ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dimbin Boyayyun Nasarorin Da Dantsoho Ya Sanar A NPA

by Bello Hamza
5 months ago

A shekarar 2024 ce, Shugaban hukumar kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta kasa, Dakta Abubakar Dantsoho, ya shiga ofis, a matsayin shugaban NPA.

Sai dai, tun daga lokacin da ya kama aikin, akwai wasu, manyan boyayyun ayyukan ci gaba da ya samar, musamman wadanda suka kara taimaka wa, wajen kara ciyar da NPA, gaba.

Karin wani abin mahimmanci da nadinsa, a mukamin shi ne, Kasancewar sa ba dan siyasa ba, amma wanda ya jima yana bayar da gudunmawar sa, NPA tun lokacin da ya yi aikin yiwa kasa hidima a NPA a 1994, ya kuma kai matakin rike mukamai da dama, bayan an dauke shi aiki a NPA, hakan ya sanya ya kara samun damar, samar da ci gaba a hukumar.

ADVERTISEMENT

Kafin a dada shi a mukamin, shugabancin NPA, Dantsoho, ya gaji ayyuka da dama a NPA, da suka hada da, manyan Tashoshin Jiragen Ruwan kasar wato na Apapa da kuma ta Tin Can Island, wadanda suka kasance, an kafa su shekaru da dama, da suka gabata.

Kazalika, sun kasance ba su da wani cikakken damar iya bayar da damar zirga-zirga ga manyan Jiragen Ruwa, musamman, da suka taso, daga wasu kasashe kasa da kasa da rashin samar masu da kayan aiki na zamani.

LABARAI MASU NASABA

Yadda Taron Bikin Maulidi Ya Gudana A Unguwar Mile 12 A Legas

NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba

A saboda haka ne, Dantsoho ya yi amfani da zurfin iliminsa da kwarewar da ya samu a NPA a mukaman da ya rike a baya da kuma dubi da nazarin da ya yi na yawan alummar kasar nan, da yawansu, ya zarce milyan 230 tare irin karfin tattalin arzikin da ta ke da shi, a fadin nahiyar Afirka ya ga cewar, ta dace a zamanantar da Tashoshin Jiragen Ruwanta, zuwa daidai da matakan sauran na duniya.

Domin ya cimma wannan burin, Dantsoho ya kirkiri cikakkiyar manhajar zamantar da Tashoshin, tare da kuma samar da wasu kananan Tashoshin Jiragen Ruwan kamar dai ta Lekki da ke a jihar Legas tare da wadata su, da na’urorin zamani domin gudanar da ayyukan su.

Misali, Tashar ta Lekki ta samar da karuwar da ta kai ta kaso 20, a 2026, idan aka kwatanta da wanda aka samu, shekarar da ta wuce wanda hakan ya sanya har ta kai matakin iya samar da zirga-zirgar Jiragen Ruwa da suka kai jimlar kaso 40.

Hakazalika, ya farfado da Tashoshin Jiragen Ruwa na  Warri, Koko, Sapele da Burutu da aka yi watsi da su shekaru da dama.

Dantsoho an zabe shi a matsayin mataimakin shugaban kungiyar kasa da kasa ta Afirka wato AIAPH, a watan Agustan   2025. inda kuma a watanni baya, aka zabe shi a matsayin shugaba na farko, dan Nijeriya na kunzamani kula Tashoshin Jiragen Ruwa na Afirka ta Yamma wato, PMAWCA inda hakan, ya kara daga darajar sa, a yankin..

Duba da yadda ya himmatu wajen ci gaba da bunkasa fannin, ya samu sahalewar dala biliyan 1.1 daga gun gwamnatin tarayya, musamman domin samar da kayan aiki na zamani a a sabbin Tashoshin Jiragen Ruwa na  Badagry, Akwa Ibom,  da kuma ta Kalaba.

Bello Hamza
+ postsBio
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Jihar Kano Za Ta Amfana Matuka Da Gidauniyar Aliko Dangote – Masu Ruwa Da Tsaki
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    An Nuna Damuwa Kan Sake Kamun Da DSS Ta Yi Wa Boɗejo Bayan Samun Belin EFCC
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Dole Al’ummar Arewa Su Rungumi Hanyoyin Kasuwanci Na Zamani —Alfa Musa
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Ba Mu Taba Biyan Kudin Fansa Ba Kuma Ba Za Mu Biya Ba – Kwamishinan Katsina

MASU ALAKA

Yadda Taron Bikin Maulidi Ya Gudana A Unguwar Mile 12 A Legas
Tattalin Arziki

Yadda Taron Bikin Maulidi Ya Gudana A Unguwar Mile 12 A Legas

September 4, 2026
NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba
Tattalin Arziki

NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba

September 4, 2026
NPA Ta Tabbatar Da Maido Da Manyan Kayan Aikin Hukumar Wuta Ta Neja Delta —Babbar Manaja
Tattalin Arziki

NPA Ta Tabbatar Da Maido Da Manyan Kayan Aikin Hukumar Wuta Ta Neja Delta —Babbar Manaja

August 28, 2026
Next Post
Kungiyar Malaman Jami’ar AFUSTA Za Ta Tsunduma Yajin Aiki

Kungiyar Malaman Jami'ar AFUSTA Za Ta Tsunduma Yajin Aiki

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.