An Bude Baje Kolin Canton Fair Karo Na 140 A Gabar Da Baje Kolin Ke Cika Shekaru 70 Da Kafuwa
Baje kolin hada-hadar cinikayya mafi girma da ake gudanarwa a kasar Sin da aka fi sani da “Canton Fair” ya cika shekaru 70 da kaddamarwa.  A yau Alhamis 15 ga watan Oktoban nan aka bude baje kolin na hajojin shige da fice karo na 140, a birnin Guangzhou na kudancin kasar Sin. Zango farko na baje kolin ya kunshi baje manyan hajoji na zamani, kuma yana gudana a yankunan baje hajoji 19 masu sassa biyar. Cikin hajojin da aka baje a yankunan sun hada da kayayyakin fasahohin zamani, irinsu kayan laturoni, da na na’urori masu sarrafa kansu, da ababen hawa masu aiki da sabon makamashi. (Saminu Alhassan)



















