Kwalejin Kimiyya Ta Kogi Ta Dakatar Da Malamai Kan Zargin Lalata Da Ɗalibai Da Sauran Laifuka
Mahukuntan Kwalejin Fasaha ta Jihar Kogi, Lokoja, sun dakatar da malamai bakwai daga aiki bisa zargin cin zarafin ɗalibai ta...
Mahukuntan Kwalejin Fasaha ta Jihar Kogi, Lokoja, sun dakatar da malamai bakwai daga aiki bisa zargin cin zarafin ɗalibai ta...
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta kammala aikin rajistar masu kaɗa ƙuri'a (CVR) a faɗin ƙasar ranar...
Kakakin rundunar sojojin ruwan Sin reshen kudancin kasar laftana Janar Zhai Shichen, ya bayyana a yau Lahadi cewa dakarun rundunar...
A yau Lahadi ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya mikawa shugaban kasar Maldives Mohamed Muizzu, sakon murnar cika shekaru...
A yau Lahadi, hukumar lura da ayyukan kandagarkin bala’o’i, da rage tasirinsu da samar da tallafi ta kasar Sin, ta sanar da shirin ko-ta-kwana a mataki na hudu, da nufin tunkarar tasirin ibtila’in da mahaukaciyar guguwa, da ruwan sama kamar da bakin kwarya suka yi a lardin Guangdong na kudancin kasar, a karo na 12 cikin shekarar nan. Bayan aukuwar mahaukaciyar guguwar da aka yiwa lakabi da Typhoon Noul, yanzu haka an aike da tawagogin jami’ai zuwa yankunan da ibtila’in ya shafa, don nazartar halin da ake ciki, tare da taimakawa mahukuntan wuraren da ayyukan sauyawa jama’a matsugunai, da tabbatar da samar musu abubuwan bukata. Rahotanni sun tabbatar da cewa, a yau Lahadi hukumar tsara ayyukan ci gaba da aiwatar da sauye-sauye ta kasar Sin, ta bukaci a samar da kudi har yuan miliyan 100 daga kasafin kudin kasa don tallafawa lardin na Guangdong, ta yadda za a iya gudanar da ayyukan farfado da kayan more rayuwa bayan ibtila’in. Ana kuma sa ran amfani da kudaden wajen gyara hanyoyin mota, da wuraren adana ruwa, da kayayyakin hidimtawa jama’a irinsu makarantu da asibitoci. Ta hanyar aiwatar da wadannan matakai, ana fatan gaggauta sake farfado da harkokin masana’antu, da zamantakewar al’umma kamar yadda aka saba. Mahaukaciyar guguwar mai lakabin Typhoon Noul, ta aukawa lardin Guangdong da safiyar Lahadin nan, inda karfin iskar a kusa da tsakiya ya kai maki 14. Sai dai rahotanni na cewa yanzu haka karfinta ya ragu daga matakin koli. (Saminu Alhassan)
Ya zuwa jiya Asabar 25 ga watan nan na Yuli, kudaden shigar gidajen sinima na kasar Sin a zangon lokacin...
Yanzu haka saura kusan kwanaki 100 a bude gasar wasannin Olympics ta matasa ta birnin Dakar ta shekarar 2026, kuma...
Gwamnatin Jihar Bauchi ta bayyana wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, wanda ke iƙirarin cewa Gwamna Bala...
Dattawan Arewa sun bayyana cewa yankin ya rasa alkiblarsa sakamakon gazawar shugabanci da watsi da kyawawan ɗabi'u da suka gina...
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana aniyarsa ta dawo da masana'antar yadi da kuma bunƙasa noman auduga a jihar,...
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.