Sojoji Sun Daƙile Yunƙurin Garkuwa da Mutane, Sun Ceto Shugaban Kwalejin Tarayya A Zamfara
Dakarun Sojin Shiyya 2 na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Operation FANSAN YAMMA sun daƙile wasu yunƙurin garkuwa da mutane tare...
Dakarun Sojin Shiyya 2 na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Operation FANSAN YAMMA sun daƙile wasu yunƙurin garkuwa da mutane tare...
Ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi, ya halarci wani taro na manyan jami’ai da aka shirya bisa cika shekaru...
A yau Talata ne kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya bayyana cewa bai kamata manufar alakar kasa da kasa, da hadin gwiwar sassa daban daban ta zama kaiwa wani bangare na daban hari ba. Lin, ya bayyana hakan ne yayin taron manema labarai na yau da kullum da aka saba gudanarwa, lokacin da aka bukaci ya yi tsokaci game da wasu rahotanni, masu cewa Amurka na shirin kara daruruwan miliyoyin dala da take kashewa, da nufin dakile karuwar tasirin da Sin ke samu a sassan nahiyar Amurka, da Afirka da Asiya. Jami’in, ya ce kasar Sin na adawa da kafa duk wani rukuni na mayar da wasu sassa saniyar-ware, kuma duk wani hadin gwiwa da Sin ke yi da wasu sassan kasashe da yankuna, musamman ma da kasashe masu tasowa, ba tana yinsa ba ne da nufin kafa rukuni, ko yin adawa da wani bangare, maimakon haka tana hada karfi da karfe ne da sauran sassan duniya da nufin kare zaman lafiyar duniya, da ingiza ci gaban duniya, da daga matsayin odar kasa da kasa, da gina al’ummar duniya mai makomar bai daya. Lin Jian, ya kuma yi tir da siyasantar da batun shimfida wayoyin sadarwa na karkashin teku, yana mai cewa yin hakan zai gurgunta tsarin gudanar da kasuwanni na kasa da kasa. Kalaman nasa sun biyo bayan wasu rahotanni dake cewa Amurka, ta bayyana damuwa game da shigar kasar Sin cikin aikin shimfida wayoyin sadarwa a sassan tekun Fasifik. (Saminu Alhassan)
Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya halarci bikin ƙaddamar da Kamfanin Jinlide•Qiangyu New Energy a birnin Nanchang na lardin...
Ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta fitar da takarda mai taken “Matsayin Sin kan abin da ake kira da ‘samar...
Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta ce gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu za ta ci gaba da ƙara ƙaimi...
Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta soke hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ya umarci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta...
Mataimakin shugaban sashen cinikin waje na ma’aikatar harkokin cinikayya ta kasar Sin He Shaojun, ya bayyana a gun taron manema...
Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayyana Shugaban Hukumar Tara Harajin Cikin Gida ta Jihar Kaduna, Jerry Adams, a...
Kwanan baya, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya fidda muhimmin bayani kan ayyuka masu nasaba da Sinawan dake kasashen ketare....
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.