Wani mummunan hatsarin kwale-kwale da ya faru a garin Gorau da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Goronyo a Jihar Sokoto ya yi sanadin salwantar rayukan mutane sama da 40. Akasarin waɗanda suka rasa rayukan nasu mata ne da kuma ƙananan yara masu kimanin shekaru 10 zuwa 15, waɗanda suke kan hanyarsu ta zuwa gonakin shinkafa domin gudanar da ayyukan noma.
Duk da cewa Hukumar Kula da Hanyoyin Ruwa ta Kasa (NIWA) ta tabbatar da mutuwar mutane 41 a hukumance, Rundunar ‘Yansandan Jihar Sokoto ta bayyana cewa tuni an ciro gawarwaki 46. Sai dai kuma, majiyoyi daga yankin da abin ya faru sun tabbatar da cewa adadin waɗanda suka mutu ya kai 53, duba da cewa kwale-kwalen yana ɗauke da fasinjoji sama da 70 a lokacin da ya kife.
Rahotanni sun nuna cewa an samu nasarar ceto wasu mutane fiye da goma a raye, ciki har da dagacin garin na Gorau. Manajan hukumar NIWA a Sokoto, Mista Abdulkadir Yusuf, ya danganta aukuwar wannan mummunan hatsari da sakaci, da ɗaukar lodi fiye da kima, gami da rashin kiyaye ƙa’idojin tsaro a kan hanyoyin ruwa.
A halin yanzu dai, jami’an Hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA) tare da haɗin gwiwar kwararrun masunta na yankin suna ci gaba da aikin bincike da ceto a cikin kogin.
Wannan al’amari ya sake fito da ƙalubalen yawan asarar rayuka a haɗurran kwale-kwale a Nijeriya, wanda yakan ta’azzara a lokutan damina inda al’umma ke yin amfani da hanyoyin ruwa saboda taɓarɓarewar tituna da kuma matsalar tsaro a yankunansu.














