CMG Ya Kaddamar Da Bikin Nuna Fina-Finai Da Shirye-Shiryen Talabijin Masu Inganci A Masar
Kafin ziyarar aiki a Masar da shugaban Sin Xi Jinping zai yi, babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin...
Kafin ziyarar aiki a Masar da shugaban Sin Xi Jinping zai yi, babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin...
An Kai Kayayyakin Agaji Masu Yawa Zuwa Gyirong Na Yankin Hukumar kai dauki da ba da agajin gaggawa ta yankin Xizang ta bayyana a jiya Alhamis cewa, an kai kayayyakin agaji masu yawa zuwa garin Gyirong na birnin Xigaze, ciki har da shinkafa tan 50 da garin alkama tan 20 da man girki tan 1, da kuma tantuna 1,122, da barguna 8,054, kana da injunan samar da wutar lantarki 14, da fakitin ruwan sha 15,500, da sauran kayayyakin amfanin yau da kullum. Bayan haka, an tura kwararru 86 daga fannoni daban-daban kamar albarkatun kasa zuwa yankin da ibtila'in ya shafa, tare da kayan aiki na musamman, don karfafa bincike kan hadurran yanayin kasa a kewayen yankin, da kuma duba manyan wuraren dake da hatsarin abkuwar ibtila'i kamar tsaunuka da hanyoyi da gine-gine da sauransu, don rigakafin sake abkuwar wani ibtila’i ko kuma ibtila’i mai biyo baya. Ya zuwa yanzu, an kammala tsugunar da mutane 499 da ibtila'in zabtarewar kasa da laka ya shafa, kuma an kwashe masu yawon bude ido 555 da suka makale. Kazalika, hukumar ta kara da cewa, wannan ibtila'in zabtarewar kasa da laka a Gyirong na yankin Xizang, lamari ne mai sarkakiya wanda ya samo asali daga zabtarewar kankara mai tsayi a kasar Nepal, inda ya haifar da kwararar tarkacen kankara, sannan ya canja zuwa zabtarewar kasa da laka. (Amina Xu)
Da safiyar yau Jumma'a, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwa ta Sin ya gudanar da taron manema labarai, inda ya...
A yau Jumma’a, ma’aikatar kula da masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin ta sanar da cewa, tun daga farkon...
A yau Jumma’a, Xi Jinping, babban sakataren kwamitin tsakiya na Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS), ya jagoranci taron shugabanni na jam’iyyar domin tattaunawa da fitar da tsare-tsaren ayyukan ceto da ba da agaji, bayan abkuwar mummunar zabtarewar kasa a gundumar Gyirong, da ke jihar Xizang mai cin gashin kanta, a kudu maso yammacin kasar Sin. A farkon taron dai, Xi wanda har ila yau shi ne shugaban kasar Sin kuma shugaban hukumar soja ta tsakiya, tare da sauran shugabanni, sun yi shiru na dan lokaci domin nuna alhini game da wadanda ibtila’in ya shafa, wanda ya abku a gundumar Gyirong da ke kan iyakar Nepal da Sin, a ranar Larabar da ta gabata. Taron ya yi nuni da cewa, ibtila’in malalar baraguzai daga bangaren kasar Nepal, ya haifar da asarar rayuka da dama tare da katse hanyoyin sadarwa a kan iyaka ta Gyirong da ke gundumar Gyirong, a birnin Xigaze na jihar Xizang. Bayan abkuwar lamarin, kwamitin tsakiya na JKS ya ba shi muhimmanci sosai, inda babban sakatare Xi Jinping ya bayar da muhimman umarni nan take, tare da gabatar da abubuwan da ake bukata takamaime game da ayyukan ceto da daukar matakan gaggawa na ba da agaji. Bisa sahalewar babban sakataren, firaminista Li Qiang ya garzaya zuwa wurin da ibtila’in ya abku domin ziyara da kuma rarrashin wadanda lamarin ya shafa da karfafa gwiwar ma’aikatan ceto, tare da bayar da jagoranci kai-tsaye a wurin kan ayyukan ceto da daukar matakan gaggawa na ba da agaji. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
'Yan siyasar kasashen yamma kan karawa batun "rarar kayan da Sin ta samar" gishiri, amma a Afirka, an kira shi...
Masana’antar sarrafa bayanai ta kasar Sin ta ci gaba da fadada cikin sauri a shekarar 2025, inda take tallafa wa...
Yau Jumma’a, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon ta’aziyya ga shugaban Nepal Ram Chandra Poudel, game da...
Maulidin Bana:Babu Wanda Ya Fi Cancanta Da Soyayya Kamar Annabi (SAW) —Mai Diwani
Yau Alhamis, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin, Lin Jian ya jagoranci wani taron manema labarai na yau da kullun. Da...
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.