ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dangote Ya Garzaya EFCC Da Ƙarar Tsohon Shugaban NMDPRA Bayan Janye Ta Daga ICPC

by Abubakar Sulaiman
8 months ago
Dangote

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ta hannun lauyoyinsa, ya shigar da wata sabuwar ƙara a gaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Ƙasa (EFCC) kan tsohon Babban Daraktan Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur (NMDPRA), Farouk Ahmed.

Wannan ci gaban ya tabbata ne cikin wata sanarwa da sashin yaɗa labaran Kamfanin Dangote ya fitar a ranar Juma’a. A baya, Dangote ya kai ƙara ga Hukumar ICPC inda ya zargi Farouk Ahmed da kashe kimanin dala miliyan 5 wajen karatun ’ya’yansa a makarantar sakandare a ƙasar Switzerland. Duk da cewa Dangote ya janye ƙarar kwanaki kaɗan da suka wuce, ICPC ta bayyana cewa za ta ci gaba da bincike kan lamarin.

  • Har Yanzu Ana Yi Wa Matatar Man Mu Bita Da Ƙulli – Dangote
  • Ƙungiyar Kwankwaso National Network Ta Gudanar Da Taron Kudu Maso Yamma A Ibadan

Sanarwar ta ce yanke shawarar kai ƙarar zuwa EFCC ya biyo bayan “janye ƙarar daga ICPC a matsayin dabara domin hanzarta tsarin gurfanarwa da shari’a.” A cikin ƙarar da aka miƙa wa EFCC, Dangote ya nemi a binciki zargin cin zarafin ofis da kuma tara dukiya ta haramtacciyar hanya da ake yi wa Farouk Ahmed.

ADVERTISEMENT

Ƙarar, wadda babban lauyan Dangote, Dokta O.J. Onoja ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa Dangote a shirye yake ya gabatar da hujjoji masu ƙarfi domin tabbatar da zargin almundahana da rashin barnar kuɗi da ake yi wa tsohon shugaban NMDPRA. Har ila yau, an jaddada cewa EFCC na da cikakken ikon bincike da gurfanar da masu laifin cin hanci da rashawa.

Lauyan ya kuma yi kira ga EFCC ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Mista Olanipekun Olukoyede, da ta gudanar da cikakken bincike kan zargin, tare da tabbatar da gurfanar da Ahmed gaban shari’a idan aka same shi da laifi, domin nuna cewa babu wanda ya fi ƙarfi a gaban doka.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Dangote
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Iyalin El-Rufai Sun Bai Ministan Tsaro Wa’adin Kwana 7 Kan Zargin Rikicin Kudancin Kaduna
  • Abubakar Sulaiman
    Atiku Ya Zargi Gwamnatin Tarayya Da Cin Bashi Kamar Mashayin Da Kuɗi Ya Ƙarewa
  • Abubakar Sulaiman
    Boko Haram Ta Kai Hari Adamawa, Ana Fargabar Mutuwar Mutane 11
  • Abubakar Sulaiman
    Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Sokoto, Sun Kashe Mutane 7, Sun Yi Garkuwa Da 12

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
Next Post
Yerima Shettima Ya Gudanar Da Aikin Duba Lafiya Kyauta Ga Mutane 500 A Kaduna

Yerima Shettima Ya Gudanar Da Aikin Duba Lafiya Kyauta Ga Mutane 500 A Kaduna

LABARAI MASU NASABA

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.