ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Darussa Daga Ramadan Na 8: Haƙuri Da Sadaukarwa Domin Rabauta Ta Har Abada

by Nuhu Ubale Ibrahim
6 months ago
Ramadan

A cikin watan Ramalana muna koyon haƙuri wajen cimma kyawawan burace-buracenmu. Ramalana makaranta ce ta juriya da sadaukarwa. Yana koya mana cewa babu damuwa, babu aibi, babu hasara idan mutum ya bar wasu abubuwan more rayuwa na ɗan lokaci domin neman jin daɗi na har abada.

Azumi ba abu ne sauƙi ba, yana buƙatar ka bar abin da kake so kuma kake iya samu, domin samun wani matsayi a wurin Allah. Mumini yana barin abinci, da ruwa da sauran abubuwan jin daɗi ne saboda Allah. Wannan barin da ya yi, ba rashi ba ne, face jarabawa ce da za ta haifar da riba mai girma a duniya da lahira. Manzon Allah (S.A.W ) ya bayyana girman ladan azumi da cewa mutum na iya samun gafarar Allah ta dalilinsa, idan ya yi shi da imani da neman lada. Azumi yana kankare zunubai, yana ɗaukaka darajoji, yana tsarkake zuciya.

  • Darussa Daga Ramadan Na 6: Girmama Ni’ima Da Gujewa Almubazzaranci A Ramalana
  • Darussa Daga Ramadan Na 5: Tsare Gaɓɓai Daga Saɓo

Ka lura da girman ladan azumin rana guda kacal. Ya zo a cikin Sunan na an-Nasa’i cewa Manzon Allah (S.A.W) ya ce:” Duk wanda ya yi azumin rana ɗaya domin Allah,to, Allah zai nisanta fuskarsa daga wuta tsawon tafiyar shekara saba’in”
Wannan hadisi Muhammad Nasiruddin al-Albani ya inganta shi.

ADVERTISEMENT

Ka yi tunani: rana ɗaya kacal! Amma ladanta kariya ce daga wuta tsawon tafiya mai nisa ƙwarai. Wannan yana nuna cewa abin da muke gani ƙarami a duniya, a wurin Allah yana da girma matuƙa idan ya kasance da ikhlasi.

Ramalana yana koya mana darasin jinkirta jin daɗi. Watau ka bar jin daɗin yanzu domin ka samu mafi girma a gaba. Wannan hikima ce da ta shafi duniya ma; duk wanda ya iya haƙuri, ya jure wahala kaɗan domin manufa mai girma, shi ne yake kaiwa ga nasara. Mumini yana barin jin daɗi na wucin gadi domin tsira da rabauta a ranar Lahira. Yana jure yunwa domin cikewar rahama. Yana jure ƙishirwa domin shan ruwan Aljanna. Yana jure gajiya domin dawwamammen hutu.

LABARAI MASU NASABA

An Tantance Masu Neman Aikin Koyarwa 500 A Jigawa

JAMB Ta Ƙara Wa’adin Amincewar Guraben Karatu Zuwa 30 Satumba

Haƙuri a Ramalana ba kawai haƙurin yunwa ba ne, har ma haƙuri ne a kan ibada, da haƙuri a kan nisantar saɓo, da haƙuri a kan kyautatawa mutane, da haƙuri a kan gyaran hali.

Idan muka fita daga Ramalana da wannan darasi, to za mu zama masu iya jure wahalhalun rayuwa domin manyan manufofi. Za mu iya barin haram domin halal, za mu iya barin ƙarya domin gaskiya, za mu iya barin son zuciya domin yardar Allah.

Allah Ya ba mu haƙuri na gaskiya, Ya karɓi azuminmu, Ya nisanta mu daga wuta, Ya kuma sa mu cikin masu rabauta a ranar Lahira. Amin.

Abu Razina Nuhu Ubale Ibrahim Paki

Ramadan
Nuhu Ubale Ibrahim
+ postsBio
  • Nuhu Ubale Ibrahim
    https://hausa.leadership.ng/author/nuhu-ubale-ibrahim/
    Layya Babbar Ibada A Musulunci Na 1
  • Nuhu Ubale Ibrahim
    https://hausa.leadership.ng/author/nuhu-ubale-ibrahim/
    Karamar Sallah: Sallar Idi A Wajen Musulmi…
  • Nuhu Ubale Ibrahim
    https://hausa.leadership.ng/author/nuhu-ubale-ibrahim/
    SAHUR [Falalarsa Da Fa’idojinsa] Na 23
  • Nuhu Ubale Ibrahim
    https://hausa.leadership.ng/author/nuhu-ubale-ibrahim/
    SAHUR [Falalarsa Da Fa’idojinsa] Na 22

MASU ALAKA

Ramadan
Ilimi

An Tantance Masu Neman Aikin Koyarwa 500 A Jigawa

August 31, 2026
Ramadan
Ilimi

JAMB Ta Ƙara Wa’adin Amincewar Guraben Karatu Zuwa 30 Satumba

August 29, 2026
Kosan Waka Ya Rasu, Gwamnan Kano Ya Jajanta Wa Iyalansa
Ta’aziyya

Kosan Waka Ya Rasu, Gwamnan Kano Ya Jajanta Wa Iyalansa

August 2, 2026
Next Post
Sin Na Bibiyar Halin Da Ake Ciki Yayin Da Zaman Tankiya Ke Karuwa Tsakanin Amurka Da Iran

Sin Na Bibiyar Halin Da Ake Ciki Yayin Da Zaman Tankiya Ke Karuwa Tsakanin Amurka Da Iran

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.