Wani sabon bincike ya gano cewa cin hanci da rashawa da rashin da’a tsakanin jami’an ’yansanda na rage amincewar jama’a ga Rundunar ’Yansandan Nijeriya (NPF) sosai, tare da yin tasiri kan yadda ’yan kasa ke son raba bayanan sirri da rundunar wajen yaki da rashin tsaro.
James Ojo Adakole ne ya gudanar da binciken, wanda aka wallafa a mujallar IRE Journals, inda aka gudanar da bincike kan ’yan Nijeriya 256 domin tantance yadda jama’a ke kallon ’yansanda da kuma irin amincewar da suke da su, da yadda wadannan halaye ke tasiri kan bayar da bayanan sirri wajen yaki da rashin tsaro a kasar.
Sakamakon binciken ya nuna cewa cin hanci da rashawa da rashin da’a na daga cikin abubuwan da ke raunana amincewar jama’a ga ’yansanda.
A cewar binciken, kashi 84.8 cikin 100 na wadanda aka yi wa tambayoyin sun ce cin hanci da rashawa da rashin da’a na rage amincewarsu ga Rundunar ’Yansandan Nijeriya, yayin da kashi 85.2 cikin 100 suka ce ba su yarda cewa rundunar tana yi wa ’yan kasa adalci ba tare da nuna son kai ba.
Haka kuma, kashi 67.6 cikin 100 sun ce jami’an ’yansanda a yankunansu ba sa nuna kwarewa da dabi’a mai kyau yayin hulda da jama’a.
Baya ga batutuwan cin hanci da rashawa, binciken ya gano cewa yawancin ’yan Nijeriya da aka bincika ba su da cikakkiyar amincewa da ’yansanda.
Yayin da kashi 62.9 cikin 100 suka ce ba su amince da Rundunar ’Yansandan Nijeriya wajen kare rayuka da dukiyoyi a al’ummominsu ba, kashi 72.7 cikin 100 sun ce ba su da kwarin gwiwar cewa rundunar za ta iya mayar da martani yadda ya kamata ga barazanar tsaro.
Binciken ya gano cewa wannan rashin amincewa ya samo asali ne musamman daga abubuwan da mutane suka fuskanta da kansu, ba wai kawai daga labaran da suka ji daga wasu ba.
Mai binciken ya kuma gano cewa wannan gibin amincewa yana da tasiri kai tsaye kan yadda jama’a ke bayar da bayanan sirri ga hukumomin tsaro.
Ko da yake adadi mai yawa daga cikin ’yan Nijeriya da aka bincika sun nuna shirye-shiryen hada kai da ’yansanda inda kashi 74.6 cikin 100 suka ce za su kai rahoton abubuwan da suke zargi, yayin da kashi 84.4 cikin 100 suka ce za su raba muhimman bayanan tsaro domin taimakawa wajen hana aikata laifuka, binciken ya tabbatar da cewa irin wannan hadin kai yana da alaka sosai da yadda jama’a suka amince da rundunar.
Misali, kashi 52 cikin 100 na wadanda aka yi wa binciken sun ce shirye-shiryensu na bayar da bayanan sirri ya dogara ne da irin amincewar da suke da ita ga ’yansanda, yayin da kashi 88.7 cikin 100 suka ce za su fi kasancewa a shirye su hada kai da ’yansanda idan amincewarsu ga rundunar ta inganta.
Mai binciken ya bayyana cewa wannan sakamakon ya yi daidai da Ka’idar Amincewa da Hukumomi (Institutional Trust Theory) da aka gina binciken a kai, wadda ke cewa hadin kan ’yan kasa da goyon bayansu ga wata hukuma ya danganta matuka da irin amincewar da suke da ita ga wannan hukuma.
Binciken ya kuma nuna cewa tsoro na hana wasu daga cikin ’yan kasar da ke son bayar da bayanan sirri ga ’yansanda yin hakan. Kashi 68.4 cikin 100 na wadanda aka yi wa binciken sun ce ba sa jin cewa suna cikin aminci idan suka bai wa ’yansanda bayanan sirri, saboda fargabar tsoratarwa ko cin zarafi, yayin da kashi 35.2 cikin 100 kacal suka amince cewa ’yansanda za su iya adana bayanan ’yan kasa cikin sirri.
Domin magance wadannan kalubale, mai binciken ya ba da shawarar cewa Rundunar ’Yansandan Nijeriya ta kara kokarin kawar da jami’an da suka aikata laifi ko suka saba ka’ida, ta samar da horo na yau da kullum kan yadda jami’ai za su rika hulda da jama’a, tare da shirya tarurrukan tattaunawa da al’umma domin magance korafe-korafen da ke maimaituwa.
Binciken ya kuma yi kira da a samar da matakai na zahiri na kare masu bayar da bayanai, ciki har da tsare sirrin bayanansu, domin tabbatar wa ’yan kasa da aminci da kuma karfafa su wajen yin hadin kai a fili da ’yansanda a yakin da ake yi da rashin tsaro a kasar.
A cewar mai binciken, gudanar da binciken ya zama wajibi ne saboda muhimmancin bayanan sirrin da ’yan kasa ke bayarwa wajen magance matsalar rashin tsaro da ke karuwa a Nijeriya.
Ya ce, “A wannan muhimmin lokaci a tarihin kasar, ’yan Nijeriya na bukatar ’yansanda su tarwatsa kungiyoyin masu aikata laifuka da ke karuwa, wadanda suka sa da dama daga cikin jama’a ke jin ba su da cikakken tsaro a kan hanya da kuma a gidajensu.
“Amma idan babu goyon bayan jama’a, samun wannan nasarar zai kasance babban kalubale ga Rundunar ’Yansandan Nijeriya.
“Saboda haka, ya zama wajibi ’yansanda su kara kokari da albarkatun da suke amfani da su wajen gina amincewa da jama’a da kuma magance munanan ra’ayoyin da ake da su game da rundunar, ta hanyar kwarewa da inganta yadda suke gudanar da ayyukan da kundin tsarin mulki ya dora musu,” in ji karshen binciken.














