Ibtila’in Zaftarewar Kasa: Ministan Harkokin Wajen Sin Ya Zanta Da Takwaransa Na Nepal Ta Wayar Tarho
Ana ci gaba da aiwatar da shirin tallafin da Sin ta ware wa kasar Nepal, wanda ya hada da tallafin...
Ana ci gaba da aiwatar da shirin tallafin da Sin ta ware wa kasar Nepal, wanda ya hada da tallafin...
Da safiyar ranar 26 ga watan nan da muke ciki, an samu abkuwar mummunan ibtila’in zabtarewar kasa a bangaren kasar Nepal mai makwabtaka da kasar Sin, lamarin da ya janyo babbar hasarar rayuka gami da bacewar wasu mutane da dama a gundumar Gyirong ta birnin Xigaze na jihar Xizang mai cin gashin kanta ta kasar Sin, wato yankin kan iyakokin Sin da Nepal. A yau Lahadi kuma an yi wani taron manema labarai a Gyirong dangane da ibtila’in, inda aka bayyana cewa, bayan abkuwarsa, an dauki matakan shawo kansa ba tare da bata lokaci ba a Xizang, inda aka kafa babban sashin kula da ayyukan ba da agajin gaggawa gami da wani sashin kula da agajin gaggawa da ke can yankin da ibtila’in ya ritsa da shi. Ma’aikatar kudi, da ma’aikatar shawo kan al’amuran ba-zata ta kasar Sin, sun ware kudin Sin Yuan miliyan 120, kana, kwamitin samar da ci gaba da yin gyare-gyare a gida na kasar ya ware Yuan miliyan 100, a wani kokari na tallafa wa ayyukan ba da agaji da ceto da kuma farfado da yankin da ibtila’in ya shafa. Kawo yanzu, an riga an tura ma’aikata 2141 na bangarori daban-daban domin bayar da agajin gaggawa a wurin, ciki har da na rundunar ’yantar da jama’ar kasar Sin, da ’yan sanda masu dauke da makamai, da tawagar ’yan kwana-kwana masu kai dauki da sauransu, gami da motocin agaji guda 269, hade da na’urorin kai dauki 3922. Zuwa karfe 6 na yammacin ranar 29 ga watan muke ciki, yawan mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon ibtila’in ya kai 16, yayin da wasu 546 suka bace. (Murtala Zhang)
Gwamnatin Jihar Kano, ta hannun Rundunar Hadin Gwiwa ta Hukumomi da dama kan Dakile Shaye-Shayen Miyagun Kwayoyi, ta kaddamar da...
Jami'an rundunar 'yansandan jihar Bauchi sun samu nasarar taso ƙeyar wani tsoho mai shekara 70 a duniya, Usman Abubakar, bisa...
A yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping zai kai ziyarar aiki a kasar Kyrgyzstan, gami da halartar taron koli...
Jirage mara matuka na shawagi a sama domin nazarin yanayi, yayin da tawagar ma’aikatan ceto ke tafe a kafa zuwa...
Masu bincike na kasar Sin sun kammala gwajin sadarwa tsakanin duniyar dan Adam da duniyar wata, inda suka yi nasarar...
Daga ranar 31 ga watan Agustan da muke ciki zuwa ranar 1 ga watan Satumba mai zuwa, za a gudanar...
Kasar Sin ta mika aikin gyara da fadada asibitin Masaka na Rwanda ga hukumomin kasar, yayin wani biki da ya gudana jiya Juma’a a babban birnin Kigali. Aikin wanda Sin ta bayar da tallafin gudanar da shi, shi ne aikin tallafi mafi girma da gwamnatin Sin ta gudanar a Rwanda, kuma wani muhimmin aiki na inganta rayuwa da ke karkashin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya. Biyo bayan gyara da fadada asibitin, girmansa ya karu daga murabba’in mita 6,398 zuwa murabba’in mita 56,957, yayin da adadin gadaje ya karu sosai daga 127 zuwa 837. An kuma samu karuwar adadin marasa lafiya da asibitin zai iya karba a kullum zuwa 2,000. Da yake jawabi yayin bikin, ministan lafiya na kasar Sabin Nsanzimana, ya ce wannan wani gagagrumin ci gaba ne ga kasar da kuma bangaren kiwon lafiya. Ya ce suna sa ran wannan asibiti zai zama alama ta ingantacciyar kiwon lafiya da za su iya samarwa a Rwanda da nahiyar Afrika. Kuma suna sa ran ci gaba da hada hannu da Sin don ganin hadin gwiwar ta fadada a bangaren kiwon lafiya. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Kafin ziyarar aiki a Masar da shugaban Sin Xi Jinping zai yi, babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin...
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.