwiwa ta Shanghai (SCO) na shekarar 2026, da kuma gudanar da ziyarar aiki a kasar Kyrgyzstan. Shugaban kasar Kyrgyzstan, Sadyr Japarov, da uwargidansa sun tarbi shugaba Xi Jinping da uwargidansa, Peng Liyuan, a filin jirgin saman kasa da kasa na Manas, a yau Lahadi. Shugaba Xi ya gabatar da sako a rubuce, a madadin gwamnati da al'ummar kasar Sin, inda ya mika kyakkyawar gaisuwa da fatan alheri ga shugaba Sadyr Japarov da al'ummar kasar Kyrgyzstan. Xi ya bayyana cewa, dangantakar abota tsakanin Sin da Kyrgyzstan tana da dogon tarihi da zamani mai alfanu, kuma tsaunukan Tianshan sun shaida musayar zumunta mai danko tsakanin al'ummomin biyu a tsawon dubban shekaru. Kazalika, tun bayan kulla huldar diflomasiyya shekaru 34 da suka gabata, dangantakar Sin da Kyrgyzstan ta tsallaka siradin sauye-sauyen siyasar duniya, tare da samun ci gaba mai inganci ba tare da tangarda ba, har ta kai matsayin hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare na matakin koli a sabon zamani. Shugaba Xi ya kara da cewa, a yayin wannan ziyara, zan yi cikakkiyar tattaunawa da shugaba Japarov kan dangantakar Sin da Kyrgyzstan, da hadin gwiwa a fannoni daban-daban, da kuma batutuwan kasa da kasa da na shiyya-shiyya kan muradun juna, domin tsara sabon shirin gina al'ummar Sin da Kyrgyzstan mai kyakkyawar makoma ta bai-daya. Ina fatan halartar taron kolin kungiyar SCO da za a gudanar a Bishkek, tare da yin aiki da dukkan bangarori don karfafa samun ci gaba mai dorewa ga Kungiyar Hadin Gwiwa ta Shanghai. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
A yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ke halartar taron koli na kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai wato SCO...
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.